Thirty-Two - Déjà-vu

2K 234 90
                                    

Mahfooz zama yayi yana tagumi, tuna abubuwan daya faru dashi yake tun sanda iyayen sa suka rasu. Da kuma zaman dayayi a gidan Fauziyya har kuma barinsa. Sannan kuma da yanda yayita zaman kansa kafin su Faisal suka dauke shi. Tabbas yaga rayuwa kala kala kuma kullum fatan ƙarewan wahalar sa yakeyi. Haƙiƙa mutanen da bai masu komai ba sunci zarafin sa. Sai kuma wata zuciya ta raya masa, 'kaima kayi ma Naseera'

Sam ya daina tunata, komai nata ya riga ya ɓoye a chan ƙasan zuciyar sa. Shifa har yanzu baiga abinda yayi mata ba. Na farko bashi bane yace tayi kama da Fauziyya, sannan bashi bane yace ta fita har mutane suka yi mata fyade. Ai kowa zai iya bin wannan hanya a lokacin, yasa yasan ba laifin sa bane. Amma duk da haka ya cire girman kai ya bata haƙuri. Maimakon ta haƙura ta barsa shine ta nema illanta shi. Cikin ransa shi yana ganin wautanta saboda meye zata ki faɗa masa cewa tanada kanjamau dan cin zali. Haka yayita tunane tunane akanta tareda kwashe mata albarka sabida ya tsallake rijiya da ƙafar baya. Yana cikin haka sai wani notification daga email ɗinsa yazo masa.

Kungiyar kwallon ƙafa ne a chan Ontario dake ƙasar Canada suke buƙatar sa akan yazo da gaggawa domin ya buga masu. Shi a duniya yana bala'in san Arsenal, amma ko wannan ɗin babu laifi. Tunani ya soma akan ya zaiyi da auren Rumasa'u dake kansa, sannan ga Zubaida da zai aura nanda sati biyu. Yasan tabbas idan yagaya ma Daddy cewa ga abinda ya faru za'a ƙarya ta shi ace saboda baya san auren ne yana neman guduwa. Abubuwa dayawa yayi tunani akansu daga karshen saiya yanke shawara ya naɗe kayansa ya gudu.

Balle gudu ba yau ya saba ba, ya gudu daga gidan Alhaji Sani ya dawo Kaduna. Yanzu kuma zai gudu daga Kaduna ya koma Canada. Saidai yanzu ba kamar da bane. Abu kaɗan za'a iya tracking ɗin mutum. Yafi so yaje chan ayi training da sauran abubuwan fitness kafin season ɗin kwallo ya gabato gadan gadan. A lokacin sai ya dawo hutun sati ɗaya yayi masu bayanin, kuma ma yayi signing contract ɗinsa ba damar breaking promises, suba ƴan Nigeria bane masu saɓa alkawari. Yanzu sai a ƙulle mutum. Idan kace zakayi abu dole kayi.

Haka yayi replying email ɗin yace ya yarda, coach ɗin wanda yana tareda wayansa a lokacin yayi mugun jin daɗi. Dama tuntuni yake kwakwan Mahfooz bayan ya buga ma Naija a Fifa. Nan ya sake amsa Mahfooz yace ya shirya kayansa, visa ɗinsa zai zama ready nan da kwana biyu. Murna mara mitsaltuwa ya mamaye Mahfooz. Anan yayi maza yayi uninstalling su whatsapp, twitter, Instagram da Crowwe ɗinsa. Yasa baisan abinda Kankana tayi ba a Instagram. Koda ya isa gida bai ganta a falo ba. Ya dai ji motsin ta cikin ɗakin ta. Baibi ta kanta ba yanata haɗa travelling bag ɗinsa. Komai nasa ya tattara. Sauran kuma ya ninke ya saka cikin akwatuna.

Da asuba wanda yasan dama Kankana tana barci kuma ba jinsa zatayi ba, ya fito da jakarsa ya ajiye a corridor. A Masjid ya haɗu da Baban Anees makwabcinsa ne, nan ya bashi mukullin motansa akan ya tayashi ajiyewa gidansu idan gari ya waye. Baban Anees bai kawo komai cikin ransa ba ya karɓa, sai kuma Mahfooz ya ajiye ma Rumasa'u takarda.

'Na tafi' ya rubuta kacal sai kuma chèque ɗin dubu ɗari. Abuja ya wuce ta jirgin ƙasa zuciyar sa yana cikin zulumi akan sabon rayuwar da zai ɗaura. Ita Rumasa'u koda da tashi wajen goma sha ɗaya. Batayi asuba ba kuma batada alamar yi. Instagram ta buɗe inda taga tanata trending. Abin ya ɗan taɓata, bata ji daɗi ba yanda ake tsine mata anata kiranta matsiyaciya. Saidai kuma data tuna cewa kuɗi zata samu sai zuciyar ta yayi sanyi. Wajen sha biyu ta fito falo, taga takarda akan tebur amma batabi takai ba. Kitchen ta shiga ta soya kwai da dankalin hausa. A falo ta dawo tana ci tanata fito ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya. Tik tok ta shiga tanata kallace kallace. Sai kawai idanta yakai kan tebur, nan ta jawo saita karanta. Taɓe bakinta.

"Kafi ruwa gudu," ta faɗa a fili sai kuma taga chèque. Nan ta soma washe baki sosai. Abaya ta saka nan take ta wuce first bank dake kawo inda yake amfani dashi. Anan aka bata kuɗin. Ta fito sai taga mutane masu surkule. Sai yasa allura a hanci sai ya fito ta baki. Anan kowa ya washe baki yana kallo. Itama ta tsaya wajen. Ta shafe wajen minti talatin sai kallo takeyi tana babbaka dariya. Abubuwa kala kala sukeyi harda yanka harshen su, laso wuta. Bayan ƙafarta yayi soma zafi. Juyawa zatayi ta tafi sai taga abinda ke hannunta. Ashe ba handbag ɗinta bane kamar yadda take tunani.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 06, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DIYAR DR ABDALLAH Where stories live. Discover now