LAIFINA NE 26

88 10 3
                                    

*PAGE 2️⃣6️⃣*

A gajiye Fauxeey taje gida, Koda ta isa gida as usual samun ummanta tai zaune a sallaya, Itama alwala tai tazo tai Sallah, Azkar tayi, basu tashi ba seda sukai sallar ishsha'i, tana zaune Kanwarta ta kawo mata abinci, taga tana murmushi

Fauxeey tace me aka samune?

Ummie tace infada miki yau nayi new catch da naje kasuwa, barima kiga pic dinshi, tana magana tana kokarin Shiga gallery a wayarta, Fauxeey tace uhm Sai yasa naga rawan kan yau na daban ne

Ummiey dai Shiga gallery tai ta Nuna mata hoton wani kyakkyawan saurayi,  Fauxeey tace masha Allah amma bekai Haidar dina kyau ba, ummiey na murmushi tace nidai bance komai ba..

Dariya sukai dukansu, mamansune Tace" Fauziya inada magana dake inkin gama

Gabantane ya fadi tace To umma inajinki, basai ma na gama ba, Maganarki tafi komai muhimmanci a rayuwa

Mamansune ta fara magana kamar haka, Kunga zaman nan bazaiyu wu ba, Ya kamata ke Fauxeeya ki fito da mijin aure, ki manta da duk abubuwan da suka faru a baya,

Fauxeey yanda taga mamanta na magana tasan tana cikin damuwa, dan haka ta kwantar da murya tace laaa Umma kwanan nan kuwa za kawo maki sirikinki, nima Inada bukatar kiga aurenmu,

Mamansu tace to shikkenan, Allah ya kaimu ya nuna mana, Sukace Ameen

Fauxeey shiga Daki tai, Kwanciya a yar katifarsu tai tana kallon silin, Abuwane da yawa suke mata yawo akai, gashi Ta  tsana taji ana mata maganar aure, to yanzuma bata da saurayi dan tasan Haidar is Hardly ma ya kula ta dan ba karamin abu tai mai ba, Wani dogon nunfashi taja tace Aure lokacine..

    Tana kwance Text ya Shugo wayarta tana dubawa taga Wannan number daya saba mata text ne, an rubuta dan Allah in baso kike in mutu ba Ki tausayamun ki picking call dina Ko kimun Reply

Har yanzu zuciyata takasa sukuni, tinaninki take a koda yaushe dan Allah ki saurareni kar alhakina ya kamaki

Tana karantawa Tace wata Sabuwa
Waye Wannan kuma
    Daurewa tai tamai text kamar haka
     Dan Allah Malan kayi hakuri, Akwai wanda nake sone ko ince akwai wanda zan aura dan Allah karka kara kiran number, Tana turamai ya karanta

Muhseen jiyai gaba daya kamar an zare mai wani abu a jikinshi,

Tsaya wa yai yana kallon wayar kamar wani tababbe

HAIDAR POV
      Haidar Kuwa, Tunda yaje masallaci akai magrib, shuru shuru bedawo ba, har akai ishsha'i shima still bedawoba, Mum din shine ta kalle agogon dake jikin falo taga karfe 9:00PM, yaranta na zaune
Suna kallon TV kallon Yasmin Ta kira sunanta tace" je daki ki karamun yayanki, Tashi tai ta tafi, tana shiga taga Bedawo ba

Zuwa tai ta sanarwa mamanta ya Haidar baya nan, What!! Tace se kuma tai shuru

Lalabo wayarta tai ta kira number shi, Yana gani yai picking yace" Salam

Amsawa tai hade da cewa kana inane?

"Haidar yace ganinan wajen abokaina nazone mu gaisa,
   Hade fuska tai tace kai maza maza ka dawo gida in bahaka in saba maka, yanda yai shuru Ahmad yace what's wrong

Sanar dashi yayi, yace" Ok Don't worry ka koma gidan, zamui waya

Haka ya tsame kanshi cikin abokanshi yayi gida, Kowa tambayar Ahmad yake meke faruwa da Haidar ne kwata kwata basa ganinshi a joint dinsu inda suke saba haduwa

Ahmad ce musu yayi beda lafiya ne bakuga ya rame ba, Suka ce eyyah no wonder

Gaba daya hankalinshi baya jikinshi, Jiyai inama karya koma gidan, Bayanda ya iya dole ya koma gidan kodan mahaifinshi da kannanshi da suke nuna tausayi a gareshi
    Tafiya yake Ahankali harya isa da yake ba nisa sosai, Knocking yayi me gadi ya budemai gate, Shiga gidan da addua yayi,

Tura kofar falon yayi gaba daya ya samesu a fallo amma banda abbanshi

Hajara tana ganinshi da sauri, ta mik'e tanajin tsoranshi, Kallonshi tai aranta tace ya za'ai hajiya tace  ba aljani bane bayan bata taba ganin mutun mekyan shiba ba

Hade ido sukai da hajara kara balla mata harara yayi, gaba daya ta tsorata, aranshi yace wannan da a kauye nake ai kadan ne ban haifeta ba, ya za'ai ma in hada jikina da wannan kwailar, wanda Abubuwan jikinta basu gama bayyana ba, shi yanason mace full option Dan shi yasan bana wasa bane, yasan kanshi, yace wannan ai ballata zanyi a ranar farko..

Maman shine ta kalle sauran yaranta tace maza ku bani waje,

Tashi sukai dagame hararar hajara sai me Murguda mata baki, ya rage a falon daga Haidar sai Hajara

    Kallon Haidar tai tace to Gatanan tun yanxu kafara kiwonta, Nan da 2 weeks za'a daura maku aure, A razane ya kalleta yace what??

Tace ai kaji me nake cewa nan da 2weeks nace

Kallon yarinyar ya kara yi, ita kuma ta wangalemai baki, a yanzu tadan fara gane ba aljani bane, tsabar kyau ne, Tace shikkenan maganata dakai se kuma gobe zakuje da ita kasuwa ka siyo mata kayayyakin sawa da kayan kwalliya,

Haidar dan tsabagen Takaici bema iya cewa komai ba, tashi yayi ya nufa dakinshi, Yana shiga Ahmad ya kira ya sanar dashi komai, Ahmad yace meye na tada hankali, karka damu fa

Haidar har ya hassala yace dan bakai bane ko? Kasa kasa da murya Ahmad yayi ya fadamai wata magana, Haidar naga yana dariya kome ya fadamai oho....zamuji nan gaba

Haidar yace to shikkenan
Bayan ya shiga dakin
   Hajara da yake masu surutun nan ne a kauye, tace Hajiya anya yana sona kuwa, naga ko magana bemun ma

Hajiya ta rasa me zatace, tace kunyata yakeji,

Hajara tace amma naga ranshi kamar a bace, Hajiya tai shuru

Hajara mikewa tai da yake taga dakin da Haidar ya shiga, Binshi tai ta shiga dakin

Tana Shiga ta sameshi ya cire riga zai dakko jallabiya ya saka

Jin an Shugo dakin dan haka yai maza ya waiga, ido hudu sukai da hajara, Ga mamakinshi sai ya Ga ko kifta ido batayi ta tsaya tana kallonshi

  Aranshi yace Kagamun yarinya, sun dau kusan 2mins hajara na kallaonshi, da yaga bata da shirin Tafiya

Karasowa wajenta ya farayi tai maza ta fita da gudu

Mamakine ya kara cikashi, kallon jikinshi yai wai me ma take kallo, hmmm Yace ya dakko jallabiyarshi ya saka,

Toilet ya shiga yai Alwala yai nafita still ya kara rokan Allah ya zama mai abunda yafi zama alheri

Hajara da gudu ta karaso dakin hajiya, Tana taso ta mata magana amma kunya ya hanata

Hajiya tace meya faru? Ganin bazata iya fada ba yasa tai shuru, Hajiya tace to muje

    Dakinta ta nuna mata tace gashinan ki kwanta saida safe, kuma karki manta Haidar be fitowa da safe, idan an hada abincin safe ke zaki dauka kikai mai, karki tashi a awajen sai kinga ya gama
    
      Hajara tace to Mama, saida sahe

Kwanciya tai a lallausar katita taji dadi sosai, Tananin saurayinta na kauye tafara yi, Jitai tana kewarshi

Tinanin haidar ta farayi, ita tunda take bata taba ganin mutun ba riga ba, to meyasa haidar ya cire? Tana cikin tinanin ne bacci ya kwasheta

Chan cikin bacci tai mafarkin saurayinta na kauye, Wai ya zatamai haka, sun taso suna soyayya lokaci daya zata gujeshi dan shi beda kudi ko

Firgigit ta tashi.........

Muje Zuwa

Yours Ummiey Xeey

Follow
Vote
Comment

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now