Twenty-four Bazan Barka Ba

1.3K 193 43
                                    


Da asuba Dr Abdallah yaje ɗakin Rumasa'u domin ya amsa number ɗinsu Malam. Ya lura da gangan ta hanasu zuwa saboda bataso tayi ta'ammali da talakawa. Fuskan san a murtuƙe sanda ya shiga, tana gunguni amma babu yadda zatayi. Dole ta bashi inda ya kira malam. Da kanshi yaje gidan inda ya sanar dasu komai. Bai ɓoye masu komai ba ya sanar dasu yadda abin ya faru. Daga auren Naseera zuwa na Rumasa'u. Ran Inna yayi mugun ɓaci, hakanan ranta yaƙi kwanciya da cewa babu hannun Rumasa'u a cikin rushewar auren. Yafi hasken rana bayyana cewa Rumasa'u batada mutunci. Mallam Salis yayi alkawarin zai halarta ɗaurin auren sabida DR Abdallah yace shine waliyin Rumasa'u tunda shi ya raine ta. Ta wani fanni Malam yaji daɗi sosai tunda abin ya nuna cewa Rumasa'u ta ƙare tareda iyayen mutunci. Inna itama sabuwar Atampha data ɗinka ta ɗauko domin ta saka. Ko bata je domin Rumasa'u tanaso taje taga Naseera, har yanzu ba'a tsaida maganar mai ƙarfi akanta ba. Dr Abdallah yace baisan wani zance ba, Saboda Naseera ƴarsa ce kuma yana san abinsa, idan suna so ayi zumunci a matsayin cewa Naseera yar uwan Rumasa'u ne suzo, amma kada su kuskura suce yarsu ce kafin hukuma su shiga tsakanin su.

Ita kuma Naseera ranar a ƙasa kan kapet ta kwana. Tunani kala kala suka rinƙa rikito mata. Yadda taga rana haka taga dare. Tun tana iya fitar da hawaye harta koma kukan zuci wanda yafi na bayyane ɗaci. Ga kuma cikin jikinta, sannan shima karin kansa yana takura mata saboda zuciyar ta sai tashi yakeyi. Uwa uwa ga HIV mugun ciwo yana damunta. Hasashe tayi ma kanta kuma tabbatar da cewa duk faɗin duniya babu wanda yake cikin matsalar dayafi nata. Chan daga baya ta tuna cewa Fauziyya ce mamanta. Bata san me Fauziyya tayi ma Mahfooz ba, kuma tasan fushin nan dayake yi rabi akan tanada jini da Fauziyya ne, saidai abinda ta sani shine kamar soyayya yadda baka zaɓan wanda zuciyar ka zata aminta dashi. Haka shima family baka zaɓa, kawai faɗowa kake yi. Dayawa da sunada zaɓi bazasu haɗa dangi da wanda suka fito daga gareshi ba.

Wayan duniya ta kira na Mahfooz amma taji wayansa baya shiga, ita har mamaki tayi koba komai zai kunna yaji muryan Rumasa'u. Shikam yana fita ya siya sabon layi a hanya yayi registration. Wajen biyun dare saita yanke shawara taje kitchen domin ta haɗa smoothie, yunwa da ƙishin ruwa duka suna damunta. Ji takeyi kamar cikinta zai haɗe da bayanta. A falo taga Rumasa'u kwace akan 3 seater tana waya. Ita kuma AC ɗin ɗakinta ne ya tsaya ta fito shan iska. Dr Abdallah yace zatayi aure bazai gyara yanzu ba. Tambaɗarɗen waya takeyi da Salima cikin nishaɗi. Tun sanda Salima ta taimaka mata da DNA ta soma neman Rumasa'u gadan gadan babu wani sauran jin kunya. Kuma itama Rumasa'u tana bata haɗin kai. Ko kuɗin data tambaya Mahfooz daya bata kaɗan Salima ta cika mata. Saidai har yanzu Salima bata san zatayi aure ba, ko minti biyar kafin shigan Naseera falon saida Salima ta gargaɗe Rumasa'u akan kishin ta da komai. Rumasa'u tana jira a ɗaura aure ne domin ta rabu da ita lokacin bakin alkalami ya bushe.

Gwiwan Naseera yayi mugun sanyi dataji irin kalaman da Rumasa'u ke faɗi, da farko tasha da Mahfooz ne angonta amma taji cewa da mace take maganar. Da sanɗa ta koma cikin ɗakinta abincin da bata ci ba kenan, sanin wannan shima yana cikin abubuwa dubun da suka hanata barci. Tausayin Mahfooz ta sake ji. Garin ɗaukar fansa zai faɗa zaben tumun dare.

Har ga Allah ita ta kasa ganin laifin sa, koko dama dai haka soyayya yake tun asali, idan kana san mutum koda naman jikinka zai rinƙa yankowa yana soyawa bazaka ji haushi ba. Ko bayan tayi sallah asuba ta sake kiransa a waya amma bai shiga ba. Tanaso ta gaya mashi cewa tana ɗauke da cikin yaronsu. Kamar yadda ta tayashi san Zanira, haka take kokarin ta tayashi san Rumasa'u. Shi nata ne duk da ya watsar da ita, they'll always be a team. Yasa bataso ya samu matsala cikin auren sa, tana so duk wani alheri dake cikin aure ya kasance ya samu. Amma kuma banan gizo ke saƙa ba. Rumasa'u bazata bashi wannan ba, alamu dayawa yana nunawa. Ta rasa gane meya gani yake mata rawar kai. Saita tuna cewa Rumasa'u tanada diri mai kyau kuma duk wani ɗa namiji dole ta burge shi.

Gidan a bushe kamar maƙabarta, mutanen Kwarbai na Zaria kowa sai bada uzuri yakeyi. Abin mamaki wai Dr Abdallah guda yana aurar da ƴarsa amma anki zuwa. Su kuma bawai sunsan kan Labarin bane, tunda baije yana shela akan HIV ba. Kuma ya gargaɗe Rumasa'u idan ta faɗi hayanta a gidansa ya ƙare. Mutane ne idan sukaji saboda wasu dalilai bada Naseera za'a ɗaura da sabuwar ƴarsa sai kawai su fasa zuwa. Cikin ruwan sanyi Allah yake saka ma Naseera.

DIYAR DR ABDALLAH Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu