Thirty - Sun Shuka Sun Girbe

1.4K 247 47
                                    

Zabura da ihu Fauziyya tayita yi kamar wanda ta haukace, amma lafiyar ta lau. Jifa ta samo yi da duk abinda ta gani. Haka taje wajen hular Alhaji Sani tayi fatali dashi. Sosai suka firgita suna zare ido cikin ɗakin kafin ta illanta su. Wanda tafi tsorata itace Jamila, haka tayita baya baya kada Fauziyya ta damƙeta. Ana cikin haka ne sai akayi sallama. Muryan da kowanne daga cikin su ne ya sani sarai cikin dodon kunnen sa.

Hannunsa riƙe yake da travelling bag ɗin Fendi, sai tabarau siriri baƙi a saman idansa. Rigar mai layi layi blue ne ya saka, sai kuma wando baƙi. Kafansa sanye yake da takalmin Michael Jordan fari tas babu kala ko datti.

“Lafiya na ganku charko charko haka?” yace masu.

Da sauri ta ƙarasa wajen dayake ta soma mashi magana tana kuka, “Wallahi Al-amin karka yarda da abinda suke cewa, zasu raba mu ne, na rantse maka da Allah ni ce asalin mahaifiyar ka”

Ajiye jakarsa yayi a ƙasa yana kokarin fahimtar abinda Fauziyya take faɗi, kwata kwata batayi ma'ana ba a batun ta. Anan ya soma bin yan ɗakin da kallo wanda sukayi charko charko cikin tsoro.

“Wai lafiya?” ya sake faɗi.

“Lafiya lau Al-amin, shigo ciki.” Alhaji Sani ya ce. Saiya kalle Fauziyya wanda take haki tana zare idanu.

“Wallahi koki natsu koki sha mamaki, kin mance na sanki sarai ne halan. Kuma nasan abinda zaki iya aikatawa da wanda bazaki aikata ba.”

Share hawayen ta takeyi da hannu ɗaya, saita riƙe ma Al-amin hannu da ɗayan hannun. Tare suka ƙarasa falon suka zauna. Mai aikin Fauziyya lokacin tazo tana share inda aka fasa table ɗin. Har lokacin Jamila bata bar fargaba ba, ta bala'in tsorata da Fauziyya. Al-amin ne yayi dogon ajiyar zuciya, sannan ya kalle baban shi.

“Abba, wai me yake faruwa ne?”

“Ina so ka natsu ka saurare ni Al-amin, nasan kai yaro ne mai hankali da kaifin basira. Toh inaso kayi amfani da wannan hankalin akan abinda zan gaya maka a gaba. Kalle Mahaifiyarka,” saiya nuna mashi Hajia Fauziyya. Anan Al-amin ya kalleta saiya sake kallon Alhaji Sani.

“Kaga wannan matar dake zaune kana kallo a matsayin mahaifiyarka, yanzu labari yazo mana wai ba ita bace ta haife ka...”

“Wallahi ƙarya ne... Na rantse da gemun mahaifina.” tace tana kuka.

Gaba ɗaya ɗakin mamakin ta sukeyi, basu taɓa jin cewa ana rantsuwa da gemu ba sai ranar, tana abu kamar yar tasha ko yar bori.

"Zo ki fita,” Alhaji Sani yace mata yana zare idanu.

Ita kuma saita ruga bayan Aisha ta ɓoye tana kuka, bataso ta fita kuma bata so ta tsaya ta bari su gama maganar su. Jamila ne ta sake magana wanda ya gigita Fauziyya.

“Ai nasan inda Rumasa'u take aure, idan kunaso sai na kaiku, abu kuma na zamani ga DNA. Zai nuna idan ƙarya nakeyi,” Jamila ta sake maimaitawa.

Fauziyya ne ta kasa haƙuri da abinda Jamila tayi, mamaki takeyi yadda ta ɗauki alwashin saita tarwatsa mata rayuwar aurenta. Rayuwar data daɗe tana ginawa. Gashi cikin mintuna kaɗan ta tarwatsa komai. Nufanta tayi tareda damƙar mata kwalar riganta. Saita soma kilarta tako ina.

“Saina halaka ki! Kafin ki kashe min aure saina kashe ki, ” tayita nanatawa tana kuka.

Da kyar aka kwace Jamila, Aisha ne ta wuce da ita ɗakin masu aiki ta rufe. Saboda muddin sukayi arba da Fauziyya na lahira saiya fita jin daɗi.

Alhaji Sani ya yanke shawara zaije Kaduna da kansa ranar domin yaga Rumasa'u tareda iyayenta. Shima Al-amin yace zashi domin a yi komai a gaban sa. Sau da dama ya saba samun shakku akan inda ya fito. Musamman yadda kamannin sa ya fita daban dana sauran yaran, gashi kuma genotype ɗinsa AA ne na sauran gidan AS. Wannan abubuwan sun daɗe suna cinmasa tuwo a ƙwarya amma babu wanda ya bashi amsar tambayar sa sai yau.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now