Twenty-nine - By Whatever Means Necessary

1.4K 227 47
                                    

Mayar da hankalinta tayi akan laptop ɗin ba tareda ta ƙarasa maganar da zatayi ba. Shima ya lura da rashin dacewar maganar. Daga nan bai sake cewa komai ba. Suna cikin kallo basu wuce mintuna goma sha biyar ba sai aka tura ƙofa. A tare suka ɗaga idansu suka kalle ƙofa, lokacin Baba Abu ne ya shigo da basket wanda ke ɗauke da abinci.

Da sauri Labib ya miƙe yaje domin ya taimaka masa, shi kuma magana ya somayi, “Ah ah Doctor ! Kaine tafe? Ai bamu san zaka shigo dubamu ba.”

“Dama ina kusa da wajen ne, nace bari nazo na duba lafiyar mai jiki.” Yayi mashi ƙarya.
“Allah sarki mun gode, nima tun safe ban shigo ba sai yanzu.”
“Sannu da zuwa,” Naseera tace cikin ladabi.

Kallonta Baba Abu yayi yana murmushi, “Yauwa ya jikin ki?”
“Alhamdulillahi, dan Allah yaushe zan tafi?” tace cikin shagwaba tana sosa kanta.

Kallon Labib sukayi su biyu da Baba Abu, shi kuma sai ya soma tunani. Daga bisani kuma yayi ajiyar zuciya, “Bari muga zuwa juma'a mai zuwa idan komai ya tafi daidai sai a sallame ku in sha Allah,”

Ƙarara Naseera ta nuna farin cikin ta, saboda ta fara takura da Labib. Kawai haka kurum tafi ganin dacewar barinta asibitin. Gwara ta koma gida tayi rainon cikin ta, itama likita ce kuma idan taga akwai wani matsala da kanta zata koma.

Likitan dake duty ya shigo dubata, anan sukayi musabaha da Labib suka sake tattauna ciwon Naseera. Shi a nashi tunanin ko ranar zata iya tafiya domin komai yana tafiya daidai. Labib ne ya nace yace case ɗinta daban ne saboda HIV ɗin.

Tare suka fita da Dr ɗin inda Labib yayi masu sallama ya tafi. Shi Baba Abu bai kawo komai cikin ransa ba, yana alaƙanta kirkin Labib akan ƙabila da suke ɗaya watau na Hausa.

Ranar an kai gaisuwan Fa'iza, inda aka saka bikinta nanda wata uku. Inna taso ace Rumasa'u tana wajen amma ko ranar da safe bata ɗauki wayar ba. Ita kwata kwata ta riga ta yanke wani alaƙa dasu. Ranar Salima ta ziyarci Rumasa'u, a ranar Rumasa'u kwata kwata bata sakan mata fuska ba.

Ita a lokacin abin ya fita kanta, ta lura Salima mugun yar rainin wayo ne yanzu. Banda 5k ko abinci daga bakery babu abinda yake haɗasu. Ko makon daya wuce tace mata ta bata dubu hamsin tanaso tayi photoshot na nishaɗi.

Bata so mutane suce tunda tayi aure ba'a ga haskenta a social media ba, ita kuma Salima ta hanata. Shine itama Rumasa'u ta hanata kanta. Da Salima ta riƙo hannunta saita fizge a wayance. Abin yayi mugun bama Salima takaici. Babu arziki ta ɗauki jakarta ta tafi. Gashi yanzu duka yan matan ta bata fiye kulasu ba tafi san Kankana.

Abin yayi mugun ma Kankana daɗi, idan zasu rinka haka tana ganin zata gwada zuwa wajen Mahfooz taga ko zata haukace, ta soma lura cewa kamar Salima karya takeyi. Saidai bataso ta gwada kuma ace abin da gaske ne tabi duniya. Amma ta soma ma kanta faɗa kaɗan, tana auren namiji da matan duniya zasu je wajen boka ko malam domin su mallake shi, ita kuma ta same shi cikin ruwan sanyi.

Ranar da yamma tayi wanke wanke, saita tafasa macaroni zasu ci da miya, saida ta gama ta lura babu kayan miya tun sanda Mahfooz ya wanke fridge bai sake siya ba. Dabara ya faɗo mata, anan ta soya manja sai suci macaroni garau garau da manja. Haka ta saka a cooler, sai manjan cikin ƙaramin cooler. Sai ta kai dinning ta ajiye, daga nan taje tayi wanka. Dama tun ranar batayi wanka ba, sai ta saka riga da skirt na material.

Torquoise blue ne da lilac, ɗinkin akwai peplum sannan da beads a design ɗin. Ɗaurin turban tayi tareda fese jikinta da turaruka. Ranar tana neman sulhu da Mahfooz. Haka tayi ta zama tana jiran sa ya dawo amma bai dawo ba. Ganin gidan yakeyi kamar kurkuku, yasa baya san zama ciki.

Haka Kankana tayita zaman jiran sa tun mangariba har Isha, dama bawai sallah ya dameta bane balle taje tayi. Shikam gogan bai koma ba sai wajen goma da rabi. Tayi gyangyaɗi harta soma barci kaɗan kaɗan sai taji shigan sa cikin gidan.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now