Twelve - Mugun Mafarki

1.2K 184 15
                                    


Koda Faash ya koma gida baiga motar Mahfooz ba, bai kawo komai ransa ba, shi a nasa tunanin kila ya tsaya wani wajen ne musamman wajen yan mata, tunda yanada su dayawa har saiya ture.

Da safe da zaije tada Mahfooz domin suje asuba shine ya lura da rashin sa cikin ɗakin. Gadonsa a shirye yake kamar ba'a kwanta ba. Anan dai ya duba bayi domin ya tabbatar da rashin Mahfooz.

Har makara ya kusan yi yana dube dube cikin gidan. Da yaje waje haka bai sake ganin motar Mahfooz ba. Anan ne yasha jinin jikinsa. Masjid ɗin yana kusa da gidansu, da sauri yaje domin har anyi sujjud na raka'an farko. Haka yayi sallah fargaba duk ransa. Tunda Mahfooz ya dawo gidan da zama bai taɓa zuwa wani wajen ba bai masa bayani ba.

Bayan ya kira wayan shi yaji a kashe, lokacin Sada da mutanen sa sun ɗauki wayan da motar baki ɗaya. Koda basu ga su Naseera ba zasu rage zafi da wannan tunda yanada tsada.

Faash gidan iyayen shi yaje domin ya sanar dasu cewa baiga Mahfooz ba, tunda har coach ya kira aka ce baya Abuja. Balle ma ga kayansa na kwallo cikin ɗaki. Gadan gadan aka soma neman inda Mahfooz yake amma babu labarin sa.

Shima Dr Abdallah ya kwana da baƙin cikin ɓacewar Naseera, Hajia Binti bata iya barci ba. Kwana tayi kan sallaya tana sallah tana kuka. Neman tsari take taya Naseera dashi a duk inda take.

Dr Abdallah yaje asibiti yana kallon dalilin dayasa bata shiga motar ta ba. Anan yaga taya ya sace daga dukkan alamu yin mata akayi. Tabbas yasan cewa ana nemanta da sharri, hankalin sa ya kwanta amma ba sosai ba. Yanzu kawai zai ajiye wayarsa a gefe ne domin idan sun kira sai ayi cinikin yadda za'a amshe ta.

Sanda Dr Chinedu yazo yaji zancen hankalin sa ya tashi. Saboda babu ARV ɗinta ba ƙaramin hatsari bane a tareda ita. Gashi shi kaɗai yasan da zancen, baiso kuma ya faɗa ma Dr Abdallah hankalin sa yayi mugun tashi. Saidai abinda ya sani koma menene ya kamata ubanta ya sani.

Lokacin Dr Abdallah yana wajen gate yana magana da yan sanda, anzo ana duba ta ina aka tafi da Naseera. Sannan ga kamfanin masu saka CCTV suna gefe an kira su. Suma zasu saka kowa ya hutu dan tsautsayin gaba.

Dr Chinedu yana gefe yana jira ya gama, bayan yan sandan sun tafi sai DR Abdallah ya juwo ya kalle shi.

"Lafiya dai Dr?"

Murmushi Dr Chinedu yayi sai yayi gyaran Murya, "Dama sanda bakada lafiya akwai wani yar matsala ne akan Naseera,"

Girgiza kai cikin takaici Dr Abdallah yayi saboda jiya Binti ke faɗa mashi, "Abu babu daɗin ji wallahi," saiya nuna hanyar asibiti alamar su shiga ciki, sunyi taku wajen goma sannan ya soma magana, "Wallahi sun cuce ne, jiya Hajia take faɗa min,"

Haɗiye miyau Dr Chinedu yayi, yanaso ya gaya masa ba wannan maganar ba. "Yi hakuri Dr amma bashi nake nufi ba, wannan sirri ne wanda daga ni sai Naseera muka sani,"

Anan Dr Abdallah yabar tafiya ya juya ya kalle shi, ganin tsoro yayi cikin ƙwayar idansa, anan shima jikinsa yayi mugun sanyi. Cikin ƙaramin murya Dr Abdallah yayi magana.

"Menene kuma?"

Numfasawa Dr Chinedu yayi, "Dr banso ɓoye maka ba. Naseera kamar yata ce. Yadda zan kare martaban Ada haka zan mata. Naso saika warke sai na gaya maka,"

"Karka damu... Menene?"

"Naseera tested positive..." sai yayi shiru.

Rufe ido Dr Abdallah yayi na wasu dakikai saiya buɗe, dukda ba'a karasa zancen ba yasan menene ake nufi. Naseera tanada cuta mai karya garkuwan jiki. Anan hankalinsa ya kuma tashi.

"Shine nake so nace maka Dr duk me suke nema ka basu domin she needs her ARV Koda yaushe," Dr Chinedu yace.

Dr Abdallah bai ce komai ba, wucewa yayi ya tafi office ɗinsa. Ya mance rabon daya shiga. Duk yayi kura da yanan gizo tunda babu wanda ke amfani dashi.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now