Fourteen - Rarrafen Carpet

1K 189 23
                                    

Assalamu Alaikum Dimplicious Empire, naga ance yanzu na daina posting kullum. Anyway, afuwan ba laifi na bane. Lockdown ya tsagaita kuma na koma aiki. Yasa nace kuzo muyi shawara, typing ƙaramin shafi kullum kokuma dogo kamar yadda nake yi idan na kammala. Diyar Dr Abdallah nawa ne, kuma naku ne. So, let's discuss. #FullyDimplated

Rumasa'u tayi kiran duniya wayan Mahfooz amma bai shiga ba, ta rasa gane dalilin dayasa ya ƙaurace mata akan maganar da bai kama kara ya karya ba. Saidai abinda ta sani bazata karaya ba, tunda ta gansa kuma ta yaba dashi babu mai raba su. Tayi mashi saƙon text yafi sau hamsin. Ta Instagram kuma yafi a ɗirga. Harda hotunan datake ɗauka take tura masa. Idan yaga kyanta zai dubeta ya yafe mata.

Yanzu ta riga ta ƙure haƙurin Rahina, ko magana basu cika yiba sosai. Kawai ana zaune ne gida ɗaya. Dama dama Rahina tana ɗan mata magana, ita kuwa haɗe girar sama dana ƙasa takeyi. Tunda ta roƙe Rahina rancen dubu hamsin ta hanata shine ta ƙullace ta. Kuma ta ɗauki alwashin saita ɗanɗana mata koɗan ta.

Gantalin ta yanzu babu kama hannun yaro, kullum tana titi gidan abinci kala kala tareda yan group ɗin one love ana hutawa. Wata rana kuma tana dawowa da abinci irin su kaza da cupcakes, haka kamshi zai bi ɗaki tana ci tana waƙa ta hana Rahina. Gashi waƙar da takeyi mai ban takaici ne, "Wal bani wal baka, wal hanani wal ƙememe,"

Rahina dariya takeyi cikin ranta sabida in dai akan abinci ne tafi ƙarfi, amma kuma idan tazo da nata su Shawarma tana bama Rumasa'u kuma ko kunya bata ji ta karɓe ta cinye.

Cikin gantalin ta da shige shige ta haɗu da Latisha. Ita ta kasance asalin ajebo rarrafen carpet. Followers ɗinta a Instagram basu fi 250 ba wanda ita Rumasa'u tana kusan dubu tamanin. Latisha kuɗi gareta kaca kaca kuma bata san hayaniya. Wani ɗan group ɗinsu Rumasa'u na One Love zaije kai mata wayanta daya tayata gyarawa.

A marsandi tazo wajen Murtala square inda suke shaƙatawa domin ta karɓa. 2017 E300 4matic ne ɓaka gashi da tint. Motan ya tuna ma Rumasa'u da Mahfooz saboda kalarsa yake hawa. Balle dataga Latisha ta fito daga ciki, sai lokacin Rumasa'u ta tuna ya kamata ta iya tuƙi koba komai zata soma fakan idon su Rahina Bulala tana fita da motar su.

Rumasa'u bata bar wajen ba saida tace a bata number ɗin Latisha. Ta whatsapp tayi mata magana tareda gabatar da kanta cewa sun haɗu ɗazu. Sannan tace ita yar Adamu Fiya Fiya ne Chairman ɗin Kaduna North local government. Sai Kuma take cewa basu gaisa ba ɗazu da kyau ba kamar taga tana sauri, dariya Latisha tayi saita bata haƙuri.

“Dan Allah kuyi haƙuri banida wulakanci wallahi kawai raina a ɓace ne, ba'a wanke min motana ba gashi kuma zan karɓe wayan shine na hau motar kayan miya nazo,” tace cikin shagwaba kamar zatayi kuka. Ita Rumasa'u bata gane abinda take nufi ba, “Daga Murtala square kinje cefane ne halan?”

Latisha ajiyar zuciya tayi, “Ina nufin motar da ake siyo mana kayan miyan shine na tuƙa da kuka ganni ɗazu,” ta sake faɗa cikin takaici. Jikin Rumasa'u ne yayi mugun yin sanyi. Motan tana kimanta shi da miliyan ashirin koda bai kai ba kaɗan ne babu. Anan ta tabbatar da cewa duniyar nan ba daidai bane. Wasu suna kogin arziki su kuma suna ta tsiya. Idan wannan ne motan cefane, tana so taga asalin motar Latisha. Suna cikin wayan sai Rahina ta shiga ɗakin, tana sauraron tafsir ɗin Sheikh Jafar Adam ne na Wacece mijinta yafi. A fusace Rumasa'u ta kalleta tareda daka mata tsawa.

“Dalla malama rage muryan nan bakiga waya nake yi ba,” ta faɗi tana hararar ta. Mamaki ya soma dawainiya da Rahina, lallai Rumasa'u ta soma wuce gona da iri. Ita kuma Rumasa'u bataso abinda zai takura ma Latisha ne. Saboda yanzu ita zata zama aminiyar ta.

Rahina bata rage ba kuma bata amsa taba, Rumasa'u ne ta tashi tana tsaki, “Latisha dear, hold on bari naje garden domin muyi waya da kyau,"

Sunyi kusan awa ɗaya suna hira kala kala, Rumasa'u ta gama karanta Latisha tsab. Rarrafen carpet ce na bugun jarida. Bama a Nigeria suka tashi ba, shekarar su uku da dawowa. Kuma batada ma ƙawaye sosai saboda batada hayaniya. Rumasa'u sai lokacin ta lura yaran masu kuɗi akwai su da basaja. Sune rarrafen ciminti suka damu da yawan followers, sukam cin kuɗin iyayen su suke yi hankali kwance. Saidai ita Rumasa'u batada wani abin tinkaho face followers ɗinta. Sune uwa da ubanta. Suke siyan mata katin subscription, sannan kullum tana cikin karya wayanta ya lalace, haka za'a bata 10k ko 20k tana kashewa a hankali.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now