Five - Annoba

1.2K 169 13
                                    

La haula get a friend like Zainab B Idris, Oum Eemad and Ahlam. I like the way you think, yadda kike tafiyar da rayuwar ki abin kwatance ne. Alhamdulillahi for knowing you, Allah ya bar min ke har Aljanna. Sannan godiya ga dukkan ma zauna TASKAR AINAU DIMPLES, Allah ya ƙara haɗa mana kai ya kuma kauda fitina tsakanin mu. One Love❤️

***
Ɗakin Shiru baka jin komai sai na agogo wanda ke maƙale a bango yana aiki. Dr Chinedu yana kan kujerar sa ita kuma Naseera tana zaune akan inda baƙi ke zama.

Hankalinsa duk ya tattara ya mayar akan nata, ita kuma sai ta soma jin babu daɗi. Anan ta fara wasa da yatsunta. Ta ƙosa taji meyasa ya kirata domin ta tafi. Shi kam jikinsa yayi mugun sanyi. Ya rasa yaren da zaiyi amfani dashi domin ya gaya mata cewa rayuwarta zai canza daga yau.

A shekara ashirin da takwas da yake aikin asibiti, Wannan ne karo na farko daya ke bala'in shakkan gayama patient ciwon dayake damunsu. Shi ba musulmi bane, amma yana jin Naseera cikin ransa kamar ƴarsa. Kamar yadda zai kare martaban ƴarsa Ada, haka zaima Naseera. Dr Abdallah aminin sane.

Ajiyar zuciya ya sake yi saiya ƙaƙalo murmushi na dole, anan ya soma rubuce rubuce na bogi duk domin ya samo ma kansa kwarin gwiwa. Daga bisani yace, "Jéhovah" cikin ransa saiya fara magana.

"Kinsan akwai wanda suke IT yan microbiology koh?"

"Eh," ta amsa masa. Gabanta ne ya soma faɗi.

"Toh ɗaya daga ciki yana nan randa aka kawo ki, shi ne yayi conducting maki test ɗin,"

"Okay," ta sake amsawa a sanyaye.

"Uhmm... Ashe ba duka results ɗin ya miko mana ba," shafa gemun sa yayi saiya ɗaura hannayen sa a saman kansa. "Chineke!" ya sake faɗi tsoro fal idansa.

Murmushin karfin hali tayi, "Dr inada ciki koh?" tace a sanyaye.

"A'a Naseera. You have tested positive for HIV,"

"Innalillahi wa inna ilayhi raji'un! Innalillahi wa inna ilayhi raji'un!!" ta miƙe tsaye tana maimaitawa.

"Calm down Naseera, ba ciwon mutuwa bane. Akwai vaccine da zaki rinƙa sha wanda zai taimaka maki wajen yin rayuwa kamar kowane ɗan adam. HIV gareki amma ba Aids ba. Aids ne abin tsoro, kuma yanzu zamu fara treating ɗinki. Har aure zakiyi sannan kuma zaki haihu."

Bata jin abinda yake faɗi, tana ɗurkushe tana rabka kuka. Ji takeyi kamar Allah ya baranta da ita. Kowane wahalar duniya a kanta yake ƙarewa. Kamar ta ɗauki alhakin wasu mutanen Allah yana saka masu.

Ta fuskanci kaɓule a cikin ƙanƙanin lokacin fiye da yadda mutune ke fuskanta a duka rayuwar su. Wasu ma basa taɓa fuskantar wannan abu. A hankali ta soma magana hawaye yana malalo mata a idanu.

"Dr anya babu tsinuwa a tareda ni?" tace zuciyarta yana mata ɗaci. Duk ilahirin jikinta rawa yakeyi. A da chan tace mutuwa hutu ce a gareta. Sanda akayi mata fyaɗe tayi tunanin gwara mutuwa da wannan. Yanzu kuma ga wannan. Ta lura kullum bala'in dake aukuwan mata yafi na baya.

"Dr baka ganin cewa ance min je ki Naseera zaki gani. Kije gaki ga duniya zai koya maki darusan daya dace dake... Dr na kasa fahimtar dalilin da yasa ni kaɗai wannan abubuwa yake faruwa dashi," kuka ne kupce mata. Anan ta rinka rusawa wiwi babu kakkautawa. Jikin Dr Chinedu yayi mugun sanyi.

Bai san me zai ce mata ba domin taji dama dama. Yana ganin saboda ita Dr ce itama yaci ace tasan wannan ba ciwon mutuwa bane. Amma sai ya tuna mutane basu san wannan ba. Gaba daya zasu rinka kyamanta suna gudun ta idan suka sani.

"Naseera kiyi haƙuri, wannan shine abinda musulmai kuke cewa kaddara, watau fate ɗinki ne. Bazaki iya kauce masa ba. Murna zakiyi an sani da wuri za'a fara baki magani."

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now