Twenty-three - Ribar Haƙuri

1K 183 29
                                    

Da sauri Naseera tabar falon, kwata kwata bazata iya jure cin fuskan da Mahfooz yake yi ba. Farad ɗaya ya canza kamar maƙiyarsa ya maida ta. A chan ƙuryan ɗakin ta zauna a ƙasa, irin zaman dirshan kamar zatayi bori. Mamaki takeyi yadda komai ya juye farad ɗaya, masoyinta ya zama maƙiyin ta cikin ƙanƙanin lokaci. Sallar la'asar taji ana kira. Jiki babu ƙwari ta miƙe ta wuce bayi domin tayi alwala. Allah ne gatan ta, kuma bata cire ran zai fitar da ita daga cikin wannan uƙuba ba. Duk runtsi tana nan zata cigaba da addu'a, wata rana kuma zai zama labari. Tasan cewa Allah baya ɗaura ma bawa abinda bazai iya ɗauka ba. Hakan ya nuna tanada ƙarfin daukar wannan kaddaran ne. Balle ma a Q94 vs 05 Allah yace Fa'inna ma'al usri yusra. Wannan kawai yana saka zuciyarta yayi mata wani irin sanyi mai daɗi. Dole akwai ribar haƙuri, koda kuma ba yanzu bane.

An tsaida bikin Rumasa'u da Mahfooz nanda kwana huɗu, daga Amarya har ango fuskansu ƙarara da murmushi. Hajia Fatu taso tayi mashi magana akan ya daina rawar kai haka. Abin da kunya yace baya san yarinya ɗaya sannan ya nuna yana san ɗayan, abin kamar dama tuntuni haka yaso yayi. Faisal shikuma yana mota yana jiran Hajia Fatu ta fito domin su tafi, dama su uku suka je a motan. Anan Faash ya tafi yabar Mahfooz wanda yana tareda Rumasa'u tana mashi rawar kai.

Shi kuma Mahfooz yana ƙoƙarin ya saisaita zuciyar sa domin yaso Rumasa'u. Yarinyar tanada kyau, yar gayu ce amma kuma tanada bala'in rawar kai. Saidai kuma rawar kai ba abu bane dazai saka aƙi auren mace. Idan tana sanshi wanda yanada tabbacin haka, yasan zata yarda ya koya mata yadda yakeso so su tafiyar da rayuwar su. Zata kuma maye mashi duk wani ɓurɓushin soyayya dake tsakanin shi da Naseera. Murna sosai yakeyi ya tsallake rijiya da ƙafar baya.

Ita kuma Rumasa'u sarai tasan Mahfooz baya santa, tasan cewa Naseera ta fita komai. Bawai tana nufin ta kyan fuska da kyan jiki ba, idan wannan ne Naseera bata kai rabin ta ba. Tana nufin kyan zuciya, natsuwa da sanin ya kamata. Tana kishi da Naseera sosai akan wannan abubuwa, ita koda ta tursasa zuciyar ta domin tayi bazata iya ba. Duk abinda bai jiɓanci samun kuɗi ba batada juriyar yinsa.

Mahfooz ya kashe kuɗi sosai saboda bikin nan, yanaso yaga duk me Tauraruwa takeso ta samu babu ƙaranci. Amma yanzu komai ya koma kan Rumasa'u wanda tafi da cewa dashi. Shi yasan tabbas zaiji daɗin auren nan, koba komai Rumasa'u tafi sanshi kuma zatayi mashi biyayya ainun.

“My love zaka bani kuɗin lalle, sai kuma na saloon za'a min full spa. Zanyi maka list anjima na bridal shower...” ta soma gaya mashi. Wannan kawai ya bambanta ta da Naseera, da itace idan bai kawo shawara ba bazata taɓa tambaya ba. Sai kuma wani zuciyar ta raya mashi dama duk salon yaudara ce. A duniyar nan ina zakaga mace mai kunya da rashin san kuɗi? Duk tanayi ne domin ta yaudare shi harya aminta da ita.

“Muje Havilla musha ice cream My love,” ta sake faɗi. Kallonta yayi yana nazarin irin zaman da zasuyi. Tanada bala'in surutu kamar ta haɗiye radio. Amma kuma saiya tuna cewa shedan ke mashi wasiwasi akan yaga aibunta. Duk makircin Naseera ne. Wanda kuma ba'a ko'ina ta gada ba illa wajen mahaifiyarta Fauziyya. Allah wadai yayi da su biyun cikin zuciyar sa, tabbas sunada shika shikan rashin imani. Jin daɗin sa ya ƙubuta yanzu, zai aure yarinya mai usuli asalin yar Dr Abdallah.

“Babu mota a hannuna, ki bari zan maki aike anjima.” Yace tareda miƙewa tsaye. Har gate ta raka shi tana rangaji kamar reshen bishiya. Mahfooz Qwaro zai zama angon ta, gashi itace yar Dr Abdallah, what more could she ask for?

Napep ya hau ya wuce gida, koda ya isa Daddyn Faash ya sake kiransa ɗaki domin su zanta. Yace masa kada yayi saurin yanke hukunce cikin fushi. Ya kamata ya duba lamarin nan sosai. Aure ba abin wasa bane, kuma bai kamata ana saki kara zube ba. Ba tursasa masa yakeyi ba, duk abinda yake so shi za'a yi masa, kawai yanaso yayi amfani da hankali ne wajen komai. Ƙeƙeshe idanu yayi yace yaji ya gani. Tunda sukeda Mahfooz basu taɓa ganin yayi kafiya kamar wannan ba, bai taɓa yin abu wanda yasan zai kawo masu tozarci ba. Komai nashi yana ƙokarin ya faranta masu ne. Sai Mahaifin Faash yayi mashi uzuri. Ya lura Naseera ta ɓata mashi rai sosai, anan yayi mashi fatan alheri tareda addu'a akan aurensa.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now