Sixteen - Bazan Barki Ba

1.1K 170 22
                                    


Mahfooz ya samu sabon sana'a, kamar yadda ake kiwan dabbobi haka yake kiwan Naseera. Duk wani motsi wanda zatayi yana kan idansa. Tana sanya shi nishaɗi fiye da komai cikin faɗin duniyar. Musamman idan tana dariya, dariyar ta yafi so a komai nata. Akwai yanda sautin sa ke ratsa cikin zuciyar sa, sannan fuskanta yana ƙawatuwa kamar fure mai bala'in kyau, gashi yana sheƙi kamar lu'u lu'u.

Ita dai Naseera doguwa ce amma ba sosai ba, da wuyan ta da kanta yayi kashi uku ana kofa. Fara ce tar mai dara daran idanu. Idanta irin kalar madara ne sannan ƙwayar idanta kuma ruwan zuma ne kamar na wasu maguna. Batada hanci mai tsine, nata yaje daidai da fuskanta. Bakinta yaɗan ciko yana yanayi da Jaruman bollywood priyanka chopra.

Tanada zara zara yatsu sirara wanda ya ƙawata ta sosai tareda yin daidai da siririn jikinta. Saidai a haka duk da sirantakar tanada diri mai kyau. Wuyanta sambal ne kamar na barewa. Sai da batada tsawon gashi a kanta, amma kuma duk gajartan sa yanada laushi kuma ya nannade kamar yadda matan africa sukeda shi. Tafiyarta abin kallo ne saboda tana yinsa cikin ado da taƙama kamar ɗawisu balle kafafuwanta a miƙe yake abin kallo. Tanada cikar ido da kwarjini, uwa uba idan tayi magana, muryanta zaƙinsa kamar an busa sarewa, kokuma zakayi tunanin susa ake mata a kunne yana ratsaka.

Ta ɗuka tana juye ruwa daga tulu, sai taji duk ta tsargu kamar ana kallonta. Wayancewa tayi saita waiga domin ta tabbatar da abinda take tsammani. Tsaye ta gansa a bakin ɗakin Ardo yana kallonta, babu abinda ya dame shi da cewa nan kauye ne ba'a nuna soyayya a fili.

Matarsa ce kuma babu wanda zai hanashi kallonta, yana tsaye ya saka hannu ɗaya cikin aljihun wandonsa, sai ƙafa ɗaya ya lanƙwasa ya jingina a jikin bangon. Ɗayan hannunsa yana wajen ƙeyarsa ne yana sosawa. Da suka haɗa ido saiya sakar mata wani lallausar murmushi sannan haƙorar sa farare tas ya bayyana. Gabanta ya soma duka uku uku. Ta lura yayi nisa kuma baya jin kira. Amma ko da yanka naman jikinta za'a rinka yi bazata taɓa amsa batun sa ba.

Ta ina ma zata amsa? Tanada mugun ciwo fah? Shima yanada nashi matsalar bataso ta saka shi wani. Balle kuma bayan duk abinda Fauziyya tayi bazata taɓa yarda wani cutarwa ya je mashi ba ta sanadin dangin su. Wahalar daya sha ya isa haka. Tana cikin tunani sai taga mutum dab da ita. A firgice ta matsa baya tana kallon sa. Saita soma girgiza masa kai alamar ya bari, baiko kula ta ba. Hannusa yasa ya matsar da nata daga tulun.

"Meye amfanin zan iya taimaka maki banyi ba?" yace chan ƙasa. Banda ita, sauran mutane gidan da suke kallon su basu ji ba. Duk saita tsargu, anan ta bar mashi komai ta wuce nasu ɗakin da sauri. Tana isa saita kama gwiwar ta kamar zatayi ruku'u tana haki, yanda takeyi kamar tayi gudun famfalaƙi amma tsabaragen tashin hankali ke dawainiya da ita.

Da gaske yanada niyyar sauya mata rayuwarta, da gaske abinda daya faɗa mata zai aiwatar. Amma meyasa yakeda kafiya da naci ne? Ai ba ita bane kaɗai mace kuma rannan ta ganshi tare da wata, meye dalilin sa na zuwa wajenta yanzu. Saura kwana kaɗan su tafi menene amfanin takura mata?

Bayan ya gama juye ruwan saiya bi sahunta, ganin yadda ta birkice yake mamaki. Baiyi tsammanin tsanar datayi masa yakai haka ba. Zuwa wajenta ya soma ita kuma saita soma tafiya baya baya tana girgiza masa ido. Miyan bakinta ya bushe rau kamar ƙashi. Saida ta kai bango babu inda zata, waige waige tayi domin ta samu wajen gudu. Anan ya tsaida tafiyar sa, saiya ajiye idansa a cikin nata. Itace ta soma magana cikin takaici.

"Dan Allah ka rabu dani, bakasan me kake faɗi ba. Na tabbata trauma ke damunka, saboda mun shigo garin nan kana ganin abinda baya nan..."

"Kina nufin banda hankali ne?" ya katse ta. Sai ya soma dariyar takaici yana safa da marwa. Ita dai bata bar inda take tsaye ba. Yatsa ya nuna mata saiya soma magana, "Watau bazan iya cewa ina sanki ba sai ina hauka? Meke damun ki ne wai? Meyasa kike guduna haka? Menene aibu na ? Ban cika namiji bane koko ni ɗin ne kika mugun tsana?" kwafa yayi saiya daura hannunsa a saman ƙirjinsa.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now