BABI NA GOMA

1.5K 117 1
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~62~}

    Farkawa nayi na ganni kwance a bisa gadon asibiti,
   A hankali na fara bud'e idona saidai kuma idon yak'i bud'uwar tsabar kumbura daa yayi,
     Sannu sannu na fara tariyo abunda ya sameni wanda yakr mummunan abu ne,
   Kuka na fasa da k'arfi tare da mimmik'ewa a bisa gado ina fad'in "Baba! Mama!! Shikenan sun rabani da martabata, sun keta min mutuncina wanda ko wace mace take tutiya dashi, wayyo Allah Babana!" Na rintse idona sosai ina k'ara tuno yanda suka ringa yi dani.

    Cike da natsuwa wani likita ya shigo hannunshi rik'e da file,
   Sallamah yayi idona rintse na amsa sallamar,
    "Alhamdulillah anyi ta barka tunda kin tashi, sannu ko?"  Likitan ya fad'a tare da zama bisa kujerar da aka tanadar domin zaman likitoci idan sun ziyarci maras lafiya.

     Jin ya zauna yasa a hankali na fara k'ok'arin bud'e idona,
    Idon ya bud'e saidai ba duka ba, saboda wani irin mugun kumburi ne yayi.

     "Sannu kinji Aisha?" Ya fad'a tare da ajiye file d'in akan cinyarshi.

    Kai kawai na d'aga bayan na gyara kwanciyata, ina mamakin yanda akayi har yasan sunana Aisha.

     "Ya jikin naki?" Ya sake fad'i kyakkyawar fuskarshi d'auke da murmushi,
    "Alhamdulillah" kawai na fad'a a tak'aice,
    "To masha Allah! Ina fatan dai kinsan abunda ya sameki",
     Ban bashi amsa ba sai wani irin kuka dana sake b'arkewa dashi ina k'ara duba kayan dake jikna, saboda harsu ji nayi na tsanesu baki d'aya.

    "Anyway, an kawoki asibitin nan ne kwana biyar da suka wuce, daga School Clinic akayi refer d'inki zuwa wannan asibitin a lokacin tamkar baki da rai, saboda ma an fidda tsammanin zaku rayu,
   Ganin ciwonki kamar yafi k'arfin clinic d'inku saboda manyan likitocin naku duk sun tafi hutu basu dawo ba yasa aka kawoki nan,
    Ina so ki ajiye hankalinki ki saurareni, karki sake yin kukan nan ki danganawa Allah komai, saboda dukkan abunda kikaga ya samu bawa to muk'addari ne daga Allah, babu wani bawa wanda yafi k'arfin k'addara, dan haka ki saurareni da kunnen basira zan miki bayanin komai".

    Kai kawai na d'aga masa, ammafa hawayen dake fita har yanzu na kasa tsaidashi daga sintirin da yake a bisa kumatuna.

     Medical glasses d'inshi ya cire ya sak'alashi a lab court d'in daake jikinshi,
    Ya k'ura idonshi cikin nawa, da sauri kuwa na duk'ar da kaina k'asa, sabida wani irin k'warjini naji yamin,
      "Bayan nurses na makarantarku sun kawoki na karb'eki emergency nida abokina Dr. Khalid muka fara duddubaki,
   Saidai kuma bamuyi tunanin ciwonki ba, kawaidai mun karb'eki ne muka fara yi miki gwaje gwaje inda a take muka gane cutar hawan jini datayi miki sabon kamu dan da alama bata wuce kwana d'aya da kamaki ba,
     Bayan mun gamane kamar ance in kalla kawai naci karo da jini a bisa cinyoyinki, baku d'aya cinyar tayi sharkaf da jini harda gullamarsa.

      Hankalina ya tashi sosai nace da Dr. Khalid "kaga babbar matsalar yarinyar nan",
   Sosai mukaji tausayinki, nan da nan muka fara duddubaki inda mukaci karo da raunuka sosai a k'asanki wanda tunda nake a rayuwata ban tab'a ganin ko mai kama dashi ba,
     Na tabbatarda wannan fyad'e ne akayi miki, kuma ba wai mutum d'aya ko biyu ne sukayi aikin ba, saboda yanayin wurin ya rarake sosai da sosai.

   Bansan lokacinda na fashe da kuka ba saboda kin matuk'ar bani tausayi, sannan kuma gaki yarinya k'arama baki wuce 17 ba amma an lalata miki rayuwa,
     Aune aune mukayi sosai anan muka tabbatarda baki d'auke da kowace irin cuta, kawaidai raunukan ne da kikaji,
    Harga Allah banyi tunanin zakiyi rayuwa ba,
    Ganin yawan jinin da kika zubar yasa nayi miki awon jini nan na tabbatarda bakida jini sosai,
   Dan haka na d'ibi nawa jinin kasantuwar zan iya badashi ga kowa na saka miki,
    A tak'aice dai kwananki biyar a asibitin nan kuma bakya cikin hayyacinki, shine yanzu wata nurse tazo gittawa taji muryarki kina sabbatu ta kirani,
   Naji dad'i sosai da kuka tashi sabida jinki nake tamkar 'yar uwata ta jini, saboda duk abunda zai samu wani ko wata sai mutum yayi tunani idan ga wani nashi abun ya faru ya zayyi? Saisa akeso mutum ya zama mai tausayi da jink'ai ga mutane baki d'aya".

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now