Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya

1.1K 171 39
                                    


Ontario, Canada

“Dr, the patient is breathing,” head nurse na cikin surgery ɗin ta faɗa da harshen turanci. A lokacin Labib ya dawo hayacinsa ya ƙarasa wajen da sauri. Jini ya daina fitowa saiya goge wanda yake wajen. Daga nan kuma komai yayi mashi sauƙi ya rufe mata kai tareda ɗinkewa.

Labib Mohammad Kakaki yanada dakarkiyan zuciya, ba kasafai abu yake razanar dashi ba cikin tiyata. Amma a karo na farko ɗaukewan numfashin Naseera ya girgiza shi. Idan yasan baza'a ci nasara a tiyata ba kokuma mutum yanada 30% chance of success, yana sanar da yan uwansa domin kada a tuhume shi. Wasu dayawa suna cewa ayi ɗin a gani rahamar Allah dayawa yake, kuma cikin ikon Allah Labib yana samun nasara kaɗan ne ba'a yi.

Surgery ɗin Naseera yayi kusan awa biyar anayi, Hajia Binti batada aiki sai kiran Baba Abu da Anty Jawahir domin taji yadda ake ciki. Tsoro takeyi sosai kada ta rasa Naseera. Gashi abu na karshe daya faru shine sanda ta wanka ma Naseera mari. Sanda ta kira na karshe lokacin ana fito da Naseera daga tiyata. Anan Anty Jawahir ta kunna bidiyo domin Umma taga Naseera. Taji daɗi sosai tagan ta kwance tana barci abinta babu firgici. Bayan Hajia Binti ta yanke wayan saida tayi raka'a biyu domin ta gode ma Allah. Tabbas shine abin godiya.

Ranar Mahfooz ya biya kasuwa ya siyo ma kanshi kayan cefane, yana jin cin sakwara da miyan agushi. Bai iyaba, kuma yasan Rumasa'u bazata dafa mashi ba. Sannan kuma ya gaji da zuwa gidan abinci, poundo flour ya siya wanda zai kwaɓa da ruwan zafi kamar teba, sai ya shiga YouTube domin yaga yadda ake girka agushi.

Tiryan tiryan abinsa yayita bin abinda ake cewa harya gama, bai wani daɗi sosai ba saboda ya cika Maggi da kuma manja. Bayan nan saiya wanke kwanonin dayayi amfani dashi tas kamar ba'a shiga ba saiya saka a cooler ya kai dinning. Ita kuma Ruma tana kwance ɗaki kamshi zai kasheta. Musamman yadda Mahfooz yayi amfani da kayan haɗi sosai. Daga kifi busarshiya da ɗanye, sai kuma kayan ciki da ganda. Harta periwinkles duka ya watsa.

Ya tafi bayi domin yayi wanka sai yayi sallah azahar saita fito falon, kamar yadda ta saba fuskanta shaƙe yake da make-up kamar zata biki. Jikinta kuma Atampha ne pink wanda aka watsa duwatsu a wajen wuya da kuma cikinta. Sai tayi ɗaurin turban tana wani fari da ido. Ita a dole yar hutu kuma yar gayu. Tanada kyan da zata janyo hankalin mai kallon ta.

Zama tayi akan dinning tareda ɗaukar kwano ta zuba ma kanta hankali kwance, yadda kasan mai aikinta yayi mata abinci. Shima yayi mugun shan mamaki yadda ya ganta. Anan ya tamke fuska tamau ya soma magana, “Watau dan kin maida ni baho shine ni zan rinka maki abinci koh? Wai Rumasa'u me kika maida nine dan Allah?”

Marairaicewa tayi tareda kane kane da fuska, “Wallahi dama zan shiga kitchen ɗin shine naga ka rigani,”

Tsaki yaja mai uban ƙara saiya janyo kujera shima ya zauna, sannan ya fizge cokalin saka abinci daga hannunta. Haka ya loda ma kansa kifi, kayan ciki, ganda da periwinkle, yanda kasan ya shekara da yunwa jikinsa. Tana kallo sai haɗiye miyau takeyi ta kasa cewa komai. Sannan ya ɗauki sakwara malmala biyu ya ajiye gefensa. Daga nan ya fara ci ko magana da ita baiyi ba. Haushinta yakeyi sosai amma babu abinda zai iya yi akai. Fata kawai yakeyi Allah ya kai masa sanadin rabuwa. Domin kuwa an daɗe ba'a laƙa mashi auri saki ba cikin anguwa.

Salima ta saba zuwa wajen azahar tunda Mahfooz zaman gidansa ya ishe shi, sai tazo su ha'ince shi kafin ya dawo. Yauma haka tazo da box of cupcakes wanda yasha decoration da waffles da oreo a sama. A waje ta ajiye motarta tunda ba dadewa zatayi ba.

Kai tsaye ta shiga cikin falon kamar nata, “Hello darling!” ta faɗa cikin raha. Duk tsammanin ta su kaɗai ne cikin gidan. Anan gaban Rumasa'u yayi mugun faɗi ta zaro ido tareda saka hannu a baki cikin tsoro. Sai kuma cikin tsoro ta soma magana.

“Gwaggo sannu da zuwa,”

A lokacin Salima ta gansa yana kwasan girki akan dinning. Abin yayi mugun bata haushi, sau da dama tana cema Kankana tayi mata girki, saidai ta ɓararraka mata wani kilafitaciyar indomie, wanda ɗanɗanon sa kamar an wanke kan tsohuwa. Ganin yawan naman dake kwanan Mahfooz gashi ma sakwara yake girba yayi mugun bata takaici. Shi kuma cikin ladabi ya rinsina ya gaida ta.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now