Twenty - Mijin Tauraruwa

1.2K 183 23
                                    

Alhamdulillahi, yar uwa kuma ƙanwata FA'IZA ADAM BARWA ta samu ƙaruwa yau. Allah ya albarkace ta da samun yarinya kyakkyawa irin ta. Allah ya raya mata ita cikin addinin musulunci. Also, my other Musketeer LUBNA SUFYAN ta gama littafin ta Abdulqadir yau. Allah ya sanya alheri, ya bamu ikon amfani da darusan da ke ciki. You know I love you.... Blah blah blah abeg don't stress me.

A hargitse ta shiga gidan Hajia Salima. Ko sallama batayi ba ta faɗa, ba ita kaɗai ta gani cikin falon ba. Su biyu ne da wata aminiyarta zaune suna shan kayan marmari. Zuwa tayi ta riƙo ma Hajia Salima hannu tana haki, “Hajia dan Allah ki taimaka min, rayuwa na zai salwanta...”

"Ki bari zamuyi magana anjima, yanzu inada baƙuwa.” Hajia Salima tace fuska a tamke. Ita bata so yadda Rumasa'u ta shigo ba babu sallama. Saboda yanzu a ɓoye take harkan ta, gashi yadda Rumasa'u tayi dole a gane akwai wani alaƙa tsakanin su.

“Hajia na rantse duk me kika ce nayi zanyi maki, ki taimaka min naci wanna yaƙin.” tace tana kuka.

“Nace ki tafi zamuyi magana anjima," ta daka ma Rumasa'u tsawa.

“Amma kin yi asara Salima, har yau baki bar wannan mugun ɗabi'an ba. Haba kinada yara da jikoki ace kina wannan shiririta.” ƙawar Hajia Salima tace tareda zabga tsaki. Kallon gefen Kankana tayi inda ta kalle matar. Tafi Hajia Salima kyau da gogewa nesa ba kusa ba. Asalin yar gayu ce, wani daham ta maƙala a wuya na gwal ga kuma zabbai a yatsun ta. Sannan ga danƙareren Leshi a jikinta wanda yasha stones. Ɗinkin bou bou ke jikinta kuma ya amshe ta. Suna haɗa ido ta zabga ma Rumasa'u harara. Da sauri Rumasa'u ta sunkuyar da kanta ƙasa.

“Fauziyya kenan! Babu ruwan ki da harka ta. Kinzo gidana kar kiyi min girman kanki da kika saba.... Ehe!” saita yarfa hannunta a iska. Kana ta juya ta kalle Rumasa'u, “Ehen my dear, me kike cewa ne?"

Anan Rumasa'u ta zayyana mata abinda takeso ayi, a canza DNA ace da nata yayi matching. Tasani har cikin ranta Dr Abdallah shine mahaifinta amma gwara ta shirya koda maƙiya zasu ce ba daidai bane. Shafa mata fuska Hajia Salima tayi tana dariya, anan ta bata haƙurin tafiyan su. Tace abubuwa ne suka bullo amma nanda mako mai zuwa zasu dubai.

“Har yanzu Latisha bata dawo daga baby shower ɗin bane daga Maldives?" Rumasa'u ta tambaye ta. Dariya Hajia Salima ta ƙyalƙyale dashi har tana sarƙewa.

“Wai ce maku tayi Maldives ta tafi?” saita cigaba da dariya tana tafa hannayenta, “Latisha yar ruɗu. Karya takeyi babu inda taje. Uban wa zai kaita Turai? Shegiya mai warin ƙashi. Yar banza kwanaki taci ma wasu hajiyoyi kuɗi sai da tayi kwanan cell...”sai ta sake bushewa da dariya.

“Wai dama yar talaka ce? Ni fah ce min tayi Mike Adenuga abokin Babanta ne, kuma rabin kamfanin Glo nata ne,” Rumasa'u tace cikin mamaki. Harɗe fuska Hajia Salima tayi tana hararar Rumasa'u. Banda jahilci a ina zakaga yaran Mike Adenuga, ita haushi ma taji kwanaki Latisha ta ara motan ta duk ta bar mata wari cikin sa.

Wayan Hajia Fauziyya ya soma ruri, cikin taƙama da ƙasaita ta ɗauka. Kana ganin yadda ta harɗe gira kasan ita ba abokiyar yinka bane. Samsun S10 ne ta fito dashi, “Son, ina jinka!” tace tanayi tana ƙarƙaɗa ƙafa. Anan Rumasa'u ta sake baki tayita kallonta. Matar ta burgeta, chas chas abinta. Sai Fauziyya ta tsaida wayan da takeyi ta kalle Rumasa'u.

“Ke juyar da fuskan ki, kuma kike sake kallo na saina ci bura ubanki. Ni ba yar harkan ku bane. Da aure na kuma har jikoki gareni. Na rantse na sake kama ki kina kallona, koni ko ke saboda sai an zubda jini...”

“Haba Fauziyya! Me tayi maki kike cin mata fuska?”

“Yo banda iskanci shegiya kamar ƙanzo, ta wani kafa min ido. Ubanki zan maki... Nace ubanki zan maki???”

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now