LAIFINA NE 14

82 10 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

Where are my fans....I'm back😍...Aci gaba da gashi

*PAGE* 1️⃣4️⃣

Mahaifiyar Haidar a fusace ta shugo gida, Tundaga window Haidar ya hangota cos yanda yaga tai parking gabanshi yaji yana mugun fadi, yasan anfada mata wata maganar, Cikin shine yaji yana murdamai dan a tsorace yake, Tinanin abunda zaifaru dashi kawai yakeyi,
  Haidar Yana ganin mum dinsu tana shirin shiga parlour yai maza ya shiga toilet dan a tsure yake Sai zawo

Mum dinshi cikin isa ta zauna a kujera ta kalle kannanshi da suke zaune da book a hannunsu suna bitar karatun da yai musu, Kallonsu tayi fuskar nan ba fara'a tace kubani wani ina yayanku?

Cewa sukai Yana ciki sanan suka mik'e Sidif sidif suka tashi suka shiga dakinsu, ciro wayarta tai cikin jaka taga miss call din Alhaji Abdullahi Dabai mijinta kenan baban Haidar, Calling back tayi shi kuma a daidai lokacin Haidar ya fito daga toilet ya labe yanajin abunda take fadawa Mahaifinshi, Kaf, abunda Aisha igala suka fadamata, Exactly ta fada mai, Haidar kuwa dan haushi kamar ya kwalla ihu, Lalle wa ennan munafukaine, jiyai mum dinshi tace barima na ma sending audio din Dan nayi recording, Katse wayar tai, ta shiga whatsapp tamai sending, sauraro yayi yaji gabashi na fadi dan ranshi yai matukar baci,
  Kiranta yai yace Na saurara kimai hukunci daidai da laifinshi kafin nadawo, tace" angama basai ka fadaba, sannan ta kashe wayar

Kiran Haidar tayi, Ya zo ya zauna a gabanta gabanshi na bugun uku uku, Kallonshi tai yanda ya natsu a gabanta tace" kabani kunya Wallahi, Ashe abunda ke tsakaninka da wannan banzar yarinyar kenan? Ashe duk tarbiyar da Muka baka wata ta goge maka shi ko? No wonder, biri yai kama da mutun sai yasa kwana biyu muka rasa gane kanka Ashe wata ke controlling dinka? Dago kai yayi yace" Mum karya suke miki ba haka bane ki fahimceni, Ni ba abunda da ya taba shiga tsakani da ita, kawai abunda nasani muna shirine sosai se kuma maganar soyayayya Amma maganar da suka fada miki karyanre, cikin Zafin rai ta kwasheshi da mari zafafa guda 2, tace rufemun baki, Sune zasuma karya? To in karyane ina yarinyar? Beda bakin magana dole yai shuru, Yana mamakin abunda sukaimai, Shi dama yasan Aisha zata iya komai dan ta bata Fauxeey a gun kowa ita a don dole tana sonshi, Dan she once told him indai tanada rai bazata taba bari ya aura wataba sedai inta mutu, aranshi yace Aisha karya kikeyi

Maganar  mahaifiyarshi ne ta dawo dashi daga tinanin da yakeyi na "bazaka janyo mana abun kunya ba, kauye zanje na samo maka mata tun wuri tunda ga abunda kkeyi kenan, Nan take yaji ya tsana kanshi, dan mahaifiyarshi intai magana ya zauna, Kanshi yaji ya dau chaji dan yasan tsab zata aikata abunda tafada, Tashi kabani waje tace" yaron banza kawai, kuma ba aiki zaka dinga zuwa ba inganka ka fita ko anzo nemanka wallahi saina mugun bata maka rai, Ai qin jin maganane irin naku? Meka nema ka rasa, Ina dad dinka nada company akai akai ka zauna a matsayin manager kaqi, yanzu gashinan kaja mana magana anata ka sace takardu, kumaba wanda besan mahaifinkaba, ka fita kabani waje shashasha,
jikinshi a sanyeye ya tashi yabar dakin ya wuce nashi, ran maza ya baci, scattering dakinshi ya fara, Ya jefe pillow chan ya jefar da wan chan haka ya dingayi,

Karar Wayarshi yaji, yana dubawa Yaga Ahmad, Yaqi picking dan ranshi a vace yake, dayaga kiran yaqi karewa kashema wayar yai gaba daya dan a yanda yake sam beson ma magana
****
    Bangaren Fauxeey kuwa tunda ta dawo gida hankalinta ba kwance yakeba, Dan duk sanda ta bude radio maganar fyade fyaden nan takeji, Aranta tace" wallahi da zan zama Wata babba a kasar nan da duk wanda aka kama da laifin Rape, Rataye za'ai yanda addinin islama yace mana, Amma yanzu sam kasarmu ta lalace idan baka da gata se aita takaka yanda akeso, ko idan ana ka men criminals ai akwai a GRA da yawa amma se a shugo ghetto area aita kama da masu laifi da marasa laifi Hmmm, Allah ya shiryar da Shuwagabanninmu tace Ameeen
     
   

Urs Ummiey Xeey

FOLLOW
VOTE
COMMENT

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now