LAIFINA NE 30

102 11 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 3️⃣0️⃣*

Fauxeey firgigit ta tashi jikinta sharkaf kamar wanda aka watsama ruwa, Tana kwance, duk  kasala tama kasa tashi a gadon ko motsi bata iyayi dan wani azaban ciwon kai ke damunta tino mafarkin datai tayi tace Allah nagode maka da ba da gaske bane, jitai kamar an kara dasa mata son Haidar a zuciyarta,

Ahankali ta daga Hannunta ta dakko wayarta, shiga gallery tai ta fara kallon pics din Haidar, Gabantane taji yana mugun fadi, anya bawani abun bane zai faru dan yanda taji gabanta na fadi tasan ba lafiya Dan tanajin din idan abu xai faru takanji haka

Kodan ta kwana biyu bata duba pics dinshi bane taga yau ya kara mata kyau Da sauri ta kifa wayar dan Kirjinta bugu yake tayi tare da jin wani mugun sonta na shigarta

Addua take tayi
ji tai Son Haidar ya dawo mata sabuwa, jitai tanada bukatan ganinshi amma kuma da kamar wahala, Hawaye masu zafi suka zubo mata a fuskarta Dan yanxu tayi nadama bata da burin da ya wuce ta ganta da Haidar

     Minti minti take tina haidar ga faduwar gaba da takeji duk lokacin data tinashi

****
    Bangaren Aisha Igala kuwa Zaune suke da abokin munafurcinta Hashimu, Ta bata rai tace har yanzu banga result mekyau ba, Malamin nan yace Haidar zai dawo gareni amma har yanzu Shuru, Kodai aikinshi beye ne?

Hashimu yai tsuru tsuru kamar munafiki ko ince munafiki, tace ba magana nake ma ba ko baka ji bane? Sosa keya yafari dan munafurtar ta yai ya kaita wani wajen malamin karya ya koma daga baya suka raba kudin, Yace kinsan aikin se ansa patient bare kinga Mum dinshi a tsaye take itama

Kamar zatai kuka dan ba karamin kudi ta kashe ba kusan 150K tace To I'm patiently waiting, naga Ranar da zan mallakeshi dan i seriously love him

Kodai ta wajen mum dinshi zamuje? Muce a tusa mata sona yanda zata yarda na aura danta? Hashimu yace nooo kitsaya dai please tace toh

***
   Bangaren Haidar kuwa bayan yatafi kai kannanshi makaranta, Hajiya ta tisa Hajara a gaba akan ta fara nunamai soyayya duk inda yaje ta bishi, duk abun da yakeyi tadinga sa kanta a ciki

   Dan haka yana dawowa Hajara da kwalliyarta ta fito har tsakar gida tanamai oyoyo, Saura kiris ta tabashi, Wani hararata yai tare da daka mata wani tsawa, yana kaucewa yace idan ma kika karasao sai kin sani,

    Bataji abunda yace ba ita kam ta takai hannunta kan nashi, Da sauri ya dago kanshi yana kallon yanda ta rikemai hannu

Kasa magana ma yai dan takaici, Tunkuda ta gefe yayi yace wuce chan kibani waje, kazama kawai Ita kam sam bata damuba dan tana dan sonshi

Yana tafe tana Binshi a baya har Ya shiga Daki, yaga ta biyoshi

     Yana kokarin shiga part din mamanshi sai gata ta shugo, kallon Hajara tai tace jeki daki ina zuwa

Shugowa tai ta sama Gefen gadonshi  ta zauna ta kalleshi, tace har kundawo? Yace Eh

Tai shuru tana so tamai magana amma tana Tsoron taji amsar da zai fito bakinshi tasan tabbas bazai taba mata karya ba

   Lafiya Mum yace?

Tace ina lafiya tai kasa kasa da murya wai da gaskene babanka zai kara aure?

Wani sanyi yaji a ranshi, Yace Eh, nan da nan ta shiga damuwa
Daki ta wuce tai tanini kodai taje wajen malamai ne dan a fasa auren nan wata zuciyar kuma tace mata karma kije dan Ba abunda zai hana auren nan.

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now