Twenty-eight - To Be Tainted

1.1K 194 40
                                    

_Assalamu Alaikum Dimplicious Empire, barka da sallah da fatan na same ku lafiya? Allah ya maimaita mana cikin ƙoshin lafiya da walwala Amin. Wanda basuda da lafiya Allah ya basu, iyaye, kakanni da yan uwa da suka rigamu zuwa gidan gaskiya Allah ya jikan su, muma Allah ya kyautata karshen mu. Allah ya kare mu daga sharrin mahassada da kuma sharrin shedan, ya tsarkake mana zukatan mu daga aikin dana sani, Amin summa amin. A Ontario nayi sallah wajen Yaya Labib, kufa ? #FullyDimplated

Bayan sati biyu...

Salima bata fasa zuwa wajen Rumasa'u ba, duk lokacin data san Mahfooz baya nan saita lallaɓa taje. Bata nuna ma Rumasa'u cewa akwai komai ba, ko ta nuna mata tana jin haushin ta balle ta kawo komai cikin ranta ba. Zagon ƙasa take mata ita da Nurse Jamila, suna neman hanyar da zasu cusa Zubaida wajen Mahfooz harya aureta.

Boka ya riga ya buga ma Jamila ƙarya, yace mata Zubaida zatayi aure muddin sukayi abinda yake so. Cewa yayi yanada wani tsami daya shekara cikin wani ƙoƙo, kuma duk wanda yasha koda cokali ɗaya ne yana samun abinda yakeso. Amma da sharaɗi ɗaya, dole aje da Zubaida har Lokoja domin ya keɓe da ita shi kaɗai sannan ya shafa mata tsimin a duka sansan jikinta.

Abin duniya yayi ma Mahfooz cinkoso, komai ya cunkushe mashi. Bayada aiki sai yawan fushi da zafin nama. Rumasa'u ta gama ƙure haƙurin sa. Banda 'My Husband' datake ce masa idan ta gansa da safe, shima ba kullum ba babu abinda yake haɗashi da ita. Ya riga ya ɗaura ma kansa aƙidar rashin san kazanta, yasa duka aikin gidan shi yakeyi. Da safe idan yaje haɗa ma kansa shayi zai ga kitchen ɗin yayi kaca kaca, kuma duka daga kwamachalan indomie ko taliyan data dafa ne. Sai tayi amfani da tukwane uku. Saboda tanayi kana chatting ko tana kallon Reality show, Keeping Up with the Kardashians na 'E'

Haka zata babbake tukunya yayi baƙin kirin wanda saita canza sannan kuma ta sake maimaitawa. Tukwanen Naseera masu armashi wanda Hajia Binti ta siya cikin so da kauna, ƙananan ciki sune yan dubu arba'in. Amma Rumasa'u duk ta illantar dasu. Duk kayan kitchen ɗin ya halake, sannan kuma dan rashin hankali idan tazo zubar da abinci daga kwanan dataci, bata lura da cokula dake cikin kwanan haka take antayawa bola tayi gaba abinta. Gashi ta fasa flask ɗin ruwan zafi guda biyu. Kuma centre table ɗinta na tsakiyar falo yayi rotse.

Ta shagala tana kallon Kim Kardashian da kannenta a tsohon episode da suka je Greece suna ninƙaya cikin teku, abin ya bala'in burgeta. Tabbas wannan ne rayuwar daya dace da ita. Ba rayuwar datake ciki yanzu ba. Duk bayan kwana biyu Mahfooz yana ajiye mata dubu ɗaya akan dinning table domin tayi cefane idan taga dama. Subscription takeyi abinta babu abinda yasha mata kai. Tunda dai Salima itama tana sallamar ta idan taje. Garin kallon TV ne taji ƙauri indomie ɗinda take dafawa yana ƙonewa, saita tashi da sauri domin taje. Anan ta ingije centre table ya rotse.

Bayan nan, wata rana nepa sunata wasa da wuta ranar, daga su kawo low current sai su maida full current. Daga nan kuma sai su ɗauke su sake dawowa dashi. Ruma tana zaune akan three seater tareda ɗaurin kirji, ranar Salima bata jeba tayi tafiya. Mahfooz kuma tun safe wajen bakwai ya fice abinsa bama su haɗu ba. Bata tashi ta kashe kayan wutan taba. Kwan fitila na falo ya soma fashewa, tsaki tayi saboda ita kanta yana mata ciwo bazata iya motsa jikinta ba. Sai wayanta ya soma ruri. Sunan Inna ta gani dara dara amma tayi fari da idanu tareda taɓe baki.

“Nifa banida ko sisi,” ta faɗa a fili.

Ita kuma Inna tanaso taji lafiyar ta ne tareda sheda mata cewa Aliyu ya samu aiki a NBAIS dake rigacikun, sannan ran asabar za'a kai gaisuwan Fa'iza. Saurayinta wanda suke tare tun tana makaranta ya samu aiki a Federal Character Commission, shine take so Rumasa'u tazo ranar domin ayi da ita.

Amma haka wayan ya gama ruri bata ɗaga ba, tana kyautata zaton wani bukatar tasu ne ya tashi zasuyi mata maula, ita kuma ta daɗe da dawowa daga rakiyar talauci. Ta kasa gane dalilin dayasa suka ki rabuwa da ita kamar yadda ta share su. Wannan wani irin jaraba ne? Tayi ma kanta tambayar da babu mai bata amsar shi.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now