Two- Ruwan Sama

1.9K 209 61
                                    


Haka Ruma Sa'u ta zauna sai ciye ciye da lashe lashe takeyi, Rahina batada ƙaranci. Ta tabbata abinci bai tsinke mata ba.

WiFi ɗin gidan aka kunna mata tayi ta bi layi layi a Instagram, tareda amsa comments din da ake mata. Har yanzu dai Qwaro baibi ta kanta ba.

Cikin taƙama Mahfooz ya fito daga bayi, wanka yayi kana ya ɗauro alwala. Yadda yake abinsa zaka san lallai yana bala'in ji da kansa. Ash Jallabiya ɗinsa ya saka saiya wuce Masjid, bayan ya dawo sai yaje durowa ɗinsa ya ɗauko kayan kwallon sa. Miskili ne na bugun jarida.

Gashi ya shahara sosai wajen buga ball, za'a iya ce masa Messi ɗin Najeriya. Yaje Dubai sau biyu wani academy amma basu ɗauke shiba sannan har Under 17 ya buga ma Naija. Yanzu dai yana buga ma Kaduna United ne kafin ya sake samun wani waje a Turai. Sannan kuma shi civil Engr ne, yana aiki a wani campany Julius Berger.

Shima ya shahara a Instagram tunda an san shi duk ƙasar, Uwa uba gashi ɗan masu hannu da shuni ne. Baya rasa hotuna gefen motoci masu alfarma, sannan ya goge, ya iya saka sutura.

Yanada kyau kuma ya cancanci a soshi. Idan yana magana dole zuciyar ka zai ɗan sosu. Akwai hikima ga bala'in kwarjini. Yan mata kullum binsa suke yi suna crushing. Yana kula wanda yake kulawa ayi soyayyar shan miya. Tun farko zai faɗa maki cewa bai tashi aure ba. Sau da dama matan suna tunanin karya yakeyi. Idan suka gwada mashi madarar soyayya zai canza ra'ayi. Amma akasin haka suke samu, daga masu tsine mashi suna ya cuce su, bai aure suba amma sun bashi benefits ɗin masu aure.

Da Mahfooz ya gama saka kayansa, saiya ɗauki takalmin sa ya wuce filin ball. Bai kunna datan sa ba balle ya shiga Instagram. Kwana biyu baya jin daɗin jikinsa. Suna match da yan Eyimba United sai wani ya buge masa gwiwa, toh ya samu ƙaramin injury.

"Rahina me zaka yi ne?” Ruma ta tambayeta yayin da taga ta kwashe takardu ta nufe gefen data keɓe ma kanta a matsayin library.

" Wallahi ina da Impromptu test ne,” ta amsa.

“Inace kin gama, banaga hoton kinyi bautar ƙasa a Instagram ba??? "

" Eh, PGD nake yi,"

"Masters?” ta faɗa cikin sauri.

“Eh toh, bai kai Masters ba. Post Graduate Diploma ne”

Girgiza kai Ruma Sa'u tayi. Amma sam bata gane abinda Rahina tace ba. Ita a sanin ta. Kana gama degree sai masters daga nan ka zama professor. Abin yayi mata sabo wai wani abu PGD.

Rahina tana karatu ita tana chatting, anan tayi updating duka apps ɗinta. IPhone X ne ta siya a hannun wani friend dinta na One Love group. Clean wayace babu inda ya fashe.

Bature yace, "an ideal mind is a devil's workshop” kuma hakiƙanin gaskiya ne saboda tana cikin zaman banzan ta sai dabara ya faɗo mata.

" Bulala, nace ba... Ina admission letter ɗinki na degree zan duba abu ne, " Rahina bata kawo komai cikin ranta ba saita miƙe ta dauko files ɗinta. Anan ta ciro admission letter ɗinta na Kaduna State University.

Cikin murna Ruma Sa'u ta karɓa ta soma dubawa. Data faka idon Lala tana karatu saita ɗauki hoton admission ɗin. Bayan minti biyar saita miƙe tsaye tace zata tafi amma gobe idan Lala ta fito daga test ɗinta tayi kokarin kiranta sai su haɗu.

Ta soma tafiya zata tafi, dayake mirror ɗin yana gefen ƙofa, sai Ruma Sa'u ta ɗauki wani turare mai ɗan karin tsada ta saka Jakarta tareda faɗin, "Ina so," bata damu da ko an bata ba. Ita dai ta dauka.

Miyau mai zafi Lala ta haɗiye saboda taji haushin abin. Turaren yana cikin masu tsadar wajen sannan kadan tayi amfani dashi. Tana lura da Ruma Sa'u ɗazu datake wasan turaruka. Domin harta mirror selfie tayi dasu Video tana faɗin nanne ɗakinta.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now