Fifteen - Ƙarfi Yaci

996 168 30
                                    

Ta bada kudi murna fal ranta batada sauran matsala, martaban ta da yan kungiyar One Love yana nan. Ita kuma Rahina kuɗin anko ne aka tura mata zata tayasu siya tunda tasan kan kasuwa. Gashi Rumasa'u ta wawushe tayi gaba dashi. Da abin yakai ma Rumasa'u karo harda cewa tayi zata biya kuɗin Dj idan lokacin taron yayi. Tasan a lokacin zata samu kuɗade dayawa hannu Latisha ƙila ma suje tare.

Ganin ta gama da yan One Love da wuri sai tayi tunanin cewa gwara taje wajen Latisha tunda bata komai. Kuma Latisha a lokacin ta saka, "Bored" a status ɗinta. Gwara taje suyi hirarrakin duniya kala kala tunda itama she's bored. Sannan ba sai ta jira baban Latisha ba domin ya dawo, tunda bashi bane aminin ta. Cikin hira take tambayar Latisha unguwar su, anan tayi mata kwatance layin su a Jaɓi road dake Kaduna, tace mata gidan sananne ne a layin tunda yafi kowane gida girma. Balle kuma ginin ba kalar namu na gargajiya bane, an ginasa a yanayin jirgin ruwa ne watau ship.

Duk juma'a kuma Babanta idan yana gari haka mutane suke taruwa yayita bada bandir ɗin naira hamsin sabbi fil daga banki. Wasu suna samun biyu wasu har hudu.

"Besty gani nan zuwa dubaki yanzu," Rumasa'u ta faɗa mata ta whatsapp. Saboda sauri da neman gindin zama, Mashin ta hau domin taje gidan. Bata kawo komai ranta ba. Koda ta isa inda akayi mata kwatance ta tsaya, amma su kuma suka ce ba'a san kowa da suna Latisha ba. Sai tace masu ba lallai bane su santa saboda kullum tana cikin manyan motoci idan zata fita kuma bata ta'anmali da talakawa.

A lokacin ta kira wayan Latisha shima a kashe, ta tura mata kuma saƙo ta WhatsApp baya zuwa. Tun haɗuwarta da Latisha koda yaushe tana ganinta online, wannan karan ne na farko data fara tura saƙo baije ba. Hankalin Kankana ya soma tashi, mugayen zato ta fara bin Latisha dashi amma sai tayi maza ta kawar da zancen. Latisha batayi kamada kalar rashin gaskiya ba. Balle tabbas taga sanda ta fito a motar cefane kuma ita ta aminta da ita. Kuma yafi hasken rana bayyana cewa masu hannu da shuni basu karya. Talaka ne yake karya domin ya samu abinda zai ci.

Rumasa'u ta zagaye layin yafi na awa biyu domin jaraba ko Latisha zata gipta. Amma babu ita babu dalilin ta. Anan hankalinta ya sake mugun tashi ga kuɗin Rahina ta kashe tana tsammanin zata samu yau, basai Latisha taje banki ba.

Rahina kuma tasan kudin yana inda yake yasa bata bi kansu ba, gobe ne dama zata kasuwa. Jikin Rumasa'u yayi bala'in sanyi. Numfashi da kyar takeyi, tafasa kirjinta keyi saboda tasan yau zataci ubanta. Sai dabara ya faɗo mata akan tayi karyan cewa tayi gamo da yan fashi sun amshe kuɗin. Amma kuma ta ina zata soma bayanin yadda kuɗin suka shiga Jakarta? Yanke shawara tayi zata ce tazo tayata kaiwa banki ne tsautsayi ya faru. Dan yanzu batada inda zata samu kuɗi. Su Inna sun saida gidansu balle taje ta ƙwaƙule su.

Tana ɗaki tana zaune sai hakki takeyi, zufa ke karyo mata ta ko'ina sai taga wayan Latisha, cikin fushi Kankana ta ɗauki wayan. Saboda hankalin ta yayi mugun tashi. A dikilce ta kara a kunnen ta, "Haba Besty ina kika shiga?"

Gyara murya Latisha tayi cikin shagwaba, "ayya besty wallahi wayana babu chargi, kuma ni ban lura ba inata chatting. Dayake mu munada wuta koda yaushe, ko an ɗauke akwai solar power yasa ni bana zama gefen socket, shine ashe yayi ƙasa ya ɗauke."

Ajiyar zuciya Kankana tayi hankalin ta ya soma kwanciya, "kin sakani cikin damuwa, idan bakiso nazo gidan ku ai saiki faɗa min," tace cikin takaici.

"Haba Besty what are you talking about? Ina cikin karanta saƙon ki kafin na amsa wayan ya dauke." tace cikin shagwaba, "gani tun ɗazu nake bakin titi kina ina yanzu besty?"

"Ni ina gida wallahi nagaji da jira na tafi,"

"Ayya besty, gashi nasa chef ya girka maki Risotto da blueberry pancakes, sai kuma an gasa maki salmon tareda veggies,"

Nan take miyan Rumasa'u ya tsinke, bawai ta gane kalar girkin bane amma tanajin sunan ta tabbatar da cewa zaiyi daɗi.

"Eh toh saina dawo ai," tace tana duba agogon bango dake aiki. A lokacin karfe goma da minti ashirin na dare ne.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now