LAIFINA NE 20

84 9 1
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

'''One of the most amazing feelings in the world is having someone fall in love with you who you thought you never had a chance with ☘️'''

*PAGE 2️⃣0️⃣*

Shigewa dakin tai cike da fargaba ta kwaso kayan wankin ta fito duk a tsorace
    Chan bayan gidan taje inda suke wanki ta zauna tai tagumi, anya zata iya aikin nan, tun baaje ko ina, ya fara kiranta, ita tsoranta daya Kar ya hada mata trap dan tasanshi Expert ne, motsin tafiyar mutun taji tai maza ta daga kayan sai taga sam basu da datti hasalima kamshin turare suke, tsumasu a ruwa tai tasa detergent ta wankesu tas, dasuka bushe ta kwasomai ta dawo mai dashi daki,

Tana zaune A yar karamar falon baki dan Hajiya bata yarda ta dinga shigan mata falon taba sedai in wani sako emergency, cellular dakin taji tai ringing dama hajiya tace duk sanda taji karar wayar dakin ta zo tanada bukatar ganinta, Dan haka ta tashi ta tafi ta tarda Usman Bobo yasa kanshi a cinyar mamansh, tana shafamai kai kamar karamin yaro, A zuciyarta tace tohh faa Jibeshi a wajen wani sangangan dashi
    Shiga tai ta tsugunna kanta a kasa tace" hajiya gani, tace yauwa Fauxeeya abincine Bobo keso na dinner yace Farfesun kaza yakeso da jallof din kuskus ina fatan kin iya?
 
Kanta na kasa tace" Na iya Hajiya,

"hajiya tace" to Komai da komai yana kitchen, fauxeey tace" tom hajjaju, tunda Fauxeey ta shugo dakin Bobo ke kallon ta, a zuciyarshi yace" like i knw this face, Dan kallon kurilla yake mata kamar yau yafara ganinta,

Tashi tai ta fita, Bobo yabi jikinta da kallo, Wani murmushi yayi, bayan tafitane ya kalle hajiyarshi yace First luv, wannan yar aikin tana mun kama da wata a school dinmu, amma wanchan akwai girman kai dan ba wanda ya isa ya tankwara ta, dan Big girl ce kuma tadanfi wannan kiba da haske,

Maman shi tace hakane kasan Allah ba yanda baya abunshi, Akwai masu kama da mutun da yawa a duniya, Bobo yace hakane amma kamannin wa ennan ya baci, Daga daga ina aka kawota?

Daga kauye tacemai, daganan bata sake magana ba,

Bobo yace" Allah yasa kam kama sukai dan idan naga yarinyar nan sena kusan kasheta,

Dago kanshi tai tace" lafiyarka kuwa? Bobo yace Mum subutar bakine, na tsana yarinyar ne, Tace better

"Fauxeey kaman tasani bata tafi ba tana labe taji abunda sukace, dafa kirjinta tai tace na shiga uku kardai fa ya ganeni, idan yagene nice Fauxeey sai yakusan kasheni dan gashinan ma ya furta, dan ba karamin kuntatamai nai a School ba, kuma nemana yake ruwa a jallo, Ya Allah ka tsareni tace daga sharrin Usman, Allah kasa ba nakawo kaina bane dan idan ya gane nice Sorry for me Sidif sidif tai ta shiga kitchen tace Dole na chanza takuna in ba hakaba na mutu,

Hajiya tace wai ma ya za'ai yar babban mutun tazo tazo gidanku aiki? Tunda nasan School dinku yaran manyane kawai, Son ka dena tinanin ko ma itace Wannan Sam ba ita bace, Yace Ok Dear Mum, kiss takai goshinshi, Ya rike mata hannu yace I love you 1st love..

    Wayarshi ne yai Ringing yana dubawa yaga abokiyar sheqe ayanshine, an rubuta MY LIFE yai sauri yai rejecting, dakinshi ya wuce ya sama waje ya zauna yai calling back dinta, shagwaba ta faramai irin na matan nan yan bariki tana kashe muryan da duk wani lafiyayyan mutun sai yaji wani iri a jikinshi, tace baby maye faru yau through out baka kiraniba, ko kasama wata ne

     Kasa kasa yai da murya alamun mara gaskiya yanata leke leken window yace" baby ba haka bane an kawo mana yar aikine kuma babba ce kinsan Zata dinga sa ido sosai shine nakeso nafara mata Warning akan duk me tagani indai tai magana sena saba mata, so nake na saita kwakwalwarta yanda bazata dinga shiga harkataba
    "Murmushi tayi tace sai yasa nake sonka, Yace nima haka

Yace Yeah, I'm here missing you, ta chanza wani murya kamar tana bacci tace nafika missing, Dan ni ganinan rungume da pillow inaji kamar kaine kusa dani, Wow my baby yace, Zan shugo zuwa anjuma naganki dan bazan iya bacci ba without seeing your beautiful face,

Tace" wow m Happy, Allah yakaimu, Mezan ajiyema? Yace abun dadi dukansu suka dariya..kiss yai mata sannan ya kashe wayar, ya kwanta a kan gadonshi, kallon celin ya farayi

Tinanin fauxeey ya fara anya ba ita bace" wata zuciyar tacemai ya za'ai big girl haka tazo gidanku aiki, kadena tinanin wannan ma ba ita bace at all...Okk yace ya cigaba da aikin gabanshi, Duk abunda yakeyi minti uku hudu Sai yayi tinanin fauxeeya

*****
    Chan gidan su Haidar kuwa mahaifinshi ya dawo daga Dubai, Kiran haidar yayi ya cimai mutunci sosai, Yace kuma tabbas aure zasumai, shi kanshi mahaifinshi yasan hukuncin da suka yankewa haidar sam bedace ba,

Amma dole sui kamar sunayi
     "Haidar yace to shikkenan na amince amma kafin auren zan koma karatu kasar waje

Mahaifiyarshi tace" Sam bata yardaba ya bari idan ya aura matar sai su tafi tare da ita, Haidar kallon iyayanshi yayi aranshi yace" gaskiya baku kyautamun ba, Yace" to shikkenan ya tashi ya shiga daki
    Ranshi a bace ya kira amininshi Ahmad ya sanar dashi duk yanda sukai, Ahmad yace" ka kwantar da hankalinka I'll do my possible best inshaa Allah bazaka aura wacce baka soba

Haidar yace" How bayan goben nan Hajiya zataje kauye ta dakkomun duk wacce ta keso

Ahmad ya busa iska a ba bakinshi yace kabar komai a hannuna

Haidar yace" Ok

    Alhaji Abdallah dabai mahaifin Aliyou Haidar ya kalle matarshi Hajiya lubabatu yace" Madam Kiyi hakuri da maganar Auren Haidar da wata kibarshi ya zaba zabinshi, Kinga bamu mai adalci ba a yan kwanakin nan da nai nadawl naga duk ya chanza, Please in ma tsoro kke bashi ya isa haka, da ni inasha wasane har ina kara tsoratar dashi, seda naga da gaske kke ashe

Kallonshi tai tace" Alhaji nariga nagama magana, kuma ba zancen Wasa nakeyiba

Dan hajiya lubabatu irin matan nan ne wanda sukafi karfin mazajensu, shi kuma Alhaji Abdullahi yaba ta dai hakuri, Yace" to Allah yakyau ta amma ina mai tabbatar miki zaki hada abunda daga baya zaki dana sani, kuma muddin kikaimai auren dole nima dole inyi wani abu......

Tashi yayi yabar mata dakin, yabarta da tinani shin mezaiyi?

Tsaki tai tace, gobe goben nan zan tafi kauye

Yace Allah yakaimu Tace Ameen a zuciyarta, Ta dakko newspaper dinshi yaci gaba da karatunshi

Bobo kuwa, yunwa yakeji sosai, se safa da marwa yakeyi a harabar kitchen, Yanaso yaiwa mata magana amma kwarjininta ya hanashi yi mata magana, Da zaran ya ganta sai yaji sam beda kuzari a jikinshi

Hakanan ya dawo dakinshi ya zauna Yana tinanin Fauxeey, Ga bebs dinshi sai kiranshi sukeyi a waya, Wanka ya shiga still ba abinci fauxeey bata gamaba

Kallon Agogon dakin yayi yaga karfe 6:00PM

Zira jallabiya yayi Ya nufa part din mamanshi......

.........Muje ZUWA

Comment Dinku yana mun Kadan Gaskiya

And Yan Wattpad kuma inbakwa voting zan dena posting gaba daya

Urs Ummiey Xeey

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now