BABI NA BIYAR

1.8K 118 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*
               
                   {~21-30~}

   "Hello honey" ta fad'a a hankali,
    "Na'am wifey, kina kusa da Hauwa ne? Ina son inyimata ya mai jiki",
    Shiru Sultana tayi kafin tace "aikuwa na fita yanzu amma zan koma, saidai ko ka kira number'nta ko kuma idan na koma in kiraka sai in bata",
   "To babu damuwa, idan kin koma d'in sai ki kirani, saboda gaskiya babu tabbas d'in zan samu zuwa gobe gidan nata dan akwai hidimar data taso min goben" 
     "Ok honey sai na koma d'in" tayi hanging up na wayar.

    Juyowa tayi ga Ummimah da Mama tace "kuyi hak'uri fa mama, maigidana ne ya kirani",
   "Uhm babu komai Sultana, bari ki fara ji daga bakin Ummimah sannan nima in fad'a miki abunda na sani" mama ta fad'a cike da natsuwa.

    Ga Ummimah ta juya tace "ina saurarenki Ummimah".

    "Asalin sunana Aisha Abubakar ne, amma Mamana da babana suna kirana da Ummimah kasantuwar sunan kakata wadda ta haifi babana aka saka min, nice babba a wurin iyayena sai k'annena guda biyu 'yan biyu ne Afrah da Amrah, shekara biyu ke tsakanina dasu tun daga nan kuma haihuwa ta d'aukewa mamana, dama wurin haihuwarsu Amrah tasha wahala sosai.

    Mahaifina nada rufin asirinshi daidai gwargwado, muna zaune a gidan haya a cikin unguwar Saulawa dake nan cikin garin Katsina, babana yana aiki a wata k'aramar ma'aikata a k'ark'ashin wani mutumi inda ya zama masinjanshi.

       Akwai shak'uwa sosai tsakaninmu, mukan zauna a koda yaushe muyi raha tare da iyayenmu,
      Babana ya sakani a makarantar gwamnati saboda bashi da halin da zai kaimu makarantar kud'i duk da yanada burin hakan,
    Na taso da bala'in son inyi zurfi a karatun boko ina son in karanci fannin education kodan in gyara rayuwar bokon zamani, hakan yasa nake miyar da hankalina a kowane term, tun yarintata ni nake d'aukar first position har na shiga secondary School,
   Bani da k'awa ko d'aya ni kad'ai nake rayuwata daga ni sai k'annena biyu wanda bana b'oye masu damuwata suma kuma basu b'oye min tasu damuwar, a raina har nakan tambayi kaina akan wa nafi so a cikinsu, *Afrah ko Amrah* (namesy Futha) saidai kuma amsar d'ayace, duk d'aya suke a wurina.

    Bayan mun rubuta jarabawar JSS ne Allah ya bani sa'a kuwa na samu sakamako mai kyau, ina d'aya daga cikin wanda suka zamo na d'aya a cikin kaf class mates d'inmu,
   Hakan yasa gwamnati ta d'auki nauyin miyar damu Private School mu uku daga cikin d'aliban makarantar.

    Babana yaji dad'i sosai saboda ya dad'e yana mafarkin ganin ya kaini private school nida Afrah da Amrah,
   Nima naji sosai hakan yasa na sake d'aure d'amarar yin karatu sosai har sai inda k'arfina ya k'are.

     Shigata makarantar na had'u da yara kala kala, wasu 'yan rainin wayone wasu kuma mutanen kirki ne, amma kuma 'yan rainin wayonsu sunfi yawa.

   Ina zaune ni kad'ai kamar ko yaushe na fiddo chemistry note book d'ina ina k'ara  duba wasu equations da akayi d'azu.

    Wata yarinya ce tayi min sallamah tare da mik'o min hannu don mu gaisa,
   Cikin mamaki na amsa sallamar nima na mik'a mata nawa hannun muka gaisa,
   Abunda yasa ni mamaki kuwa dan ban tab'a tunanin akwai irinsu a wannan makarantar ba, tunda naje babu wadda tayi k'ok'arin yimin magana saidai masu bina da kallon banza musamman ma yanda sukaga ina participating a cikin class.

   Bayan na gyara mata wuri ta zauna ne tace min "sannu",
   Nima sannun na miyar mata dashi.

   Murmushi ta sakar min ta sake fad'in "naga kaman You're busy ko? Gashi kuma magana nazo muyi dake".
    Ajiye littafin nayi nima na miyar mata murmushin nace "babu komai ai, ina maimaita karatun d'azu ne kuma ma na gama, ina saurarenki, Allah dai yasa lafiya".
    "Ahh lafiya lau karki damu, na kula dake tun shigowarki makarantar nan kinfi son rayuwarki ke kad'ai, baki damu da rayuwar kowa ba, baki da k'awa ko d'aya ko magana bata dameki ba, iyakacinki kawai ki bada amsa idan wani teacher yayi tambaya, kina da k'ok'ari sosai kuma kowane teacher yana alfahari dake, baki dad'e da shigowa makarantar nan ba amma har an fita outing dake kusan sau biyar ko sau shida, kuma duk wata queeze ko debate d'inda zakuje zakiyi winning, shine nake son idan babu damuwa me zai hana mu zama friends? Ba dan komai ba sai dan ki ringa koya min karatu, saboda nidai bana ganewa idan akayi karatu, amma kinga idan ke kika natsu kika koya min zan gane sosai, amma fa idan babu takura".

    Murmushi kawai na miyar mata dashi,
   "Babu takura ko d'aya, sai dai matsala d'aya kawai",
   Kallona tayi tace "matsala? Wace irin matsala?",
    "Nidai kinga ba d'iyar kowa bace ba face *'yar talakawa* (Afrah), bamu da komai sai rufin asiri, yanzu haka school d'in nan da nake gwamnatice ta d'auki nauyina, iyayena sun min nasiha sosai akan na guji yaran masu kud'i saboda natsalace dasu, suna da wulak'anta talaka sosai,
    Saisa kullum nake ni kad'ai sabda gudun wulak'anci, gaskiya kiyi hak'uri kinfi k'arfina".

    Kallona tayi sosai hawaye ya fara kwaranya daga idonta,
   "Mesa zakice nafi k'arfinki? Kin manta cewa da talaka da mai kud'i duk d'ayane a wurin Allah? Wanda yafi wani shine wanda yafi wani tsoron Allah, dan Allah ki daina wannan maganar, nidai bani da matsala ko d'aya kuma ki tambaya kiji,  indai har kinji na kwanta miki a rai to kiyi k'awance dani kar kiji komai" tana gama fad'in haka ta goge hawaye.

     Shiru nayi mun jima babu wanda ya kuma fad'in komai,
   Saida na nisa sannan nace "to ki bari zanyi shawara da mamana, duk abunda ta yanke zan sanar dake insha Allahu",
    "To babu komai, ina fatan zata amince saboda nikam kin kwanta min a rai, ina son mutum mai irin halinki, gaki da kamun kai sosai duk mazan class d'in nan babu ruwanki dasu kin huta",
    "Nagode sosai sai kin jini" na fad'a bayan na sake bud'e littafina,
    "Au! Shine ba zaki tambayeni sunana ba ko? To tunda baki damu da ji ba ni ki fad'a min naki sunan",
   Kunya naji sosai nayi mata murmushi,
    "Sunana Aisha Abubakar amma anfi kirana da Ummimah, kefa?",
     "Sunana Salmah Abubakar, amma Gentle ake kirana dashi",
    "Nice name, surname d'inmu d'aya dake kenan?" Na tambayeta,
    "Ehh kam hakane".

   Da haka har lokacin dawowa break fast yayi, malami ya shigo akaci gaba da karatu daga inda aka tsaya.

       K'arfe uku daidai aka tashi kamar yanda aka saba,
    'Yar jakata na rataya a kafad'a, na nufi hanyar titi don in samu keke napep in hau.

       Gentle ce da sauri ta ringa k'wala min kira, daga farko ban jita ba sai daga baya, hakan yasa na dakata na jirata har ta iso inda nake,
    "Tunda aka tashi nake rarraba idona ta inda zan hangoki, sai daga baya baseerar in biyoki tanan hanyar ta fad'o min,
    Ina zakije ko tanan ake zuwa d'aukarki?"

     Bayan nayi mata d'an murmushi nace "keke napep zan tara in tafi".

   Da sauri tace min "a'a dan Allah karki tari napep d'in nan, kizo gaya can anzo d'aukata, dama neman da nake miki kenan inji idan ba d'aukarki za'a zo ba sai mu tafi dake a ajeki a gidanku".

      "A'a nidai ki barshi wallahi nagode",
     "Raina baiji dad'i ba idan baki zo mun tafi dake ba, dan Allah kiyi hak'uri mu tafi".

    Dafa kafad'arta nayi nace "Salmah kenan, iyayena zasu min fad'a idan sukaga kun bani lift, kiyi hak'uri babu komai wallahi zan hau keke napep d'in dama kullum ita nake hawa".

    Badan taso ba tace "to shikenan sai anjima, ki gaishe dasu mama" ta tafi,
    Kallo d'aya za'a mata asan bataji dad'in rashin bintan ba, nima kuma kaina banji dad'i ba, saidai kuma dole babu yanda zanyi sai dai hakan, babana zai iya yimin fad'a sosai kuma yace na fara bin yaran masu kud'i ina son in canza hali irin b'ara rayuwata, wanda kuma sam ba haka bane, kuma na kula da Salmah ko a cikin yaran masu kud'in ma ita batada mugun hali, tanada halin kirki kuma tanada son kyautatawa.

    Da wannan tunanin na isa bakin titi na tsayar da keke napep na hau.

Princess Amrah😘
NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now