BABI NA UKU

2.3K 143 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)
               
                    {~2-10~}

      Washe gari da sassafe Sultana ta tashi Umar suka fara shirin zuwa aiki,
    Bayan sun gama shiri ta yima Hafsa da Haydar wanka sannan ta shirya Hafsa cikin Uniform d'in School d'insu,
     Sauran pepper soup d'in jiya tayi warming nashi sannan ta soya mata Irish da k'wai ta saka a launch box d'inta.

      "Wow! Kinyi kyau baby na, barin snapping naki"
    Hafsa uwar iyayi kuwa aka wani yi style na d'aukar hoto,
    Saida Sultana ta d'auketa hoto kala biyar sannan tace "to ya isa haka, barinyi Feeding haydar shima tunda dai kinga anan zan tafi in barshi",
    "Ok Momy ki d'iba a nawa ki bashi" Hafsa ta fad'a cike da soyayyar k'aninta,
     "Ahh Hafsa ai na d'ibar masa nashi daban, gashi kin gani" Sultana ta fad'a tare da nunawa Hafsa sauran Irish da k'wan data ragewa Haydar.

    Saida suka gama tas Umar ya fito cikin suite d'inshi black and white,
    Yayi matuk'ar yin kyau kamar in saceshi in gudu,
    "Yadai Madam? Hope kun gama saboda inada aiki da yawa a Office yau, kuma kema d'in nasan ba zaki rasa ba".
     "I think bani da aiki nikam, bandai san ko sai naje zan sameshi ba, mun gama dama kai muke jira",
     "Ok muje kawai" ya fad'a bayan ya soka wayarshi cikin aljihu.
   Bai gama sakawa ba yaji k'arar text message ya shigo masa,
    Zarowa yayi ba tare da tunanin komai ba ya fara karantawa,
    _"Nasan zakuyi tunanin kawai inason inyi wasa da hankalinku ne, to sam ba haka bane, kamar yanda na fad'a maku an cuceta kuma bata da halin karb'ar fansa saboda anfita kud'i, mulki da komai ma, na rok'eku dan Allah da soyayyarshi ga mafificin halitta ku taimketa,_
     _Idan har kuna bisa ga ra'ayin taimakonta zaku iya maido min da reply ni kuma sai in baku address nata"_

     "Again?" Umar ya fad'a a bayyane.
     "Menene ya faru honey?" Sultana ta tambayeshi bayan ta gama sakawa Hafsa socks and sandals nata.
      "Karb'a ki gani" ya mik'a mata wayar,
      "Ana so ayi wasa da hankalinmu ne kawai, zanje wurin MTN su duba min wannan layin, inhar na gano kowaye yake mana yawo da hankali wallahi sai ya raina kansa, ni bana son raini ko kad'an".

    Bayan Sultana ta gama karantawa ta mik'a masa wayarsa,
    "Ni ina ganin honey kafin kayi haka ka tura da reply d'in, tunda har yanzu akace za'a turo mana da address kaga kamar akwai alamar gaskiya a ciki".
    "Alamar gaskiya? A cikin wannan maganar? Bana tunani kam, koma waye idan da gaske yake ai sai yazo ya tinkaremu da maganar tunda dai yasan gidanmu yazo ya kawo takarda jiya, dan haka wannan shirmene kawai kuma kibar maganar nan kamar yanda na fad'a miki jiya, kuma yau yau d'in nan insha Allahu zanje MTN Office suyi min bincike akan layin nan" yayi gaba bayan ya miyar da wayarsa a cikin aljihu,
    "Ku fito mu tafi lokaci na tafiya" yayi waje.

     "Safiyya!" Ta k'walawa Nany d'in Haydar kira,
     "Na'am momy" ta fad'a tare da saukowa daga kan bene da sauri.
     "Gani momy" ta fad'a tana kallon Sultana,
     "Ki d'auki Haydar ki goyashi nasan yanzu zayyi bacci tunda na mashi wanka ya karya kuma".

    D'aukarshi tayi kuwa ta goyashi, harda ba-bye yayima Momy'n shi, Hafsa ma ta d'aga mashi hannu sannan suka fita suka samu Umar har ya fitar da mota waje yana jiransu.
    "Afuwan honey, kanata jiranmu",
    "Hmm! Bakya laifi wifey, ku shigo mu tafi".

    Saida suka fara dropping d'in Hafsa sannan suka nufi Federal High Court Katsina,

      Kai tsaye kowa ya nufi Office d'inshi,
    Zaman Sultana keda wuya kuwa sak'o ya shigo mata,
   Exactly irin wanda akama Umar ne,
   Aikuwa bata jira komai ba ta miyar da amsa,
    _"A shirye muke da taimakonta indai har da gaskene wannan sak'onnin da ake turo mana, kullum burinmu shine muga mun taimaki wanda aka zalunta ko kuma wanda ake k'ok'arin zalunta, dan haka ina jiran address d'inta yanzu"._
     Tayi sending tare da ajiye wayar akan desk d'inta.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now