Nineteen - Naga Wajen zama

1.1K 185 40
                                    

Ikon Allah Naseera ta tsaya tana kallo, mamakin irin ƙarfin halin Rumasa'u takeyi. Wanda ita kuma banda Allah ya wadai da ita bata komai. Tanata cewa tasan sirrin ta, kuma ita ba yar Dr Abdallah bace. Mamakin yadda Rumasa'u ta san wannan sirrin takeyi.
“Lafiya? Daga ina kuma dangin mahaukaciya?” Barira mai aikin su ta faɗa, riƙe Rumasa'u tayi tana jijiga ta tareda zare mata ido.
“Nace daga ina kika shigo mana cikin gida?”
“Ni ce asalin yarinyar nan gidan, wannan yar damfara ce,” tace da karfin tsiya.
"Ke kam baiwar Allah haka aka ce maki ana yi? Kizo cikin gidan mutane kamar sabuwar hauka kina surutai marasa dalili,” sai Barira ta soma zare mata ido da kyau, “Ki natsu kizo ki fita kona tara maki gajiya kuma na fitar da ke.” ta gargaɗe ta.
A lokacin Dr Abdallah shima yazo yaga me yake faruwa. Kallon Rumasa'u yayi sosai sai yayi gyaran murna. Da sauri ta fizga kanta daga riƙon da Barira tayi mata, wajen sa ta ƙarasa tanaso ta rungume shi. Shima da sauri ya kauce mata.
“Daddy na dawo,"
“Daddy asalin ƴarka ta dawo,”
“Daddy anyi maka musaya ne da wancan a asibiti, amma yanzu nagane gaskiya na dawo domin mu zauna cikin jin daɗi da walwala.”
Kallon Naseera yayi wanda ita kuma tana gefe ta kasa haɗa ido dashi. Tabbas ita ba ƴarsa bace kamar yadda yake tsammani.
“Baiwar Allah daga ina kike?” yace mata cikin ƙaramin murya.
“Ai Daddy anan garin nake,” ta amsa tana washe baki kamar gonar auduga.
“Kuma kika ce kece asalin yarinya ta?” ya tambaye ta, ya lura batada hankali. Kuma amfani da ƙarfi bazai ƙubutar dasu ba. Gwara lallami da salama. Anan ta zayyana mashi abinda taji Inna wanda take tunanin iyayenta ne suna magana akan tabon haihuwa a hannun Naseera, kuma tanada tabbacin cewa ita ce yarta. Sai kuma Rumasa'u ta ƙara da faɗin cewa dama ita tunda ta tashi daga gidan bata wani san yan gidan. Tanaji cikin ranta ita ba ƴarsu bace. Sau da dama tana mafarkin rayuwa cikin hutu wanda yafi dacewa da ita.
Umman Naseera ne ta ƙarasa wajen itama, sauƙi ya samu fiye da yadda take ji da tun isowar Naseera.
“Hayaniyar menene wannan?” Umma tace.
Da sauri Rumasa'u ta sake rugawa wajenta, “Lovely Mum, yarinyar ki ta dawo. Ni ce kika haifa. Na daɗe ina sanki tareda begen ki cikin raina. Maƙiya suka rabamu,” saita riƙa mata hannu.
“Toh ke yanzu dan kinji ana magana sai ki faɗo min gida kice kece ƴata? Bakida ilimi ne halan? Koko kina tunanin haka akeyi?” Dr Abdallah ya katse ta.
Juyawa tayi ta kalle shi, saita soma takawa inda yake. Da hannu ya dakatar da ita karta ƙarasa wajensa. Anan ta ƙame kamar an dasa ta a wajen.
“Daddy kana zaune da wancan bakayi binciki ba, meyasa kake so kayi dogon bincike a kaina? Meye takeda shi wanda ni banida shi?”
“Hankali” kowa ya ayyana cikin ransa harta Barira dake gefe tana kallon drama.
Umma ta ƙarasa gefen Naseera wanda ke kuka tana karkarwa, tashin hankali take ciki mara mitsaltuwa. Saboda idan wanda ta gani tareda Rumasa'u jiya itace mahaifiyar ta yafiye mata akan Fauziyya da Mahfooz yake alaƙanta ta da ita.
“Fitar min daga gida. ” Umma ta waigo tace mata babu alamar wasa cikin idanta. Zaro ido tayi zatayi magana sai Dr ya nuna mata hanyar ƙofa, “Get Out my friend!” saiya daka mata tsawa.
“Kika sake shigo mana cikin gida sai hukuma sun rabamu,” Umma ta jaddada mata.
Barkewa da dariya Rumasa'u tayi babu kakkautawa, yi takeyi tana jijiga tareda tafa hannayenta.
“Mommy! Daddy! Ai yanda Allah ya haɗamu babu abinda zai rabani daku wallahi. Amma idan karya nakeyi, meyasa ita wancan ta tsargu idan ita asalin yarku ce?”
Kallon Naseera akayi wanda akwai alamar rashin gaskiya tareda ita, ja da baya ta somayi tana girgiza kai. Kuka wanda ya zame mata game jiki taketa rapkawa. Mahfooz ne ya faɗo ɗakin, yafi minti biyar da shiga gidan baiga kowa ba, sai yaji hayaniya yana tashi shine yazo gani. Jikinsa ya soma tsuma dayaga Rumasa'u, ya ɗauka shi taje nema.
“Ke wai mayyar Inace, ana dole ne?”
Murmushi tayi harda kashe masa ido, “My love Rumasa'u kake ji wallahi. Idan na saka rai a abu babu yanda za'a yi dani. Amma bari kaji komai yazo gidan sauƙi, nasan saboda kuɗin nan gidan kake san wancan. Karka damu ni ce asalin yar gidan ba ita ba.”
“Bangane ba?” ya faɗa tareda bin duka yan ɗakin da kallo. Dr ne yayi kokarin faɗa mashi abinda Rumasa'u tace, sai Barira tace ai sanda ta shigo saura kaɗan kila da Rumasa'u ta kashe Naseera. Domin fatali takeyi da komai. Anan Mahfooz ya zuciya, mai taɓa Naseera saiya shirya saboda bazai kyale shiba. Zuwa yayi saiya rama mata marin, itama cikin zafin nama ta dafe kumatu ta soma masifa.
“Yanzu akan wannan korarriyan ka mareni My love?”
Haska mata wani yayi saiya finciko mata hannu, janta yake har suka kai farfajiyar gida. Suma su Dr ana biye ana kallon su. Aikam sai Rumasa'u ta ganna mashi cizo mai zafin gaske. Saita ruga bayan Dr Abdallah ta ɓoye tana kuka, “Dan Allah Daddy ka cece ni, wallahi banaso na tafi,”
Saiga Mahfooz ya dawo ya sake damƙeta, riƙo mata kugu yayi wannan karan. Figanta ya somayi kamar akuya yana ja. Haka tayita tirjewa shikuma yana ɗanɗasa mata mari har suka kai bakin Gate. Anan ya saketa.
“Fita dan ubanki, mara hankali kawai !”
“Wallahi baku ga karshe na ba, bari naje na kira Nafisa domin tayi maku bayani,” tace tana kuka. Su duka suna tsammanin Nafisa kila ƙawarta ne ko malaman asibiti. Basu san cewa Nafisa itace wanda ta haifeta ba take kira gatsal. Itama bawai taso tace mata Nafisa bane, amma bata taɓa zuwa Makka ba, bama Makka ba ko nan Chadi balle tace mata Hajia. Kuma yanzu basuda gami da juna. Sun kusan yin marabus na dindindin.
Takalmin ƙafarsa ya cire ya jefeta dashi wanda yasa ta ruga a sittin tayi titi tana zage zage. Sai ya koma cikin gidan da sauri, wajen Naseera yaje domin yaga lafiyar ta. A ɗurkushe ya ganta tana kuka cikin kuryan ɗaki.
“Tauraruwa...” ya kirata a natse. A hankali ta ɗago idanta jajaye mai kamada garwashi. Duk jikinta baya mata daɗi.
“Tauraruwa ta tafi. Ki daina kuka bazata sake takura maki ba,” saiya janyota ya riƙe. Buga mata baya yakeyi a hankali.
Kai tsaye Rumasa'u taje gida, dayake Asabar ne Mallam yana gida. Daga zaure tayita kwaɗa kira, “Nafisa ! Nafisa!! Nafisa!!!” daga Aliyu har Fa'iza sunji kamar muryan Ruma, amma kuma sun san bazata kira Inna da sunanta gatsal ba. Saida ta shigo cikin ɗakin tana haki kamar mayunwacin zaki. Riƙo ma Inna hannu tayi tana so taja, “Nafisa dan Allah kizo kice ma iyayena na asali ni ce yarsu. Naje nayi masu bayani sunƙi amincewa dani.”
Kallonta kowa yayi tareda yin shiru, ɗakin baka jin komai bayan fanka dake wal wal a saman ceiling. Mallam ne yayi dogon ajiyar zuciya ya fara magana, “Uwar mu, yau kuma tanan kika ɓullo?”
Ta juya a fusace zatayi mashi rashin mutunci amma ta kasa. Ganin yadda ya tamke fuska ga kwarjini ta ko'ina yasa ta bari. Tasan cewa idan tayi mashi ba daidai ba zai lallasa mata duka. A hankali ta soma magana.
“Wallahi Mallam naji abinda Nafisa take cewa jiya....”
“Waye Nafisa?"Mallam ya tambayeta babu wasa fuskan shi.
“Ina nufin Inna... Kuma dama ni tuntuni kamar yadda kuka sani ne bana jin daɗin zama cikin gidan nan. Zaman da mukayi Allah ya amfana amma inaga lokaci yayi da zan tafi gidan mu. Koba komai zaku hutu da masifan da kuke ikirari ina janyo maku. Nima zan huta da wahala, kowa zai huta...”
“Rumasa'u kar kiyi min haka Dan Allah...”Inna tace saita barke da kuka.
“Bafa maganar nan.... Karma ki soma dan saina tafi wallahi.... Atoh dai gwara kiji, yanzu babu salan yaudara da zaki bini dashi kuma.”
“Waya hanaki tafiya?” Mallam yace mata. Harga Allah ya gaji da bala'in ta. Kamar aljana take abubuwan ta kuma shi yanzu ya saka mata ido ne. Rawar baki ta somayi ta rasa ta inda zata ce masu tana so Inna ta bita ne domin tayi masu Dr Abdallah bayani.
“Inna kema ya kamata kiga asalin yarinyar ki, daga gidan nake amma basu yarda dani ba, yasa nace kizo muje kiyi masu bayani.”
Aliyu ne wanda bai fahimta abinda ake faɗi ba ya tambaye su, Inna cikin kuka ta zayyana mashi tun daga haɗuwarta da Naseera a police station zuwa jiya. Kuma tayi mashi bayanin tabon haihuwa a jikin Naseera. Kuma tace bawai tanaso ta ɗauko Naseera bane, tunda tanada aure kuma ta gina rayuwar ta. Aliyu shima ya gaji da Rumasa'u, fata yake wancan ta zamto yar uwansa. Su yarda kwallon mangwaro su huta da quda. Shine yace ma Mallam su tafi suga inda Rumasa'u take magana.
Chatan Napep akayi masu suka tafi harda Fa'iza, lokacin Mahfooz yakai su Arɗo Bello tasha baya gidan. Falon ana zaune ana karin kumallo. Kunun gyada suke sha da kosai. Anayi ana taɓa hira jefi jefi tareda kallon Sunna TV. Basu sake maganar abinda ya wakana ba.
Mai gadi yazo yayi sallama yace ana kiran Dr a bakin Gate, bai kawo komai ransa ba yabi sahunsa suka je. Anan Mallam ya miƙa masa hannu suka gaisa. Ya rasa ta inda zai fara masa bayani, abin babu tsari kamar mahaukata rana ɗaya suce wai ga zance ga magana. Saidai kuma tunda Inna tace tana jin haka toh gwara suzo a ƙarƙare. Rumasa'u ce ta sauka daga napep, anan Dr ya ganta sai yayi kwafa. Ya gane me yake tafe dasu, sai yayi masu izini domin su shiga. Koda Naseera ta gansu saita yarda Rumasa'u da gaske tanada bala'in naci. Wannan shine ya muka iya da wanda ta gagari wuta, wai inji kishiyar qonanan.
Duk sun zauna an gaisa, sai Mallam Salisu ya masu bayanin abinda suke zato. Dr Abdallah ya karyata zancen saboda baya tunanin anyi musaya. Anan Naseera ta dakatar dashi ta wuce ɗaki, koda ta dawo tareda takardar DNA dake nuna cewa ba ƴarsa bace. Saita miƙa mashi domin ya karanta. Salati yayi sosai, daman shi kaɗai yaga abinda ke takardar. A haka kuma saiya sake dakewa, bazai taɓa barin Naseera tabar gefensa ba, koda kuwa ba ita bace ƴarsa. Ita ya sani kuma zaije kotun duniya domin ya amshe ta. Balle kuma ta wuce shekara sha takwas yanzu zata iya zartar ma kanta hukunci. Bazai taɓa bari taje gidan mutanen nan marasa ɗa'a ba, kafin ta soma ta'ammali dasu ta zama yar tasha. Koda yake ya lura Rumasa'u ne kawai takeda hayagaga. Fa'iza wanda a ƙasa ta zauna akwai natsuwa a tareda ita. Sunkuyar da kanta tayi ƙasa bata sake cewa komai ba bayan ta gaida su. Rumasa'u ce taketa bin ɗakin ta kallo tana yatsina fuska. Ita kuma ta soma tunanin kalar fentin da zata sake yi a falon, kwata kwata bata san farin gida. Dama dama ace kila purple ko green.
“Toh yanzu me kuke so nayi maku?"Dr Abdallah ya tambaye su. Inna ce ta soma kuka amma bata ce komai ba. Tasan batada bakin da zatace wani abu ba, bayan sun tarbiyyantan da ita sun aurar. Banda ma sakayya ba abinda zata bisu dashi. Kawai dai taso tasan gaskiya ne.
“Haka kurum zamu zauna dake cikin gida baiwar Allah bamu sanki Ba? A ina kika taɓa ganin anyi haka?” Hajia Binta tace. Baƙin ciki mara mitsaltuwa takeji, kwata kwata bataso zancen su ya kasance gaskiya. Harta mugun tsanar Rumasa'u, kuma ta rantse bazata zauna gida ɗaya da ita ba. Saidai idan Dr Abdallah zai saketa amma bazata zauna da wannan goggagiyar cikin gida ɗaya ba.
“Toh ai sai ayi autopsy a duba... Abu daya jiɓance zamani ga autopsy anayi,” Rumasa'u tace. Kunyar duniya ya soma ɗawainiya da Aliyu da Fa'iza, Mallam shima haka ya dafa kai. Meyasa Rumasa'u take san zubar masu da mutunci duk inda aka je. Barira mai aiki wanda ta fito kawo masu ruwa a jug tayi mata magana, “Sisin gaye DNA ake cewa. Autopsy sai kace za'a yi ma gawa. Koko nan wajen mutuary ne?” tace mata cikin masifa. Dama ita batada wasa kuma Hajia Binti tana jin daɗin aikinta. Itace take taka ma mutanen da suke kawo masu shawagi birki.
“Koma meye sai ayi min a gani ai.” ta sake faɗi. Soyayyar zama a gidan shigan kowane sansa na jikinta yakeyi. Yasa babu inda zata. Dr Abdallah ya yanke shawarar za'a yi ma Rumasa'u DNA test, yace mata taje Abdallah Specialist yanzu ayi mata test, sunada sample ɗinsa a chan sai ayi comparing, saidai results sai ranar Litinin zai fito, tunda ran Asabar ba'a wani aiki sosai asibiti. Fafur taƙi fita wai bazata je ko'ina ba. Zata zauna anan har Litinin ɗin.
Mallam yayi juyin duniya tazo su wuce, tanata kuka bazata tafi ba. Suna cikin artabu ne saiga Mahfooz ya dawo. Anan ta shiga taitayinta ta nufa hanyar ƙofa, tanayi tana watsa mashi zagi tareda Allah wadai da hali irin nasa takeyi. Shikam ya zaro belt ɗin wandonsa yana zare mata ido, idan batayi wasa ba zai lailaya mata jiki. Aliyu ya bala'in jin daɗin abin, kuma yana fatan Rumasa'u ta zauna a gidan, koba komai Mahfooz wanda baisan alakan suba zai koya mata darasi. Ba tabi su Inna ba, hanyar ta ta nufa taje wajen Hajia Salima. Domin ita kaɗai ce zata taimaka mata taci wannan yaƙi. Balle tayi aiki a ministry ɗin kiwan lafiya, tasan yadda zatayi a murɗe DNA ɗin a saka sunanta a matsayin ɗiyar Dr. Idan tayi mata wannan ta ɗauki alwashin duk meta ke nema hannunta zata bata, duk muninsa.

Wannan kenan!

#Naseera
#Mahfooz
#Rumasau
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated


Ainakatiti 💫

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now