“Innalillahi wa inna ilayhi raji'un,” yayita nanatawa cikin firgici. Tallabo mata kai yayi ya riƙe. Baisan me zaiyi ba saboda tashin hankali.“Sake min yarinya, mugu kawai azzalumi. Duk laifin ka ne take wannan halin ai.” Hajia Binti tace tana kuka. Babu arziki ya sake Naseera ya koma baya. Barira tazo da sauri taga meya faru, bata tsaya ɓata lokaci ba ta wuce sama domin kiran Dr Abdallah. Shi kuma ya rufe ido yana hutawa.
“Baba, Naseera ta faɗo daga bene jini yana kwararo mata,” ta faɗa da karfin gaske tsaye a bakin ƙofa. Shima haka ya tashi cikin sauri saiya bita. Lokacin Kankana tana ɗakin Naseera bata fita ba tanata mata dube dube. Sai taga trinket box ɗinta cikin durowa. Yan kunne ne na gwal da sarka kala hudu. Saita ɗauke guda biyu set, da babba da kuma ƙaramin cikin. Ta lura Naseera bazai amfane taba. Balle bata fiye ganinta da yan kunne ba. Sannan taga tana tareda baƙin cikin Qwaro batada kwanciyar hankali da zata rinka kwalliya. Shine ta ɗauka gwal ɗin koba komai zata iya siyarwa tayi wani abin da kuɗin.
“Subhanallah ! Ya akayi haka?” Dr Abdallah ya ce sanda ya isa wajen. Babu wanda ya amsa shi a wajen. Saiya kalle Mahfooz wanda ke rakuɓe a gefe yana kallo.
“Zoka tayani ɗaga kanta.”
Saiya kalle Barira, “Ɗauko min jakana,”
Mahfooz ya soma zuwa wajen kenan, sai Hajia ta sake dakatar dashi. “Bana ce karka sake matsowa kusa yarinya ta ba?” tace a hasalce.
“Binti this is not the time, ki bari muba yarmu agaji.” saiya gyaɗa ma Mahfooz kai alamar ya ƙaraso babu damuwa.
Haka Dr Abdallah ya bada taimako na gaggawa tareda saka mata Oxygen domin ta shaƙa numfashi. Sai ya ɗauke Naseera zai nufa hanyar mota da ita. Tafiya yayi taku uku sai bayansa ya riƙe, balle kuma ga ciwo dayake fama dashi. Da sauri Mahfooz yaje domin ya taimaka mashi. Har da Dr Abdallah ya hana sai kuma ya yarda. Yanzu lafiyar ƴarsa yake so ya ceto kafin komai. A lokacin Rumasa'u ta fito daga ɗakin Naseera, saidai ba haka taso sosai ba. Taga wani kimono ɗinta mai bala'in kyau wanda taso ɗauka, sanin halin idan Barira ta kamata bazata ji da kyau ba yasa ta bari. Yanzu zata fake idonsu ne sai ta shiga da jakarta domin ta ɓoye.
“My husband meye haka?” tace ganin Naseera a jikinsa. Babu wanda ya kulata. Hajia Binta tana kokarin gyara zaman hijabinta. Da sauri Rumasa'u taje tasha gabanshi tareda ware hannu tayi blocking hanya.
“Meye haka zaka ɗauketa? Ai nice matarka ta sunnan. Meyasa bazaka ɗauke niba saboda cin amana.... Dan ubanki sauko tunda ba gadon gidan ku bane shegiya yar matsiyata.” saita kai hannu zata finciko Naseera.
Barira ne ta sharara mata mari tareda janyeta, wanda daga Dr, Hajia da Mahfooz basu ce komai ba suka nufa hanyar parking. Sai suka shiga mota suka wuce Abdallah clinic. Duka sosai Barira tayi ma Rumasa'u gashi babu mai ceton ta. Daga nanne ta yaga mata kaya saiga dan kunnen Naseera ya fito daga rigar mamanta. Laga laga tayi mata sosai dukan tashi ki sha gishiri, sannan ta koreta titi tareda watsa mata kayanta. Kwata kwata ta mance yarinyar Dr Abdallah ne kuma zata iya rasa aikinta akan abinda tayi. Kawai dai Rumasa'u ta daɗe tana shigan mata hanci kuma yau ta fyatota la'ada waje.
Emergency ward suka wuce da Naseera, cikin ikon Allah cikin jikin Naseera bai ɓare ba. Kawai dai ta shiga coma ne kuma likitoci sunce ba abun tashin hankali bane. Idan kwakwalwarta ya huta zata iya farkawa bada dadewa ba. Hajia Binti tana jin haka saita sake fashewa da kuka. Inji ne ke taimakawa yarta domin ta rayu, kuma duk ba laifin kowa bane face Mahfooz dake gefen wajen.
“Mallam ka tafi ka bamu waje. You've cursed enough pain in my family,” tace mashi tareda nuna mashi hanyar ƙofa. Yaso yayi magana ta dakatar dashi.
“Wannan ne rana ta karshe da zaka sake ganinta, nayi maka alkawari.”
“Umma kiyi haƙuri ki yafe min,” yace da kyar saiya fita daga ɗakin. Zuciyar sa tana mashi ɗaci. Bayaso ace a karo na biyu Naseera ta shiga wani hali saboda shi. Amma kuma babu abinda zai iya mata yanzu, tunda dai shiba likita bane. Addu'a yayi mata na fatan alheri cikin ransa.

DU LIEST GERADE
DIYAR DR ABDALLAH
Mystery / ThrillerZuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba. Yanayin da zai zama useless baida amfani. Sai yanzu ya lura da dalilin dayasa ya kasa barci. Ba komai bane illa wannan sabon s...