LAIFINA NE 37

76 11 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

_Wannan page din sadaukarwane ga duk wani masoyina...Ummiey Xeey na sonku irin sosai dinnan❤️🖤🤍_

*PAGE 3️⃣7️⃣*

   Haidar firfigit ya tashi yana nazarin mafarkin da yayi na Fauxeey Janyo laptop dinshi yayi ya shiga Wani file inda ya boye Pics din Fauxeey, Shiga yayi yana kallonsu daya bayan daya, Faduwar gabanshine ya tsananta, Kallonta Yakeyi kamar yai magana ta amsa, shaukin sontane ya kamashi, hannu ya saka ya shafa fuskar ta ta jikin laptop din Tino Da maganganun mutane yayi na Yanzu ka rasa wanda zakai soyayya da ita se mara Asali? Kallon pics din yaci gaba dayi, gaba daya ya fita hayyacinsa dan Wani radadi yaji zuciyarshi na meshi, Harga Zuciyarshi yanason Fauxeey sedai da kamar wuya, Hajiyarshi ta amince ya aureta, Hawaye masu Zafi suka zubomai yana Tinanine meyasa Fauxeey tamai haka, meyasa ta gujeshi a lokacin da yake tsananin sonta, Dan ba karamin azabtuwa yai ba lokacin da ta rabu dashi,

Wata zuciyar tace you're the course of everything,

Tafiyar Hajara yaji yai sauri ya rufe laptop din amma idonshi sun yi ja dan he's badly missing her, ita kadai yake sha'awar kasancewa da ita for the rest of his life sedai kash....

Shugowa hajara tai yanda ta kalleshi tasan
Baya cikin walwala, Kusa dashi taje ta zauna, Gashi tayi kwalliya ba laifi tayi kyau. Turaran Fauxeey da take sawa shi kokacin da sukaje kasuwa yasai mata, dan Haka tana zama kamshin turaran ya buga hancinsa, Gani yake kamar fauxeey, Kallonta yai gaba daya yaga Fuskarta ta koma Na fauxeeya

Wani abu yakeji a kwalwalwarsa yamai yawo, Dan Sam beson Kamshin turare sosai dan tadamai feelings yakeyi, bare yaji Favorite perfume din Abun kaunarshi fauxeeya

Kallon Hajara yai yace please ki fita, Kasa kasa da murya tai tace haba Ya Haidar Kwata kwata saura kwana nawane ka dena ganin fuskata, Ni naga akwai damuwa a tare dakai sai yasa nazo, dan Tun dazu baka fito falo ba

Yanda tai magana seta bashi tausayi, Dan shi a duniyar nan yana bala'in jin tausayin mace, balle when it comes to Love, he respect love sai yasa duk wanda yaganshi cikin soyayya yake tausaya mai dan yanzu yasan ba shakka Hajara  na sonshi shima yana dan Liking dinta sedai bazai taba aurenta bane..

Shuru yai na wasu mintina, Kamshin turarenta na bugan hancinsa, Gashi tazo kusa dashi ta zauna,

Hajara batasan tana son Haidar da tausayinshi ba se a lokacin dan tunda Hajara ta fahimce Auren dole akeso aimai Taji gaba daya Tana tausayinshi dan duk wanda ya rasa masoyi a zamanin se yayi kuka wallahi

Kiran Sallar Ishsha'i sukaji, Dama Allah Allah Haidar yake Akira sallah ta fitan mai a daki dan bazai iya juran ganinta ba, Dan masha Allah ta cika ta ina komai ma zai iya faruwa

KO kallonta baiyiba Yace muje mui sallah tace" toh, fita sukai yana bin bayanta da kallo yana astagfirullah, Dan Hajara akwai Kugu

Ya haidar seka dawo aimana addu'a tace, inanan Inanan dawowa idan kadawo masallaci yai kamar bejiba yasa kanshi ya fice Masallaci....

****
    Bangaren Maman Fauxeey kuwa tunda Ummiey ta fada mata Cewar Fauxeey bazata dawoba tace Kai ina akwai wani abun, Ummiey ita kanta batasan meke faruwa ba amma taji a jikinta something is Wrong, sedai kawai ta kwantar wa mamansu da Hankali, Mamansu tace to bakomai, ina dai maku fatan Alheri a duk inda kuke, Allah ya tsareku ya kareku ameen, _Mothers please a dinga yawan ma yaya addu'a ba kara min tasiri yakeyi a garesu ba_

***
   Bangaren Fauxeey kuwa bayan ta idar da issha'i addua itama tai akan Allah ya tsareta, dan One leg a duniya one leg a lahira dan tana tsaka me wuya, fitarta gidan Akwai wahala, Gashi tanata Kiran number boyayyen masoyinta shuru, Tayi text yafi 20 shima shuru betafi ba

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now