BABI NA SHA TAKWAS

1.3K 102 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~70~}

   

     _Gaisuwa ga masoyiya ko ince abar k'aunata *Aunty sis💞* muna jin dad'in yanda kike kula damu a koda yaushe, bamu san ta wace hanya zamubi don ganin mun gode miki ba, saidai muyi fatan Allah yabar mana ke yaja da rai, Allah kuma ya raya zuri'ah bisa tafarkin manzon Allah (SAW), wannan shafin sadaukarwa ce gareki, Allah yabar zumumci ameen. #onelove#_

******

      Saida wutar ta gama cinye gidan k'urmus sannan mutane suka fara shiga ciki dukda gumin dake tasowa daga cikinshi,
   Alamar gawama babu a ciki, hakan yasa wasu suka fara tunanin ko wuta ta cinye gawarsune? Cike da tausayi suka ringa fita daga cikin gidan wasu har yanzu basu daina hawayen tausayi ba.

****

    Sultana ce ke jan mota a sukwane sai faman k'ara wuta take,
   Can daga bayan motar na jiyo murya ana fad'in
    "Wallahi bansan garinya na manta kayan sakawar mama ba, kuma abun haushi wai duka nawane kawai na had'a a jikar bakon, babu nata ko d'aya"
    "Ai saisa kikaga ina gudu dan kar dare ya nitsa sosai bamu koma gida ba, amma da yake kayan ne kawai zaki d'auka ai da sauk'i ma"  Sultana ta fad'a bayan ta rage gudu da motar.

   Murza idona nayi dan tabbatar da muryar wadda naji, ko tantama  babu wannan muryar Ummimah ce, to amma garinya hakan ta kasance? Kenan basu cikin gidansu lokacin da wutar ta kama?,
   Ku biyoni yanzu zaku samu amsoshin wannan tambayoyin.

   Lokacin da Sultana ta nufi gidan su Ummimah dan ta tambayeta address d'in Zarah da Rabiatu,
   Ta samesu itada Mama yanzu sun d'an saki ransu akan baya,
   Bayan sun gaisa ne ta fad'a masu abunda ya kawota,
   Ko amsa Ummimah bata kaiga bama Sultana ba taji wayarta ta d'auki ruri alamar k'arar shigiwar text message,
   D'auka tayi ta fara karantowa

    _ina shawartarki daku d'aukesu daga wannan gidan da suke ciki, saboda muguntar waccan nasan komai zata iya aika masu savoda tasan gidansu, amma idan kika d'aukesu daga ciki kinga shikenan hankalinku kwance kuna tare dasu, sannan kuma ku kanku zakufi samun sauk'in yi masu tambayoyi ba sai kun tado mota kunzo har gidansu ba. #shawarace#_

    Cike da mamaki take karanta sak'on,
   Kanta ta jinjina alamar ta gasgata maganar,
    "Ina zuwa mama" ta fad'a bayan ta mik'e tsaye ta nufi waje,
    Umar ta kira ta shaida masa sak'onda aka tura mata,
   Suna cikin wayar shima nashi ya shigo a k'aramar wayarsa,
    "Ki d'aukosu kawai idan zasu yarda" ya fad'a cike da mamakin wanda yake turo masu wannan sak'unan wanda su kansu su Ummimah d'in basu sani ba, nima kuma Amrah ban sani ba kawai dai ina baza idona don ganin ko wanene wannan amma kuma shiru har yanzu.

   Tsinke wayar tayi ta shiga cikin gidan har yanzu bata daina mamaki ba,
   Bayan ta sauna tace
   "Dama wata tambayace ta kawoni inyi miki Ummimah, to amma kuma sai mai gidana ya kirani yace idan babu damuwa ko zaku bini mu koma gidanmi da zama na wani lokaci? Saboda zamanku anan zai iya zama matsala koba yanzu ba".

   Ajiyar zuciya mama ta sauke sannan tace
    "Tabbas maganarki gaskiyace Sultana, ni kaina tunda aka fara maganar kai k'arar nan hankalina ga baki d'aya bai kwanta da zaman gidan nan ba, dan haka mun amince mu tafi d'in babu damuwa mungode sosai Allah yayi maku albarka, Allah kuma ya mana jagora".

    Dad'i sosai Sultana taji da Mama bata musa mata ba,
    "Ameen mama, sai ku had'a kayan da zaku tafi dasu yanzu mu tafi yamma nayi".

   Tashi Ummimah tayi ta nemi 'yar Gana most go ta fara ziba kayanta, saida ta gama kuma kwata kwata ta manta bata had'a na mama ba, sai hijabi d'aya wadda ke rataye a k'ofa ta saka wadda saboda itane tayi tunanin ta saka kayan mama d'in, ga kuma sauri da takeyi kasantuwar Sultana tace suyi sauri tana so ta d'auko Hafsa daga islamiya.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now