LAIFINA NE 13

85 10 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       ❤️ *LAIFINA NE*❤️
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*Ina ganin comment Dinku, Ina godiya sosai*

*PAGE 1️⃣3️⃣*

Hajiyarsu haidar samun waje tai tana danna wayarta, Kallo daya zakai mata kasan ta amsa Sunan ta, Farar macece dugowa ga jikinta Dan moderate dinnan, Batada kiba sosai amma gabobin jikinta manyane sai yasa wasu suke ganinta kamar tanada kiba, Aisha Igala ce ta kalleta tace" Bari na kawo miki abun sha ko? KO kallonta bataiba tace No karki damu bana bukata, hada ido sukai da hashimu ta kashemai ido...
   Haidar kuwa tunda mamanshi ta tafi hankalinshine ya tashi kasa sukuni yayi, Yasmin ne kanwarshi tace" yaya dan Allah kai hakuri akan abunda ya faru, kowani bawa da kaddarshi please karka damu kaji yayana komai zaizo ya wuce, tana magana tana langwabewa

Kallonta yai, yaji sanyi akanshi tabbas kanwarshi nada kankali, kuma maganar data fada hakane, Seyai mata Smiling yace OK baby Sister, Adaidai lokacin Safiyya ta shugo rik'e da coffee a hannunta guda biyu, Tazo kusa da Haidar tace" ya haidar gashi, Kallonta yai cike da kaunar ta dan yana mutuwar son kannanshi Dan sunada hankali sosai, yace thank you sister, Tace Ur wlcm ya, itama takai cup din bakinta ta Fara shan coffee tanawa Yasmin Gwalo, Haidar Kwana biyu bamuji kuna waya da Fauxeey  ba Lafiya? Gabanshine yaji Ya Fadi, kifkifta ido yafarayi, Da Alama basusan meke faruwa ba, kallonta yayi rike da coffee a hannu yace tananan kuma

Yasmin tace" ana nunamun yan ubanci yanzu Safiyya kinfison  ya Haidar akanni, nimadai inada kafa, tashi tayi taje kitchen ta hada abarba juice yasha citta da kwakwa da sugar se kamshi yakeyi, tazo tace nimadai ganawa nan tunda ana nunamun Wariyar launin fata dan ku kunga farare ne ko? Tana magana tana shagwaba Dan maganarta rabi shagwaba ne
    Haidar kamar zai fashe da dariya seya Dan murmusa ya tinafa mum nachan kuma yasan negative Amsa zata dawo dashi, Dan haka binsu da kallo kawai yayi, yana addua A azuciyarshi Allah ya kawo komai cikin sauqi

   ****
  Hajiya lubabatu na zaune kusan 30mins, kafarta daya nakan daya, ta kalle su Aisha tace manager nan kuwa zai dawo?
Aisha igala tace me kike bukata da muryarta da ba hausa takeji sosai ba, Tace" nazone akan maganar takardun da akace sun bace ko kunada masaniya akai kufadamun gaskiya nice mahaifiyar Aliyou haidar matar Tsohon ministan man fetur

Aisha Igala da Hashimu rudewa sukai sukace matar Ministan man fetur, Dama Aliyu dan tsohon minista ne? Dama tsohon minista nada babban yaro haka,

Hajiya lubabatu murmushi tayi, Tace" wani abun ne? hashimu ya fara Sosa kai yace Kwanakine aka tambayeshi agabana akace kokai Dan minister ne saboda sunan yazo daya yace" A'a bashi bane kawai sunana yazo daya shine muke mamaki

Hajiya lubabatu tace kayya kuna aiki anan bakusan Asalin Haidar? Har a radio aka fada anan naji labarin sai yasa nazo Dan jin ya akai hakan tafaru? Hajiya tace" basusan korarshi zai iya ja musu a rufe company din nan ba? Nan hanjinsu ya kada lalle matarnan da zafi take yanzu aka rufe ai sun Shiga tara

Tace nibashi ma ya kawoni ba KO kunada masaniya akan ya hakan ta faru, Aisha ne taiwa Hashimu magana ta ido saboda already yasan kudirinta, Ya soma magana kamar haka, Haidar nada wata kawa Ko ince budurwarsa  anan Company din to gaskiya yarinyar ance baasan asalin taba, anjamai kunne akan ya rabu da ita yaqi,

Dan tsaya Hajiya lubabatu tace" dakko wayarta tai yana magana tana recording, yaci gaba da cewa yarinyar nan sunanta Fauzeeya shu'umace, duk abunda tasa haidar se yayi, karshemai har fita sukeyi  saboda Zargin yarinyar akeyi, Duk tagama bata Mai tarbiyya, Ga irin dressing din da takeyi da wanda zai mata kallon yar mutunci
     Zufa ne yake ketoma hajiya lubabatu aranta tace biri yai kama da mutun, ci gaba Ina jinka, To karshema dai kamar fada sukai tace itace ajalinsa, Ita ta dauke takardun tasa aka koreshi tace saitaga bayanshi

Hajiya lubabatu tace" dan Allah kunsan gidan yarinyar? Aisha Igala tace calm down hajiya, ai yanzu yarinyar ta gudu, ba'asan Ina takeba, ta tarkata iyayanta sunbar garin dama zuwa sukai ba'asan Asalinsu ba

Wani ajiyar zuciya Hajiya tayi tace" nagode maku, cikin Azama ta Shiga motarta ta fita zuciyarta cike da tunani

    Aisha Igala bayan hajiya tabar wajen ta kalle Hashima tace" Ana mata hatsabibai ne ashe kafini hatsabibanci, Da nine ai bazan iya wannan maganganun ba, I Salute you hashimu,

   Murmushi yayi yace" haba ke ai tawace yanzu saiki bani ladan karyan nan da nayi,
Tace" karka damu konawa Zan baka

Kara mastowa da kujerta tayi, tace" dama Haidar Dan babban gidane? Kace naga wajen zama sena aureshi

Hashimu dariya yai yace Kefa abunda kkeso sai kinyishi nidai yar tayakice

Wani Shu'umin dariya tai tace yanzu aka fara, Hashimu yace tabbas kuwa

****
   Su Haidar kuwa yana zaune da kannanshi suna hira sannan yana Kara musu nasiha da subi duniya ahankali, Dan Allah su rik'e tarbiyar da aka basu, sukace yaya Haidar insha Allah

   Hajiya lubabatu kuwa tana driving tana kiran numbern mahaifin Haidar da yake yana kasar waje, Yanata ringing bedaukaba, Tinanin zuci ta fara tace no wonder biri yai kama da mutun, a wannan satin gaba daya a rikice yake, Kuma da Chan karfe 4 nayi yadawo amma yanzu sam Seyakai magrib ahanya yace aikine yamai yawa, Zanje gidan insameshi tace hmmmm

Sauri sauri taakeyi taga gidan ma yayi mata nisa tuki takeyi amma kamar baya yake komawa

***
Bangaren Fauxeey kuma bayan ta fito gidan baba mairo ce bayan laasar taga akwai sauran lokaci dan haka Tabiya ta  layin da akaiwa yarinya fyaden nan, Ta tsaya chan da nisa tana karewa gidan kallo, yanzu tinanin ya za'ai ta sama aiki a gidan? Seda ta gama kalle kallenta tana dai tsaye a wajen taga wani saurayi ya fito, Basai ance maka wayeba  duk yanda akai shine dinnan da ake kuka dashi a unguwar, dagashi se jallabiya, daga nesa ta hangoshi amma dukda daga nesan ne ya hadu. tare napep taga yayi a kofar gidansu, yai maza ya shige saiga Yan Mata wasu su biyu sun fito daga gidan, da sauri ta dakko wayarta ta daukesu, hade wannan saurayin, ya daga musu hannu, ne Nepep yaja yai gaba,

Kallon inda take yayi yaga kamar ana kallonshi kara kurawa inda fauxeey kallo yake kamar ana kallonshi,tai maza ta juya bayanta ta labe a bayan wata bishiya,

Shikam yana tsaya yana kallon wajen tabbas jikinshi ya bashi, akwai mutun a wajen Fara karasowa yayi inda yaga fauxeey dagata hakan tai maza ta ruga da gudu ta shige wani gida,

Dayaga kamar anbar wejen sai ya juya ya koma gida amma gabanshi na fadi, kasancewar layin ba kowa GRA ne,

Jinjina kai tayi tsoro duk ya kamata kardai ya biyota, cikin tsoro ta fito ahankali ta tere nepep yakaita gida..........

mahifiyar Haidar kuwa A fusace ta dawo gida.........

Muje Zuwa

Dan Allah comment dinku da vote sunayin kadan Ku karaaa

Muje zuwa

Urs Ummie Xeey

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now