Six - Wanene Mahfooz I

1.2K 158 23
                                    

Wanene Mahfooz?

Mahfooz Abubakar Gwaiba yaro ne tilo a wajen Iyayen sa, Abubakar da Phalida. Dan asalin Zaria ne, dangin mallawa wanda ke zaune a gidan Gwaiba. Mahaifinsa ɗan kasuwa ne. Ya shiga sana'ar kasuwanci bayan ya kammala NCE a FCE Zaria inda ya karanta Maths/Chemistry.

Ba kowa ya koya masa sana'a ba illa yayansa Alhaji Sani Kwari. Shima Alhaji sani zuwa yayi Kano tun yana dako da zama a matsayin yaron shago harya kai shi ga samun nasa. Shi baiyi karatu ba. Yanzu haka yanada shaguna guda goma Sha shida a kasuwan Kwari dake Kano. Shi kuma Abubakar a kasuwan Sabon gari dake Zaria yake nashi, saidai yaje Kano ya saro.

Anan ne ya haɗu da Phalida har sukayi auren soyayya. Bayan shekara ɗaya da aure sai Allah ya albarkace su da samun yaron su Mahfooz. Saidai Phalida bata haihu da kanta ba. Cs akayi mata. Koda ta koma gida cikinta bai bar ciwo ba haka yayita ruwa yana takura mata.

Phalida batada aiki saina ziyarar asibiti, amma ya ki ci yaci tura. Haka dai suka cigaba da rayuwa yau ciwo gobe sauki. Lokacin da Mahfooz yakai shekara hudu sai Phalida ta sake ɗaukar wani cikin. Amma dayake babu rabo wajen haihuwa ta rasa ranta tareda babyn.

Hankalin Abubakar yayi mugun tashi, basuda iyaye balle a riƙe Mahfooz. Sannan kuma Alhaji Sani ne kawai namiji a ɗakin. Sauran duka mata ne. Yasan ba kasafai bane miji ya yarda mata ta ɗauki nauyin yaron daba nata ba. Koda agola ne balle yaron ɗan uwa.

Alhaji Sani ya cema Abubakar ya dawo da Mahfooz Kano wajen matarsa domin ta raina Mahfooz. Tunda yanzu haka yanada yara shida kuma autansa bata wuce tsaran Mahfooz ɗinba.

Duka yaransa shida mata ne, baida yaro ko ɗaya namiji. Shima zaiso Mahfooz ya zauna dashi domin ya koya mashi kasuwanci kala kala.

Matarsa Hajia Fauziyya yar ƙabilar Beri Beri ce na jahar Borno. Kuma a lokacin yaranta shida, akwai Aisha, Maryam, Zubaida, Anisa, Sadiya sai Zanira.

Alhaji Sani bai taɓa nuna ma Fauziyya cewa rashin haihuwar ƴa mace yana damunsa ba. Za'a iya cewa itace ta cusa masa ra'ayin saboda halinta. Sanda aka kai Mahfooz gidan babu laifi tana faram faram dashi. Saboda tana tunanin Abubakar zaiyi aure nanda nan su tafi. Ya girma Zanira da shekara ɗaya amma komai tare ake masu.

Harta Abubakar idan yaje Kano yana siyan masu kayan wasa iri daya baya nuna wariya. A gidan Alhaji Sani na Rijiyar zaki ilimin addini dana boko wajibi ne akan kowa. Yace ba'a taɓa daina neman ilimi. Harta shi yana tsayawa karatu a masallaci bayan Isha. Yasa itama Fauziyya tana zuwa Islamiya sannan kuma ta koma Sa'adatu Rimi inda tayi NCE domin ta ƙarasa.

Wata rana lokacin Mahfooz yana shekara shida Abubakar yace ya kamata ya sake aure domin ya dawo da Mahfooz Zaria wajensa. Har anje ankai kuɗin gaisuwan. Yaje kano domin yaga Mahfooz sannan kuma ya taho da kayansa na sana'a wanda yayi order.

Sun wuce tashan yari da ƙadan suka samu hatsari babu wanda ya rayu cikin motan saboda kurmus suka ƙone. Anan Alhaji sani ya sake jin tausayin Mahfooz sosai. Tun daga lokacin ranar Alhamis da Juma'a idan babu Islamiya zai aika a wuce da Mahfooz kasuwa.

Alhaji Sani yana bala'in alfahari da Mahfooz, yaron baida kiwiya shima yana jin daɗin zaman shagon. Gashi idan anzo miƙa leda ko compliment card shi yake maza ya bada. Sannan idan yaje gida yayita bama Zanira labarin yadda kasuwa yake sannan kuma da rana suna cin balagu da shinkafa kokuma kaza.

Babu abinda Alhaji sani ya raga ma Fauziyya dashi wajen fannin abinci. Fridge ɗinta yana ambaliya da nama dasu kifi. Saidai Fauziyya tanada wani abu, akwai ta da kyashi. Tanada bala'in kallon abin mutane. Ga kyamar talaka. Bata bada sadaka komin kankantar sa.

Batasan taga Alhaji Sani yayi wani abin alheri, bataso taga an bama makota taimako. Shi karin kansa zakka da ake bada wa bayan anyi ramadan na hatsi da ba dole bane bazata bari a bada ba. Abinci saiya lalace yana wari zata bama almajirai. Dama kawaici take ma Mahfooz, yanzu kuma haƙurin ta ya gaza.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now