LAIFINA NE 3

176 19 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       ❤️ *LAIFINA NE*❤️
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Shout out to all my Fans...Daga jiya zuwa yau naga sakonni na fatan Alheri....Ina Godiya Mara adadi..I so much love you all_

*FREE PAGE 3️⃣*

Maza biyoni tace" Jikinshi na rawa yabi bayan mahaifiyarshi har falonta, Dan suna matukar tsoran Mahaifiyarsu Dan mace ce me zafin Gaske, Kallonshi tayi tace Ali yaushe ka dawo da har ka kasa Zuwa kacemun kadawo? What's wrong with you Dan kaga mahaifinka bayanan ko? Kasa kasa yafarayi da murya yace Mum it's not like that, banda Lafiya ne Yasa na dawo, Motarma A waje na ajiye!

Kallonshi ta farayi tace I'm ur mother kar ka kuskura kafaramun karya, budurwa kayi da zata Fara chaza ma brain KO? Da Sauri ya dag'o kanshi ya kalle ta yace noo Mummy!

Wani dogon Nunfashi taja Tace be careful, Tashi ka tafi

    Jiyai kamar an watsa mai ruwan Sanyi, shi tsoranshi ma daya kar fauzee ta kirashi agaban mummy, Ahankali ya tashi ya nufa bakin gate, Yace me gadi ya budemai gate ya shugo da motarshi kirar Vibe, Yai parking

Bayan yayi parking ne, ya wuce Dakinshi, da yake akwai toilet a ciki, Shiga yayi toilet din yayi yai wanka sannan ya daura Alwala yai sallah yai nafiloli Sannan yaje part din mummy zaici abinci amma duk abunda yakeyi mum na kallanshi duk beda kuzari, kuma tasan akwai abunda ke damunshi, ko cin abincin da yakeyi tana ankare dashi Dan beci Wani sosai ba, Dan Ali mutun ne me kazar kazar Amma ranar he's quite, yanan yin Abu very slowly hatta kannanshi seda Suka Lura da hakan

Mamanshi kuwa aranta tace ba soyayya ba zakaci ubanka tai banza dashi taci gaba da kallon TV!!

Wajen 9 yabar Falon yai musu Sallama, Mum tace don't forget you should take paracetamol, Yace insha Allah mum, Tace Shifakallah, yace thanks, kannanshima sukaimai Allah Kara sauqi yace Ameen
   Yana fita mum tabishi da kallo tace uhm Yaro Yaro ne LOL

  Daki direct Ya wuce, da shigarshi yakai hannunshi kan phone dinshi, he checked ko akwai missed call din Fauzee but unfortunately he found none! Kirjinshine ya Fara beating yace" kardai ace tayi fushi da yawa!! Nan take zuciyarshi tace mai "Laifina ne" meyasa na mareta!

Beyi kasa a gwiwa ba ya Kira number ta, Ringing biyu Aka dauka, Saita muryanshi yayi kamar Karamin yaro yace" My Girl Ina Kika shigane, I'm here missing you?

Ummie ne ta gyara murya tace Yaya Haidar Ba Anty Fauzee bace, Nice

"Ohh ohhh yace Tana Ina? Tace" ta shiga toilet tace" idan ta fito Ki ce Mata na Kira, she should call be back please, Ummie tace OK, Sannan ta kashe waya

Suna gama baya ummie ta shiga binciken inbox, Taga texts din da haidar ya turowa fauzeeya ta gani, nan ta Shiga karantawa, Rik'e baki tayi tace Allah ya shirye Anty fauxee what did she mean? KO Dan reply ai tamai, Karar bude toilet taji kafin Ta ajiye wayar Fauzee ta fito a toilet kamar tayi kuka ma Dan her eyes looks redish

Da sauri ta karaso tace" meye na tabamun waya, Ina naki? Ummie ne tace Ya haidar ne ya Kira, shine na dauka, yace ki kirashi

Wani bakin ciki taji, tace how many times zanyi warning dinki akan kidena picking din wayana when ever kikaga ankira? Ummie stop it banaso please, saboda I warned you times without number

Ummie Smiling tayi tace" aunty Fauxee u don't have anything da zaki Mun hiding, what's happening Between you and Ya haidar?

Fauzee tadan tsuke fuska tace, wannan tsakaninmune ba ruwanki, karki sake tambayana, Ummie tace Allah baki hakuri my aunty saida safe, ta tashi ta wuce dakinta, aranta tace koma meye senaji tunda baki da abokiyar shawara sama Dani

Ummie Shiga daki tai tai kwanciyarta, sannan ta dakko wayarta ta shiga WhatsApp, Group din yan school dinsu ta Fara dubawa, tai Sallama kunyi baccine? Kutashi I have gist for you, kan kace meye Maza da mata duk sunfito saboda Ummie yarinyace me barkwanci, nan Suka Fara hira....

    Bangaren Fauxee kuwa bayan ummie ta fita a dakin Kashe wayarta tayi, shi kuma Haidar Yanata Kira a kashe, gashi dare yayi ballantana yaje gidansu, dukda koyaje ba lalle bane ta fito, Daren dai kwata kwata bemai dadi ba Dan ji yakeyi I'm missing something

   Fauxee kuwa tinani ta Shiga, tace dole nasaida mota ta Dan bazan iya tafiya da ita ba ma, beside ma ni yanzu hakama bansan Wani gari zamu dosa ba, And duk rintsi duk wuya bazan bari hatta ummie tasan Dalilin barinmu garin nan nan, Haidar sena koyama Hankali, saikayi Dana sanin mari na, I hate you....wato koda na aureka haka zaka mun? Tinani ta shiga yi, tana cewa aranta wato duka haka maza suke.....

Bangaren Haidar kuwa kasa bacci yayi Dan Abu biyune ya hadun Mai, jiyai yana matukar son Fauzee amma idan ya tino da Banzan da tacemai  se ranshi ya Kara soya, A tinaninshi Ai duk Wanda akacewa Banza Ana nufin beda amfani ne, yar  karamar tsaki yaja, Yace bari na hakura da beb dinnan kawai, wata zuciya kuwa tace zaka Iya? Oh ohh ohhh ya furta kamar Wani karamin Yaro, yana tambayar kanshi meyasama ya sama ranshi zai aureta ta! Hasbunallahu wa ni'eemal wakeel yake ta nanatawa har bacci yai awon gaba dashi

Washe Gari Saturday
     As usual dama idan weekend ne Fauxee bata tashi sai kusan 9AM yau ma haka ta tashi dukda kasancewar batajin dadi amma tinani be hanata bacci ba, Saboda kwata kwata ta cire Haidar a ranta, tunda ya iya daga hannunshi ya mare ta..

After sunyi having break fast tai wanka tacewa mamansu Zataje ta saida Motarta, Her mum was shocked, saboda her face ya nuna akwai damuwa,
Dakyar dai ta kwantar mata da hankali tace idan sunje Chan din zatasai Wata motar, Mamansu tace To Bakomai, Ta kalle Ummie tace Ku Fara shiri kunsan dai gobene tafiyarmu ni bari naje na dawo, ta batar musu da tinani tace Mammah daganan Zan buya companyn mu, Sukace a dawo Lafiya, Allah ya tsare

   Mamansune ta kalle ummie tace Badai wata matsalar bane KO? Ummie with her full confidence ta fara magana tace Mammah wani matsala ci gabane ma, Kinsan Fauxeeya da kokari, mace ce amma ko wani namijin albarka, Mudai fatanmu kibimu da addua Allah ya Kara sa mana Albarka, Tace hakane Allah yai muku Albarka Ummie tace Ameen

   Fauxeeya kuwa data fita Tada motarta tayi, Sanye dake da Riga da window, ta dakko after dress ta saka, Ita yarinyace amma Sam batason saka babban gyale bare hijab. shigarta takeyi son ranta, Tana tafe tana nazarin wani Abu,

  Seda tazo kofar gidansu Haidar dayake hanyar wucewarsune, ta kalle gidansu tace, Ga gidansu banzan nan, Mugu azzalumi, taci gaba da driving dinta, bata tsaya ko inaba se wajen Aminiyarta Farida

Tana shiga Farida sukai 4 eyes, Kwalla ihu tayi farida tai dan aminai ne na gaske, Tace myfrnd myfrnd yau kece da safen nan nan

   Fauxee tace eh nice ko korana za'ai zanzo incinye maku abinci KO?

Farida tace laaa nidai banceba, Fauxee tace to naji tana kokarin cire after dress dinta, tace inasu mummy? Farida tace Mum suna gidan biki, kanwar mum ke aurar da yarinya Wanda ta dawo daga Dubai karatu

Nima shugowata kenan zanwa daddy abinci kinsan yanada ciwon sugar bakowani abinci yake Ciba

Fauxeey tace OK, Gyara zama tayi tace nazo Ne muyi magana nasan ke kadai zaki rikemun sirrina...Farida ta zauna tace tabbas hakane before mufara magana ina zuwa

Kitchen ta nufa ta zubo mata nunun gyada me dadi da fanke ta kawo Mata, tace kici kafin mufara magana Tace OK

Nan ta dauka kofi tafarashan kunun gyada fari tas ga gar d'in gyadar ya fito sosai, naga tana santi nace Bari mujirata ta gama shaaaaaaaa LOL

hope kuna jin dadin novel din.....more comment more typing

URS...UMMIEY XEEY

VOTE.
FOLLOW
SHARE ✍🏼

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now