Thirty-one- Miscreant

1.1K 196 42
                                    


Hello Dimplicious Empire, sorry for my abrupt silence. Abubuwan ne sai a slow, anyway in sha Allah I am back for good. Thanks for all the calls and messages. Godiya to Hajia Baby Nice for keeping me on my toes, Maman Eemad for dragging me back. Ƴan TASKAR AINAU DIMPLES ance kunyi quiet saboda bana nan sorry for that. Anyway y'all should remain fully dimplated. Don't forget to like, comment and share with your friends.

Jama'a nayi wata uku banci abinci ba, dan Allah a siya littafina Hasken Lantarki ta manhajan Okada ko na samu na kai wani abu bakin salati na. Link yana bio ɗina.

***

Yan biyu babu abinda ya samesu cikin ikon Allah. Sadiya ce ta buge a gwiwa inda jini ya taru saboda farin fata. Sannan tana dingishi kaɗan kaɗan amma bayan nan ita ƙalau take. Haɓon datayi a hanci shima ya tsaya.

Salima kuwa ƙafarta ne ya tsage, sai aka wuce da ita tiyata domin a dinka wajen. Kowa yana cikin jimamin mutuwar Jamila har lokacin. Suna mamakin yanda ta mutu da Darbuzu a bakinta. Al'ajabi suke suna tunanin irin saɓon da takeyi da bata samu damar mutuwa da sunan Allah ba. Aisha ce ta kira Anty Amina domin ta sanar da ita abinda ya faru. Tayi kiran duniya na mamanta amma bata ɗauka ba. Lokacin taje bayi tanata kukan kila Sadiya da yaranta sun mutu. Dana sanin abinda tayi sosai takeyi sannan tana kaico da Mahfooz. Duk wani masifa da bala'in duniya daya auku mata dashi take kuka. Harta idan taci tuntube Mahfooz take tsinemawa.

Cewa takeyi ta tabbata yana daga gefe ya laɓe yana kallonta yasa ta kusan faɗi. Anty Amina babu arziki ta faɗa ɗakin Fauziyya, bata ganta ba cikin falo saita wuce uwar daka. Yau yana cikin rana kwarara data taɓa shiga bedroom ɗin Fauziyya. Sam bata yarda kishiya ta shigan mata ɗaki ba, ko ƙawayenta bata yarda su shiga. Iyakacin su corridor da parlor.

“Me kike min cikin ɗaki?” ta tambayi Amina, a lokacin itama ta fito daga kewaye kenan. Cikin rawar baki da tashin hankali Amina ta soma magana.

“Kiyi haƙuri Anty, dama Aisha ce tace bakya ɗaukar wayan ki wai su Sadiya sunyi hatsari,”

Dayake Fauziyya tasan dawar garin bata kulata ba, dama jiran da takeyi kenan kafin ta faɗa asibiti ace ya akayi ta sani. Mayafi ta ɗauka tayi hanyar falo inda Amina tana bin mata baya, fafur Fauziyya ta hana Amina shiga motar saidai taje ta hau napep tunda bata iya tuƙi ba. Haka ta figa mota ta wuce, a hanya ne ta kalle wayarta inda Aisha tace ga inda suke ta saƙo.

Cikin ikon Allah Amina tana fita ta samu adaidaita sahu, sai tayi chata suka tafi. Idan ranta yayi dubu yayi mugun ɓaci amma babu yanda Amina zatayi da Fauziyya. Idan da sabo yaci ace ta saba da halin Fauziyya.

Lokacin Salima tana emergency ana dubata, hatsarin yayi mugun illanta ta. Gabaki ɗaya ta fita hayacinta.

Halimomo yar kungiyar su na One Love Kankana take so ta nuna ma bariki. A da chan da kyar aka sakata a kungiyar saboda kwata kwata bata iya wanka ba. Sannan batada kyau. Fatar jikinta tayi bleaching ɗinsa kamar mai shafa kumfar lux. Tayi kwana biyu bata social media kamar anyi ruwa an ɗauke, sai yanzu ne ta dawo da zafin ta.

Kamar Kankana itama Halimomo yar talaka ce, gwara Mallam Salisu yana koyarwa. Babanta kam yankan farce yakeyi a bakin tasha. Hotunan data soma bazawa ya firgita Kankana. Sannan gata koda yaushe gefen mota. Kirar Honda ce Camry 2016 model. Ga hannunta sun sha zobben zinare kuma ga hakorin Makka. Cewa tayi zatayi aure ta samu wani mai hannu da shuni.

Kankana ta tsani Halimomo, ko magana bata mata. Cewa takeyi kamar ƙanzo take duk abin kyama. Amma yanda Halimomo ta goge yanzu kamar ba ita ba. Tayi allurai da ake ƙara haske ba wancan wawan bleaching ɗin ba. Jikinta yayi luhu luhu sannan duk baƙin yatsunta babu shi.

Cewa tayi ya kamata yan One Love a haɗu a shaƙata, duk wanda ya samu lokacin ranar Asabar azo aje Crystal dinar, wani sabon wajen cin abinci na ƴan ƙarya. Roban Coca-Cola a wajen dubu ɗaya da ɗari biyar. Sannan roban ruwa kuma dubu ɗaya. Anyi haka ne saboda kada talaka ya samu ya shiga.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now