Three - Ummata

1.4K 187 18
                                    

Abdallah Specialist aka kai Naseera, nan aka wuce da ita emergency ward. Uncle Sadiq baisan an kwantar da Dr Abdallah ba.

Shi ƙanin Dr ne kuma yana PhD a Spain. Yau ya dawo saboda yabar matarsa da cikin yaronsu na biyu. Ya fita ya siya abu ne saiya kaɗe Naseera.

Bai kawo komai ransa ba ya kira Number ɗin Dr Abdallah, shi kuma a lokacin yana sallah bai dauka ba. Anan ya kira wayan Hajia Binti wanda take gida. Ta fito daga bayi kenan tana shimfiɗa sallaya sai wayarta ya soma ruri. Harda bazata ɗauka ba saboda lokacin sallah ne, sai wani zuciyar yace ta dauka tunda bata fara ba.

Data ga sunar Sadiq nan take ta sake fuska tana murmushi. Sallama tayi mashi shima saiya amsa. Anan yake mata bayanin tazo asibiti da Dr saboda ga abinda ya faru. Nan take ta zura hijabinta ta nufa ɗaki domin ta ɗauko ma Naseera kayan da zata saka saita nufa asibitin. Tunani kala kala kawai takeyi.

Likitocin sun duba Naseera sannan sun dauki samples a jikinta wanda zai taimaka ayi arresting wanda sukayi laifin. Sannan suka umurceta akan tayi wanka tareda magani.

Koda ta shiga bayi ta kunna famfo zama tayi akan seat ta buɗe sabon babin kuka. Ta kasa gasgata abinda ya faru da ita. Daga haduwar ta da yan daba, sai kuma Mahfooz. Eh Mahfooz yanzu ta sake tuna abinda yayi.

Tabbas ta sheda wasu babu alheri a sanin su, da ace bata taɓa ganin sa yafi mata akan wai yasan ta ya kuma san inda ta fito amma yayi ƙememe. Mamakin irin halinsa takeyi. Ba ƙaramin mugu azzalumi bane na bugun jarida.

Anan tayi kuka kashi kashi, na farko ga abinda yake wakana na cewa ba DR Abdallah bane mahaifinta. Na biyu ta ina zata ɗaura rayuwarta daga nan. Wa'annan mutanen sun cuce ta.

"Naseera kina bayin ne?” Umma ta tambayeta. Shima kukan Naseera ta sake fashewa dashi. A yanzu lallai ta gane ma'anar maganar da tayi da Babanta ɗazu akan bama mutane uzuri. Yanzu ta fahimci ƙila zai iya yiwuwa mugaye suka ma Umma fyade har ta ɗauki cikinta.

Tasan Ummanta kuma tasan halinta, tasan cewa tanada tsoron Allah. Fasikanci ba abu bane wanda zata aikata. Nan take duk wani makami data ɗauka akan Hajia Binti ta sauke. Tasauyinta takeyi matuƙa. Abinda yayi ma Naseera daɗi shine tasan cycle ɗinta kuma yau yana cikin ranakun da bazata iya ɗaukar ciki ba. Balle kuma anyi flushing mata system ɗinta.

Koda ta fito da Hajia Binti ta fara haɗa ido da, kwalla fal idanta. Tana tausaya ma yarta da sabon abinda zata shiga. Flash backs zai rinka damunta duk sanda ta runsta ido. Taimaka mata tayi domin ta saka kaya sai suka zauna su biyu shiru. Babu wanda yace komai.

Uncle Sadiq ne ya dawo tareda wani abokin sa, ASP Musa. Anan aka soma tambayar ta abubuwan daya faru. Nan ta faɗa masu komai harta abinda Mahfooz yayi. Bata dai nuna ta san shi a ido ba. Cewa tayi wani ya gani amma bai hana ba.

Umma ta tsine ma Mahfooz sosai, mamaki takeyi ace wai mutum bai da ɗigon imani a zuciyar sa. Tausaya ma iyayen sa takeyi saboda sunyi asarar haihuwa.

Shi kuma gida ya koma baije chemist ɗinba. Tanata faɗo mashi a rai yarda take hawaye tana kiran sunan shi. Abin ya so ya ɗan bashi tausayi amma yayita kawar da tunanin.

"She deserves it," wani zuciyar ta ayyana mashi. "All is fair in love and war," ya sake tunawa. Duk laifin tane ya kasa taimaka mata. Yana rage wani duhun dake cikin ransa. Yana rama abinda aka yi mashi yana yaro koda basu bane. Shifa baya cira ran cewa Naseera batada alaka da makiyan sa.

Bazai illanta ta da kansa ba, amma idan yaga tana ƙone wa kuma akwai kofin ruwa gefen sa, toh tabbas zai shanye ne.

Hawa kan gadonsa yayi yanabin shafukan kwallo, sai a lokacin ya tuna Ruma Sa'u. Anan ya koma explore yasan bazata rasa yawo ba. Nan yaga wani page na fresh ajebutters sun yi posting ɗinta. Cikin ikon Allah kuwa sunyi tagging ɗinta.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now