BABI NA TARA

1.4K 105 4
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

_Da gudu na taho har ina cin tuntub'e saboda makarar da nayi wurin mik'a jinjina tare da yabon gwanata kuma namesyna *Futhatul-Khair* akan daddad'an littafinta mai taken *k'awata kishiyata,* da jin sunan ma ba sai an fad'awa mutum kalar ma'anarsa ba, dan haka na tayaki murna, sannan kuma na miki fatan Allah ya k'ara miki baseerah da kaifin ido #onelove#_

               
                   {~61~}

     Fitilar hannuna na ringa haska motocin gaban gate d'in, amma kuma duk wadda na duba babu Gentle a cikinta,
  Dan haka na k'ara matsawa daga gaba ina hahhaskawa still dai babu ita,
   Cike da tashin hankali na kashe fitilar wayar tawa, na latsa kiranta saidai kuma naji ana shaida min da babu kud'i kona flashing a wayar,
   Hankalina ya k'ara tashi, kamar zautacciya na ringa k'wala mata kira amma shiru ne.

    Har kusan Faculty of Humanities naje da yake shine daga gate d'in hostel babu nisa saishi amma babu ita,
   Motoci biyu na hanga daga can nesa aikuwa babu shamakin komai na doshi wurinsu,
    Dalle fitilar nayi ata farkon amma sai samari matasa na gani cike da motar, zasu kai kimanin mutum takwas zuwa goma, harma mamakun yanda motar ta d'aukesu nayi,
   Hak'uri na basu sabida naga kamar basuji dad'in haskewar ba.

   "Ke ubanme yasa kika haskemu da fitila? Ko mu sa'anninki ne?" Wani daga cikinsu ya tambayeni cike da muryar maye, alamar yasha ya bugu sosai.

   "Kuyi hak'uri 'yar uwata na fito nema ne, nayi zaton ko itace anan" na fad'a cike da tsoronsu bayan na doshi inda d'ayar motar take.

    Basu kuma cemin komai ba har na isa wurin d'ayar motar,
    Haske cikinta nayi saidai kuma banyi sa'ar kallo ba,
   Saboda mace da namiji ne a bayan motar sunata aikata alfasha gasu tsirara haihuwar uwarsu,
    "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Kawai na fad'a cike da tashin hankali, saboda sam basa cikin hayyacinsu sun lula can wata duniyar.

    Har nayi shirin juyawa zan tafi naci tuntub'e da takalmi,
   Haskawa nayi saboda harda shirin kadani yayi,
   Cike da mamaki na kalli takalmin na k'ara kallonshi,
   "Wannan ai takalmin Gentle ne" na fad'a a fili bayan na tsuguna k'asa ina k'are mashi kallo,
   Daga cam gefe na hangi gyalenta da d'ankwalinta,
   "Ya Salam" na sake furtawa saboda sam ganin abun nake kamar a mafarki.

    Tamkar bana cikin hayyacina na koma jikin gilashin motar na ringa bubbugashi da k'arfi, saboda ni a tunanina kota k'arfi da yaji ne aka turata cikin motar.

   Duk bubbugawar da nakeyi shirune sabida har yanzu basu dawo hayyacinsu ba,
     K'afar takalmin nata d'aya na fara bubbuga gilashin dashi take kuwa suka zabura su duka biyun a tare,
    Da sauri mazan dake cikin waccan motar sukayi wurina,
   "Waike wace irin sakaryar yarinya ce? Ubanme kike a wurin nan? Ina ruwanki dasu?" Wani daga cikinsu ya fad'a kamar zai fad'o min,
   Saurin matsawa nayi gefe hannuna aka ina tsala ihu ina fad'in "jama'a ku taimaka mana, sun tura 'yar uwata a cikin mota",
     Kasantuwar babu giccin kowa yasa babu wanda yajimu,
   Da hanzari cike da kunya macen ta miyar da kayan jikinta bayan namijin ya sauka daga gareta,
    Fitowa daga motar sukayi su duka biyun suna tambayar abunda ya faru.

   Gaba d'aya wutar kaina ta d'auke lokacin dana d'ora idona akan Gentle sai rarraba ido take tana fad'in "wai miye haka kukeyi Khalifx? Muna tsaka da jin dad'inmu zamu nemi tsayar damu" har a lokacin bata kula dani dake gefe ba ina binta da kallon mamaki.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now