Eight - Mahfooz III

1K 163 14
                                    

Koda ya buɗe idansa ganin wani abokin kasuwancin Alhaji Sani yayi a gefensa. A lokacin bai tuna komai ba, kallon kallon suka soma. Shine ya miƙe ya je ya riƙe ma Mahfooz hannu.

"Mahfooz ka tashi? Ya jikin naka?"

A lokacin abubuwa suka fara dawo ma Mahfooz, sai yaga ƙarin ruwa yana shiga jikinsa. Kaɗan kaɗan komai ke dawo masa, kamar a mafarki ya tuna abinda ya faru da Zanira. Wani ne ya shiga ɗakin yana magana.

"Musa kazo fah, za'a yi mata sallah,"

Anan Mahfooz ya tuna komai tas, buɗe ido yayi yana kokarin ya zauna. Musa ne yazo da sauri ya riƙe shi. "Likita yace a bari ruwan ya gama shiga jikinka domin ka samu lafiya sosai."

Wani ɗaci ya turnuke Mahfooz saiya soma kallon Musa cikin ido sannan ya fizge ƙarin ruwan, hawaye yana malalo mashi kamar gudun famfo. Shi kaɗai yasan me ke damunsa. Kwakwalwarsa tafasa yakeyi. Komai sabo yake dawo mashi. Yana ganin yadda Zanira take sauri zata wajensa. Sannan sanda mota ta ɗauketa.

Runtse ido yayi ya cigaba da hawaye yana shesheƙa kaɗan kaɗan. Dafa bango yayi yana kokarin miƙewa. Anan jiri ya debe shi saida ya zauna. Kallon Musa yayi da kyar ya iya furta, "ruwa"

Roban Swam dake gefe ya miƙa mashi. Tas Mahfooz ya shanye ruwan yana ajiyar zuciya. Da kyar ya samu ya miƙe kuma. Bayi yaje domin yayi alwala, dole yaje sallar Zanira. Itace gata na karshe da zai nuna mata.

Jallabiya ya ɗauka yasa saiya fita. Kansa yana mashi ciwo kamar ana sarewa da gatari. Ko sanda ya isa an soma kabbara. Sahun baya ya samu saboda yawan mutanen.

Zanira tayi mutane sosai, yarinyar tanada mutunci yan anguwa kuma sun sheɗeta. Kowa yana tausaya ma Alhaji Sani saboda ita kaɗai ce wanda ta gaje shi a kirki. Sannan kuma kowa da yaji labarin yadda mota ya kaɗeta saiya tausaya mata.

Da aka zo ɗaukar gawan a makara sai Mahfooz yaje, a lokacin Alhaji Sani ya ganshi. Shi yafi tausaya ma Mahfooz akan shi. Dama dama shi yanada sauran yaran. Amma Zanira ce kaɗai ta rage ma Mahfooz gashi yanzu ta rasu itama. Dan shima yasan cewa baya nan sanda Mahfooz yafi bukatar shi. Zanira ce take tareda shi tun zuwan sa gida.

Tare suka jera kowa da abinda yake ayyanawa cikin ransa, zuciyar Mahfooz sai raɗadi take mashi. Haka aka kai Zanira gidanta na gaskiya. Gidan da kowane musulmi yake jiran zuwa. Saidai muyi fatan idan lokacin mu yazo Allah ya sa mu cika da imani.

Kulle kansa yayi a ɗaki yayita rusa kuka mai tsuma rai. Ya kasa saisaita tunani waje ɗaya. Komai ya cushe masa. Idanun sa jazur kamar garwashi. Gashi shima yana jinyar jikinsa amma baicin abinci kwata kwata. Da kyar ya yarda aka ƙara mashi ruwa shima ganin Alhaji Sani yana gefe ne, bai ce mashi komai ba. Yasan abinda yake tunani cewa kada shima ya mutu.

Yasan dole akwai mutuwa, amma bai taɓa tunanin mutuwa nan kusa. Yadda Zanira ta rinka yi kamar tasan cewa zata mutu. Abin ya sake mashi ciwo da yaji cewa wai Zanira ce ta gansa daya suma.

A da duk wani soyayya dayake ma Zanira ashe kaɗan ne, yanzu ya gane yana bala'in santa. Yanzu ne ya gane amfanin ta. Dan kam da tanada rai yanzu dolen sa yayi completing treatment ɗinsa babu gardama kota soma masa rigima tana zuciya.

Zanira ce ransa kuma Fauziyya ta ɗauke mashi ita, ta raba shi da abinda ke saka shi farin ciki duk duniya. Yasan alhakin sa ne ya kama Fauziyya akan yaranta. Amma akwai sauran yaran ai. Meyasa mutuwa zata ɗauke mutum ɗaya dake jin ƙansa a wannan azzalumin duniyar.

A ranar ya kashe wuta zai kwanta, anan ya kunna da sauri. Firgici da tsoro ya kama shi. Tuna mashi yayi da zaman kabarin sa. Anan ya sake buɗe sabon shafin kuka. Tabbas Fauziyya ta cuce shi

Ranar da Zanira ta cika uku, bayan sunyi asuba a Masjid da Alhaji Sani. Mahfooz ɗakinsa yaje ya kwashe kayansa tas, saiya rubuta wasika ya ajiye ma Alhaji Sani a ɗakinsa.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now