Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah

1.1K 181 37
                                    


Tunda Naseera ta fahimci cewa Mahfooz ba canzawa zaiyi ba, saita saurara masa. Shima zaman a haka yafi mashi daɗi sosai. Ya riga ya birne rayuwarsa na baya kuma baya so ya ɗauko wannan babin. Zaune suke cikin jindadi da walwala, idan suna tare cikin ɗaki banda hira kala kala basa komai. Musamman ko a aikin Naseera kokuma akan nasa. Yana bala'in alfahari da ita yadda take malaman asibiti. Hirar asibiti sosai suke yi tareda yanda take ceto rayuwar mutane. Har yake ce mata da tana nan sanda umman sa keda rai, da ita zatayi mata operation sanda aka haife shi. Kuma bazata mutu ba, duk wannan abu bazai faru ba. Daga nan kuma sai ransa ya ɓaci ya kanne fuska.
Ita kuma mamakin yanda yana kwallo kuma yana aikin Engeering ɗinsa takeyi, nan ya gaya mata yanzu manya manyan hanyar da gwamnati sukayi shiya zana da kuma wasu gadoji.
A kwana a tashi babu wuya wajen Allah, har rana ya zagayo za'a ci kasuwa. Kuma yaune ranar da akayi sunar yaron Charo. Koda mutane suka shiga cikin gida tareda ganin su Mahfooz, basu kawo komai cikin ransu ba. Saboda dama Charo tanada wasu yan uwa a brini, kuma ansha sune suka zo sunar yaronta. A iyaka cin kwanakin nan Mahfooz ya nuna mata soyayya fiye da yadda take tsammani. Ya mutunta fiye da yadda take gani ana ma wasu. Idan suna tare zata gaya masa gameda ciwon ta, taran numfashinta yakeyi da sauri. Ya kalle ta cikin idanu babu wasa kuma a nasa. Ya sake jaddada mata cewa koma menene bazai rabu da ita ba, gwara tabar sirrinta cikin ranta. Idan tana ganin zai rabu da ita akan shi ne toh zai bata mamaki. Muddin bazai cutar dashi ba, toh bayaso yaji. Yaji kuma ya gani zai zauna da ita. Dogon nazari tayi, kuma kamar yadda yace ne idan bazai cutar dashi ba, baida amfanin ya san koma menene. Haka suka soma gina rayuwa mai tsabta irin na ma'aurata. Kallon Mahfooz takeyi a kaikace ko zai nuna alama na cuta amma bata gani ba. Koda yake ba'a ganewa a fuska, ta ɗauki alwashin idan sun koma zatayi mashi gwaji domin ta tabbatar da abinda likitoci sukayi bayani.
Shikam gode ma ranar da su Sada suka ɗauketa yakeyi, saboda da basu zo wannan kauye ba bazasu taɓa kasancewa tare ba. Sannan yayita gode ma Ardo daya nace mashi akan ya aure muradin zuciyar sa. Dama ance every disappointment is a blessing, duk ya mugun abun daya faru dakai idan aka duba ta wani fannin akwai alheri cikinsa.
Tabbas Naseera itace tauraruwan zuciyar sa, yana samun natsuwa sosai idan yana tareda ita. Yanzu ya daina firgici idan yana barci, sau daya yayi tun jituwar su sai ta riƙe shi tana kwantar mashi da hankali, tareda jaddada masa tsoro ba komai bane face abinda mutum ya ƙera cikin ransa.
Bayan asuba ranar da zasu tafi, da safe tana kwance tana ƙara barci. Saiga Mahfooz yaje wajen jakarta domin ya tayata haɗa komai. Dan shi baya so su kai azahar a garin. Zumbur ta miƙe da sauri ta fizge jakan kamar an tsikareta da mashi. Idanuwanta sunyi dara dara kamar sabbin tocila. Anan ta soma ajiyar zuciya tareda ajiye jakar gefenta. Kallonta yakeyi yana mamakin yadda ta canza farad ɗaya, kuma menene ke cikin jakar data ke masa mugun ɓuya? Ita kuma tana tsoron kada yaga AVR ɗinta, yayi mata alkawarin bazai rabu da ita ba duk runtsi amma bata so ya sani ta haka. Ta fiso itace ta fito ɓaro ɓaro ta gaya mashi.
Barin ɗakin yayi yaje wajen su Ardo, anan yake sanar dashi cewa zasu raka su gida dashi da Bamanga. Musa yaso zuwa amma aka ce ya tsaya ya taimaka ma matarsa. Anan akayi ta hada hada ana haɗa masu kayan da zasu tafi dashi. Naseera sunsha kuka da Charo kamar idansu zai fita, kuma taje wajen Fesindo tayi mata bankwana tareda neman yafiya wajen ta. Mahfooz bai mata maganar tsarguwan datayi ba. Shi ke ta sakar mata murmushi, ya lura hankalin ta baya jikinta. A cikin motar hannun sa yana maƙale da nata gam. Kamar wani zai zo ya kwace mashi ita.

“I will never leave you,”

yake furtawa idan idansu ya haɗu. Babu karya Mahfooz yana ƙara mata kwarin gwiwa. Hankalinta yaƙi kwanciya gabanta sai faɗuwa yakeyi. Ta rasa dalilin dayasa ta shiga cikin yanayin. Banda azkar cikin ranta batayin komai. Ji takeyi kamar wani mugun abu zai faru da ita.
Bayan azahar suka isa Kaduna daga garin Niger, kai tsaye gidansu Naseera aka wuce. Sai da aka nufa hanyar layin Mahfooz ya fara tsorata. Bai taɓa tunanin zaiyi mashi wahalar gayama iyayenta ya aure ta kai tsaye, ba tareda sanin su ba. Gashi ko sau ɗaya baiyi practicing irin jawabin da zai yi ba, kokuma yadda zai tsaya, zama ko gaida su. Sai a lokacin ya tuna cewa bai taɓa zuwa bikin kirki ba balle yasan yanda ake yi gaban surukai. Tsakanin shi da taro sai wajen ɗaurin aure a masallaci.
Ranar Nurse Jamila tazo duba Hajia Binta, jinin ta ya hau sosai wanda yasa saida aka kwantar da ita ana ƙara mata ruwa. Duk ta rame bata iya cin abincin kirki. Hankalin Dr Abdallah yayi mugun tashi, ya rasa Naseera gashi yanzu kuma Hajia rai yana hannun Allah. Dambun shinkafa wanda yasha zogale da nama Nurse Jamila ta kawo. Sai tayi kunun zaƙi da kuma ginger drink. Sannan ga ferfesun kayan ciki tareda yanka su kankana da abarba. Liyafa sosai tayi cikin cooler ta kai masu. Ita da yarinyar ta Zubaida suka je. A turakar Hajia Binti suka ganta kwance tana numfashi sama sama, duk ta galabaita ta zama abin tausayi. Babu haufi Anty Jamila ta tausaya mata,
Jibe yanda take wahala akan yarinyar da bana nata ba. Da kanta ta canza ma Hajia Binti ledar ruwa. Sai Zubaida ta zuba masu abinci, tareda tayasu gyaran ɗaki.
Taxi Ardo yayi masu chata su huɗu, sun isa layinsu Naseera suna kofar gidansu. Koda suka fito daga motar, wasu samari su uku suke tafiya a layin. Da sauri ɗayan ya nufesu yana murmushi.

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now