LAIFINA NE 21

75 15 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 2️⃣1️⃣*

Bobo na kwance yunwa duk yabi ya dameshi, kallon agogon dakinshi yayi yaga karfe shida, shuru shuru ba alamun fauxeey Har kusan 6:00PM fauxeey bata gama Abinciba, Bobo dakin mum dinshi yazo, Samunta yai tana kujera zaune tana kona TV, marairaice fuska yayi yana Shafa cikinshi alamun yunwa, yace" Mum kirjina yafaramun Zafi ina tsoron kar ulcer na ya ta shi
  Tashi tai cikin azama ta shiga kitchen din ta farawa fauxeey masifa ita fa batasan Aiki da sanyin jiki, ga son dinta chan ya kusan fadi saboda yunwa, tun break fast din safe beci komaiba
    Bobo na kwance yaji hayaniyar mahaifiyarshi yasan Da fauxeey takeyi, seta bashi tausayi, daya sani beyi magana ba

Fauxeey tace" Hajiya nagama kwashewa kawai zanyi nasa a food flask na kawo, Tow tace" ki sauri dai
    Abun yabaa Fauxeey haushi wai akan banzan yaron da beji zatazo tanamata tsawa, ita gaskiya bazata jure Wulakanci ba, wata zuciyar tace Fauxeey fushi ba naki bane, Yaufa kikazo gidan, idan kinason cimma burinki sai kin jure komai kin rungama hakuri, Hmmm tace ta juye abincin takaiwa kowa nashi, Harda megadi

Hajiya ne ta fara kwasar girkin fauxeey taji ya mata dadi matuka, ita da abinci ko rabin plate bataci yau gashi Harda karawa, lalle Fauxeey ta iya girki, Itako zataso taji wajen wata koya girkin nan

    BOBO kam dagashi sai gajeran Window da wata yar vest, Kiran Fauxeey yayi yace tasamai a plate kuma ka'idan shine indai zaici abinci saida mutun kusa dashi dan zai bukaci asamai ruwa a cup da a dakko mai tissue da zai so yanacin abinci anamai hira me dadi, satar kallonshi tai  Aranta tace" tirkashi

Tasamai abincin a plate ta koma gefe tazauna, se kakkare fuskarta take da hijab, yana lura da ita yace" Kee meye na boye fuska ni dodone?

Tana wasa da yatsunta tace" kai ba dodo bane kuma bazaka taba zama dodo ba, amma naga bedace bane kana shiga irin wannan, kafeta da ito yayi na watsu yan mintina, kamar zaiyi magana kuma saiya fasa,
   Kai hankalinshi kan Abincinshi yayi ya fara ci, Jin dadin abincin seda ya kalle ta, ya duba jikinta anya ita tai abincin nan kuwa? Kara kai abincin yayi bakinshi yaji kunnanshi ya dauka, Abincin yamai dadi sosai amma be nuna zalamarshi agabanta ba

Waya koya miki abinci me Dadi haka yace" kanta na kasa tace tun ina karama muke abinci a gidanmu, yace very good tai kamar batajin turanci tace meye very good? Yace yayi kyau, Tace tooo

    Cin abincin yai sosai yace ta mikomai ruwa ta bashi, Ta sakamai a cup ta mikomai tana zumbura baki, kallon Agogon dakinshi tai taga 7:00PM Tace zan tafi gida dare yayi

Yace aww ba aikin kwana kkeyiba? Tace Eh bana kwana bane, sai ya tsinta kanshi baiji dadi ba, Inama na kwana takeyi, Kawai yaji yarinyar ta fara burgeshi,

tashi tayi tai wucerta, Taiwa Hajiya Sallama tace A sauka lafiya

Fauxeey fitowa tai daga gidan

Waigowa tai ta kara kallon gidan, babban gidane sosai, wannan badan tashiga gidan ba zata iya cewa Gidan yankan kaine

     bobo ta tino, Tace senayi taka tsantsa dan take takenshi bai wuce yace yana sona, Ni kuma ba soyayya dashi ya kawoni gidan ba, ahankali ta karasa gidan su zeenatu ta chanza kaya taiwa maman Zeenatu bayanin komai tace dakyau

Tai mata Sallama....

Ummansu Fauxeey kuwa hankalinta a tashe, cewa ummiey tai ki kiramun fauxeey magrib tayi har yanzu bata dawoba gashi gari bana muba, toh ummiey tace ta dannan wayar zata kira fauxeey kenan Tai sallama a gidan, ummiey tace Gatanan ma...

Sallama Fauxeey tayi cikin natsuwa suka amsa da waalaikis Salam
   Samun waje tai ta zauna Tana maida nunfashi dan ta gaji sosai

Kanwartace ummie ta kawo mata abinci ta fara ci, Dayake bata salla tana off, kwanciya tai dan ta huta dakko wayarta tai ta fara latsawa
   Text ne ya shugo mata da wani lamba, Ta bude text din ta fara karantaw..." _Salam gimbiyar mata, tun lokacin da idanuwa na sukai tazali dake har yanzu na kasa samun natsuwa dan Allah inkinga text dinnan ki kirani_ tana karantawa ta goge dan ita batasan ma mu'alama da kowani namiji, Ita sam aure yanzu bashine a gabanta

****
   Muhsin na ta duba wayarshi, Yana ganin message din Fauxeey yai delivered Yaji wani sanyi aranshi, Atleast zata karanta, Abokin shine yace hmmm Ina mamakin ka fa, Daga ganin yarinya bakasan asalinta ba zakabi ka dama kanka? Kai kasan ko irin yan iskan matan nan ne, ko shigarta sam be nuna mutuniyar kirki ba, please ka dena damun kanka

Jin maganar Abokinshi yasa ya tsuke fuska yace dan Allah karka sake ce mata yar iska, And ko tanada Asali ko bata dashi sai ta zama mallakina,

Abokin yace to Wallahi saina sanar dasu Hajiya, idan ma wani Abun kagani a idonta ka zauce haka za'ai gaggawar karya shi

Shuru Muhsin yayi yace bazaka gane SO bane...

***
   Fauxeey bayan ta gama karanta text din nazari ta fara shin waye wannan? Ajiye wayar tai Mahaifiyarta ta lura da ita, Fauxeeya tace"

Naam mama

Mamansu tace ina matukar tausaya miki akan wannan aikin, Baki samun Hutu kwata kwata kodai zaki hakura dashine Mu koma Garinmu muci gaba da rayuwarmu, in yaso kudin Nan Da muke dashi sai ku fara wata sana'ar
Bacci fauxeey takeji amma da taji maganar mahaifiyarta Zumbur ta tashi, Tama rasa me zatace
    Ga samu yana neman ya zama rashi, yanda ta shiga gidan su Usman bobo dinnan Ai se ta aiwatar da abun da tai niyya inshaa Allah, Dukda tanason ta koma Wajen Haidar amma Tana ganin abunda tasa agabanta yafi muhimmanci

Budar bakin Ummiey tace" Aikuwa mamah, For how long zamuita zama a garin nan, Ai gwanda inda muka taso tunda kince kwata kwata baKison zaman Bauchi,

Fauxeey tace" yanzu duk abunda akai mana ku zakui marmarin zaman bauchi? Nikam bazan mantaba wallahi, koda yake Ummiey Ke kadan ne naki ni kuma fa? Wallahi dan mugunta bada kyau ne da duk saina rama

Mamansune yanda taga Fauxeey na magana Tace Duk kuyi hakuri, ku manta da Abunda akai muku abaya, shi dama rayuwa haka take yanzu ba gashi kuna bada labari ba?

Wani dogon nunfashi Fauxeey taja....Ummiey tace" to iyayan Zuciya ayi hakuri SABR please sisto, Binta da kallo tayi tace eh An man dai ai ancecu mu

Ummiey Tace" Hakane

Fauxeey tace wlhi mama badan keba da tuni na Hada musu Tarko, yanda suka bamu wahala ko,
Mamansu na murmushi tace" tunda ma muna da rai da lafiya basu nakasa kowa cikin muba Ai mungode Allah

Fauxeey tace" hakane amma badan mun tashi tsaye da addu'a ba da yanzu sun gama illatamu

Mamansu tace kudaiyi Hakuri, Allah dai yasa muku albarka Sukace Ameen

Chan dare number da akaiwa Fauxeey text sai kiranta yakeyi, Ya kira kusan 8 Fauxeey tana gani taqi picking

Muhsin yaji sam bejin dadi a ranshi, Tinaninta Yake tayi dakyar bacci ya kwasheshi

    Beyi nisa da Baccin ba yai mafarkin wai ga wasu kura ye nan nabin Fauxeey, tanata gudu sai gashinan yazo, tana ganinshi ta fada jikinshi tana kuka

Firgigit ya tashi Yana salati.....

*Shin me akai musu Fauxeey haka ne*

*Shin Menene dalilin da yasa Fauxeey ta tsana maza*

Amsoshin nan suna Nan gaba kuci gaba da biyoni💃🏻

Gaskiya idan bakwa comment zan tsaya da rubuta book din haka

URS UMMIEY XEEY

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now