One - Kankana

5.9K 375 36
                                    

Bismillahi rahmanin rahim,

“Mutuwa hutu ce a gareni," ta ayyana a ranta yayin da zufa ya karyo mata a wuya, bayan ta da sauran ilahirin jikinta.

A farad daya labarinka zai juya, daga fari zuwa baƙi. Tabbas ta saba jin yadda rayuwar mutane ke canza wa amma bata taɓa cin karo dashi ba sai yau.

"Daga ina zan ɗaura?” ta sake ayyanawa, sai dai kuma babu wanda zai bata amsar tambayar ta.

So da dama zaka kwanta cikin walwala amma ka tashi komai ya tarwatse maka. Duka abinda kake tunanin shine gaskiya sai kaga akasin haka. Wanda ka yarda dasu sai su kasance sune masu cutar dakai. Rayuwar da kake zama da makashin ka amma ta sigar mutunci. Tabbas a yanzu ta yarda da maganar da bahaushe yace, "mugu bai da kama."

Ance rashin sani yafi dare duhu, amma da wani sanin gwara zama cikin tandun kwalli. Saboda yanzu rayuwarta ya canza fasali.

Haɗiye miyau tayi mai mugun zafi, idan kana kusa da ita zaka iya jin ƙarar sa. Sannan ga wani matsanancin ciwon kai da ke addabar ta, tashin hankali tareda rudani data shiga kwanakin nan shine sila.

Fuskan ta a tamke yake babu annuri ko kaɗan, girar sama da ƙasa a harɗe. Goshin ta kuma yayi layi layi. Idanta kuma ba kalar daka saba gani bane, ruwan toka ne ƙwayar sannan kuma yana sheƙi. Budurwa ce ajin farko mai kimanin shekaru ashirin da hudu a duniya.

Tanada bala'in juriya da dakewa, duk abinka da ita, bazaka ga wani gazawa a al-amuranta ba. Ko yaya matsala yake damun ta bazaka gansa a fuskanta ba. Hawaye kam idan tace tunda take bata taɓa kuka ba bazaka musa ba. Shi kansa ma murmushi za'a iya dirga sau nawa takeyi a rana.

Hakan bawai yana nufin da chan ta shiga wani ruɗani bane, a'a ita haka halittan ta yake. Akwai juriya da dakewa.

Matse ƙaramin towel ɗinda ke hannun ta tayi, sai ta sake shafa mashi a saman goshi. Bata iya haɗa ido dashi saboda ɗacin dake ji cikin ranta. Yana bala'in bata tausayi. Ita bata kuka, a yau tayi kishi da wanda suke iya kuka tareda nuna damuwan su ƙarara. Tabbas kuka rahama ne a tareda ɗan adam. Kukan zuciya wanda yafi na bayyane ciwo shi takeyi. Shi kam murmushi yakeyi tareda binta da addu'a cikin ransa.

Dattijo ne mai kimanin shekaru sittin da biyu, fuskan shi akwai furfura wajen girar sa da kuma gemun sa. Hannun sa yake kokarin motsi dashi inda ta miƙa nata tareda magana cikin sauri.

"Baba! Ina ke maka ciwo?"

Murmushi yayi sai yace, "Ba inda ke min ciwo Naseera, ki daina damuwa."

Daci kawai zuciyar ta ke mata, ga gudun dayake yi kamar jirgi. Tabbas BP dinta ya hau a yanda take jin kanta. Ita kaɗai tasan abinda ke mata ciwo. Saboda Zuciyar ta yana mata barazanar fashewa, ga kuma tausayin mahaifinta daya luluɓeta kamar bargo. Haƙiƙa an zalunce shi.

"Ki tashi ki tafi ya isa haka kafin supervisors su fara neman ki. Kada ace zaki nuna preferential treatment saboda ni Babanki ne."

"I want to be here," ta faɗa a sanyaye tareda ƙara saka towel cikin ruwa ta sake matsewa. Wannan karan wajen wuyan sa tabi tana gogewa. "Baba, bana so na rasa...."

Bata karasa magana ba sai ƙofa ya bude, "Assalamu Alaikum," aka ce yayin da wata dattijuwa ta shiga. Hannun ta cike yake da coolers.

Amsa sallamar Naseera tayi a dikilce saita miƙe tsaye tareda gyara mazaunin rigarta, "Baba toh bari na tafi zan dawo anjima... " shima bata kalle matar ba tayi maganar. Baza'a ce mugun kallo ta watsa ma matan ba amma Ƙaninsa ne.

"Allah ya maki albarka," saiya kalle matar data shigo, "Binti kice yarki ta daina damuwa. Zan warke in sha Allah."

Hajia Binti ta kalle Naseera fuskanta cike da annuri, "Yar Siri Siri, Naseeran Babanta naga tana jin gari, ciwon nan yasa ta sai kumbure kumbure takeyi, ita a dole Daddy's girl." Hajia Binti ta faɗa fuskanta babu damuwa.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now