Twenty-one - Annihilation

1K 202 30
                                    

Golf stick dake gefe jingine da bango Naseera ta kalla. Tunani kala kala suka rinƙa faɗo mata, tabbas ance haƙuri shine gishirin zaman duniya. Amma wata sa'in amfani da barkono ba aibu bane. Idan ta sakan ma Rumasa'u fuska zatayi bala'in raina ta. Dole wani abun da kanta zatayi ba saita jira anzo anyi mata ba. Ɗaukar sandar tayi tareda murtuƙe fuska tamau, saita ɗaga muryanta sosai cikin masifa.

“Wallahi ! Wallahi!! Wallahi!!! Kinji na rantse, idan baki saukan min daga kan gado ba sai dai a tsinta gawar ki,"

Da farko Rumasa'u tayi banza da ita, sai taji alamar tafiya. Aikam da sauri ta sauka tareda matsawa gefe. Babu haufi Naseera ta bata mamaki, bata taɓa tsammanin zata iya magana ba kokuma tayi yadda tayi. Tun sanda suka haɗu a police station banda kuka babu abinda Naseera keyi.

“Yanzu dan rashin imani saiki kwaɗa min wannan sanda, dan kinci sa'a na kwanta a tsamin gadon ki mai warin fatsarin kwance,” sai taja dogon tsaki tareda fita tana watsa mata harara. Murmushi Naseera tayi, ashe ma Rumasa'u batada karfi yadda ta fita da sauri.

Raba dare Naseera da Mahfooz sukayi suna waya, su biyun basu taɓa tsintar kansu cikin wannan yanayin ba. Sauƙin san juna ke yawo a duk ilahirin jikinsu. Balle Naseera ta sauke fushin datake yi mashi tana tarairayan shi.

“Tauraruwa, dan Allah ki yafe min.”

“Na me kenan?”

“Duk abinda nayi maki, ranar da muka fara haɗuwa, yanda ban taimaka maki ba. I was wrong and I hate myself for it, na shiga uku Tauraruwa saboda kaina nayi mawa. Bake bane, kaina na cuta...”

“Shhhh!” ta dakatar dashi, har ga Allah ta yafe mashi. Sam yanzu bata jin tsanar sa saboda batun. Kawai tanaso ta gaya mashi gangancin dayayi ya saka mata ciwo. Ciwon da zai iya saka rayuwar su cikin barazana. Amma sai wani zuciyar ya raya mata, Mahfooz ya fita daban cikin maza. Shi ɗin bazai kyamace taba. Saidai har cikin ranta akwai faɗuwar gaba dake addabar ta. Saita alaƙanta shi da zaman Rumasa'u dake cikin gidan. Anan ta canza masu maganar zuwa wanda taga yafi dacewa da daren.

“Mijin Tauraruwa idan mun samu babies wani irin suna kake so a saka masu?”

Lumshe idanu yayi yana murmushi, da gaske shine keda iyali. Abin kamar almara. Gyara kwanciyar sa yayi ya kwanta rub da ciki. Sai ƙafar sa suna yawo a iska, a natse cikin bedroom voice ya amsa, “Tauraruwa ina san kisa Zanira, kinga bayan nan duk menene ni banda damuwa.”

“Uhmm....Zanira! Zanira!! Sunan waye halan? Your mum?”

“A'a,” ya amsa mata, saiya sha ruwa dake cikin roba a gefen sa, “Ba sunan mamana bane, ina santa ne... Amma she can't reciprocate yanzu saboda bata nan tareda mu,” yace cikin takaici. Bawai ya gaya mata Zanira bane domin yana so ya ɓata mata rai, ya gaya mata ne saboda tabbas yana san Zanira. Kuma ita ce ta soshi sanda duniya ta guje shi, bazai taɓa mancewa da hallacin datayi mashi ba. Sannan Naseera ta daɗe tana cewa yayi katanga a rayuwar sa, yasa ya fara gaya mata wani sashe a inda baida ɗaci ko takaici.

Ajiyar zuciya tayi, idan tace bata kishi da koma wacece Zanira tayi karya, amma kuma Mahfooz namiji ne. Haka Allah ya halicce shi, yanada sashe huɗu a zuciyar sa wanda Allah ya bashi damar ya cika. Duk abinta bangare ɗaya zata mallaka.

“Muna san ta,” tace mashi amma bai fahimta ba.

“Naji kace kana santa ne ɗazu, kuma ina sha nida kai yanzu mun zama ɗaya. Duk kalmar daya jiɓanci 'ni' ya koma 'mu' da fatan Mijin Tauraruwa ya gane," sai ta soma dariya. Shima dariyar yayi sosai, Naseera tana fahimtar sa fiye da yadda yake zaton wani ɗan adam zai fahimta ɗan uwan sa.

“Yanzu muna san Zanira, kuma idan mun samu baby girl in sha Allah abinda zamu saka mata kenan.” ta faɗa. Taso ta tambaye shi ina Zanira? Matarsa ce ko budurwar sa? Meya sameta ? Amma ta fasa. Ta lura baya san takura, zata haƙura randa ya shirya zaiyi mata bayani. In sha Allah kuma bazata bashi kunya ba. Yadda ya aminta da ita haka ita ta sallama ta aminta dashi.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now