LAIFINA NE 6

158 10 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       ❤️ *LAIFINA NE*❤️
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 6️⃣*

Fauxeey ne Zaune a gaban wannan matar da taje gidanta, Tace mata Dan Allah ita bakuwace ta bata wajen kwana, inda zataje ya mata nisa ne gobe zata wuce Chan, Matar nan maisuna Mairo Tace" to Yar nan bakomai, Ai da nakowane, Dakin Seemah mairo ta kaita tace ga masauki nan, Fauxeey tace nagode Mama, Wacece Seemah? Seemah Yar mairo ce budurwa da bazata wuce sa'an Fauxeey ba, Amma tafi fauxeey sanin kan duniya da kallo daya zakai mata kasan idonta a bude yake, Dan Kitson attach nema akanta ga fuskar nan yasha mai, Tayi fara Sol...Wannan kenan
    Fauxeey Kuwa kare mata kallo tayi, aranta tana zayyona abubuwa da dama, Suna zaune dai suna hira jefi Jefi, Mairon ta kawo masu abinci, Shinkafa ne da wake da Mai da yaji, Nan Fauxeey tai Mata godiya tace bakomai,

   Chan Kusan karfe 8:30 fauxeey ta dakko wayarta IPhone 11, ta Kira ummie kanwarta tace tabaiwa ummansu, Ummansu ta amsa bayan sungaisa tace kin Isa wajen kuwa tun dazu muke kiran wayarki a kashe, Fauxeey tace Mammah ba network ne Sai yasa baku sameni ba, Tace OK A kula dai, Allah yayi Albarka fauxeey tace Ameen!

    Bayan ta gama wayar ne, Seemah ta kalleta tace Baiwar Allah daga ina kika fito? Tace Daga gombe muke, Wasu aikine ya kawoni nan Sai yasa, Seemah tace OK, Amma kinyi aure? Fauxeey tace meyasa kike tambayan hakan ko kinga na miki kama da matan aurene? Seemah tace a'a just tambayane, Fauxeey tace A'a banyiba da saurana!

   Seemah tace very good, Kibari ki huta kisama Wanda zuciyarki yai miki, karki gaggawa dukda nasan komai lokacine,

Fauxeey gyara zama tayi dan antabo Mata inda yake mata Kaikayi, Dan taga alama Akwai magana abakin Seemah, Uhmm Fauxeey tace" amma meyasa kikace karnai gaggawa ai aure da dadi? Seemah nunfasa tayi tace" Tun Ina 20years akaimun aure kasancewar inada girman jiki, Aketawa mahaifiyata ta aurar dani, Banshiga school da wuriba kasancewar Halin rayuwa kinganmunan bamuda komai sedai rufan Asiri, Ina Ss2 Akaimu aure KO takarkar waec bandashi,  intakaice miki Nayi aure, wahalar yau daban na gobe da daban, Dangin Miji suka sani a gaba wai ban Iya komai ba, Karshe dai Sakina yayi! Yanxu Banda aure, So KO zanyi ba yanzuba
    Fauxeey jikintane ya Kara mutuwa, ta Kara tsinkewa da halin Maza, Wai duk maza haka sukene daga me wulakanta matarshi, se mai bata wahala da sauransu, Nidai nace Baduka aka taro aka zama dayaba, dukda kinda babban dalilin fadan hakan,

Fauxeey Ta matukar tausayawa Seemah, ga ba ishesshen karatu ba, Ga mijinta ya yayi Mata wannan Sakamako!! Seemah tace kinji atakaice kenan,

Fauxeey tace to Amma dukda kika fito da kin natsu, sorry bance baki da natsuwa ba amma they way I see you hmm, Seemah tace hakane, Zan Iya fada miki komai Dan Inajikinki tamkar Yar uwata, Kinsan Zauranci Itama jarabawace, Ba kowa ke Iya hakuraba indai ya fito dinnan se masu karfin imani, dan yanzu a zamanin nan mayuwace ace mace tai 20years bata sha'awar namijiba sedai in batada Lafiya, masu imanin cikinmune zakiga suna addua da azumi,

fauxeey tace OK nagane inda Kika dosa, kardai ace kina cikin masu aikata wannan mummunar Aikin!, Seemah riko hannunta tayi tace Kitayani da addua' Allah ya Kara shiryamu, ni kaina inasone indena Wallahi

Fauxeey ta nunfasa tace" karki damu inshaa Allah Zaki Dena, Amma akwai wasu mazan jahilai, basa tinanin insun sake mace wani hali zata Shiga? Kawai sun dauka kalmar da duk abunda namiji yayi adone a wajenshi? To Wallahi su sani inhar basu tuba na zasu hadu da fushin ubangiji, Allah dai yasa mugane gaskiya muyi aiki da ita Ameen

Seemah najin maganganun Fauxeey tabbas maganarta gaskiyace ba kuskure a cikinta, Fauxeey tace Allah ya Kara shiryamu, Seemah tace Amen

  Sannan Seemah tace amma daga ganinki you're nor from poor family Dan fatarki ma ta nuna, Murmushi Fauxeey tayi tace tabbas hakane amma rayuwar damukai har gwanda wani talakan Dan Sam bamusama kwanciyar hankalina, Sai yasa kikaga namiji sam baya gabana!! Seemah binta da kallo tayi, Fauxeey tai saurin batar Mata da tinani tace ammafa na kusan aure! Seemah tace" ayyoh koda naji, Amma zaki iya ban labarinki? Fauxeey tace mezai hana, Amma ba yanzuba kallon agogo tayi taga 11:00PM, tace dare yayi sedai gobe, Dan haka suka kashe Globe din Dakin sukai kwanciyarsu,

Fauxeey kuwa ba bacci taiba, aranta tace gobe dole daina chanza layi, Inba hakaba Abunda naiwa Haidar Seyai tracking Dina, Yagano inda nake, Wani murmushi tayi taja bargo ta rufe jikinta tai bacci

     Cikin baccintane taji Seemah na taba mata jiki! Firgigit ta mik'e ta wanka Mata fari? Tace dama ke Yar lesbian ce? Allah yakaimu gobe Sena fadawa mahaifiyarki, Kuka Seemah ta fara tace Dan Allah tayi hakuri, kifahimceni Wallahi ba haka bane? sakkowa a kasa Fauxeey tayi ta shinfida sallaya a kasa tai kwanciyarta, Daren dai batai bacciba, Dan Tinanin abubuwa da yawa takeyi, tana ganin rayuwa itadai, data tsalleke nan sai nan! Ahaka dai bacci ya kwasheta.
   Washe gari nayi ta tashi tai sallah, da yake ta haddace Azkar akanta ta zauna tayisu, seda haske ya Fara fitowa sannan ta tashi a sallayar, Ta Shiga ta gaida baba mairo sannan ta kira Ummie and her beloved Mum as usual addu'a tai Mata Sannan ta kashe wayar

Tunda ta tashi Ko A batacewa Seemah ba, Seemah ma haka Dan mugun kunyarta takeji, Wajen karfe 8 na safe, Fauxeey tace tana zuwa, Fita waje tayi taga Shago a bude na communication Tace tanason Sabon layi nan take aka bata Etisalat Akai mata rejister, ta kwashe duk numbers din da take bukata a tsohon layin ta saka a sabon Sim din
   Sannan ta biya wani shagon provision ta siyo masu sugar mudu, da babban gwangwanin peak milk da bornvita da cret din Kwai sannan ta dawo gidan hade da bread a leda
      Tana shiga dakin baba mairo ta ajiye, baba mairo kukan dadi ta Fara dan rabonsu da irin wannan harta manta Dan talauci ya musu yawa, Allah yai mana tsari da ita
      Nan ta sa mata Albarka, adaidai lokacin Seemah ta shugo, abun ya bala'in bata mamaki, se taji kunya sosai

****
  Bangaren haidar kuwa tun asuba ya tashi yai wanka kasancewar yau Monday da azumi a bakinsa, Da wuri ta tafi office, But inbanda faduwar gaba ba abun da yakeji.....

    Misalani 9:AM aka tattaro zaa shiga meeting...

Hmmmmm Muje zuwa

More comment please

Vote and share

UMMIEY XEEY😍

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now