LAIFINA NE 8

124 8 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 8️⃣*

Fauxeey na dakin Seemah ta mik'e tsaya tana yafa gyalen abayarta, Kallon Seemah tayi tace ni Zan wuce yanzu! Sai Allah ya sake hadamu, Seemah riketa tayi tana kuka baba mairo ta shugo "tace mai yafaru? Fauxeey ne "tace Mama zantafi ne shine take kuka, Baba mairo itama bataji dadi ba, Tace Da sauri haka? Yanxu ina zaki nufa? Fauxeey tace kamar yanda na fada muku aiki ya kawoni, So zanje ne na duba wajen Naga a masaukin da akaimun! Baba Mairo tace Hakane, Allah yayi Albarka, Fauxeey tace" ameen, Nagode nima, Da zata tafine ta dakko kudi masu yawa ta basu tace susai abinci sannan taba Seemah phone Number dinta tace Dan Allah ta dinga kiranta akai akai suna gaisawa, Kuma intasama lokaci Zata dinga zagayowa suna gaisawa, baba Mairo "tace mungode

   Fitowa sukai tare da Seemah zata rakata, nan Ta kara Mata nasiha akan please Ta natsu, we're all human being's, We're not perfect dukda muna laifi amma Dan Allah taji tsoron Allah, Tasani akwai mutuwa, yanzu idan ta mutu mezatace wa ubangiji? Zaman kabari ma kadai ya isheka tun kan azo ranar hisabi, Allah yasa mucika dakyau da imani Ameen,

   Tabbas kuwa Seemah maganganun nan ya tsuma Mata jiki, Cetama tai tagode, Fauxeey tace" bakomai, Ki koma gida ni Zan sama mashin ya karasa Dani, tace OK to bakomai Gashi munyi Sallama zaki tati bakiban labarin ki da tarihin rayuwarki ba amma kinsan zanso hakan? Fauxeey tace muna tare ai inshaa Allah bawai munrabu bane, Zakiji komai tana magana tana murmushi,

Seemah tace nagode yaruwa

Bayan Seemah ta tafi, Fauxeey takawa a kasa tafarayi tana kallon garin da yananin al'adarsu, musulmai ne amma suna social life, Dan Wani wajen baka gane musulmai da arnan, kowa yana Shiga yanda yakeso, Dan haka mashin ta samu tace yakaita gaba da unguwar nan, Yace ta Kawo 70naira tace to, Shiga wata unguwa sukai, Unguwar sabuwa ce, Akwai manyan gidaje akwai kuma irin namu na yaku bayi, Chan daga nesa ta hango Wasu mutane sunyi dandazo kome ake awajen oho, Cema me mashin tai ya sauketa, ta bashi 100, Ta karasa a kafa inda akai dandazon, Saboda mutane da yawa ba wanda yasanta, Kasa kunnanta tai taji meke faruwa,

Wani mutun ne Yace" ai kunga irinta kuma kudinga hakuri da abunda Allah ya baku, Akwai sana'oi kala kala basai kundinga kai yaronku suna bauta a Wani gidan ba, Wai da sunan nemo abun duniya, fauxeey tace" aranta Exactly akwai littafin dana karanta na fresh ummiey xeey *Silar gidan aiki* Duk kusan abunda yafaru kenan, Iyaye wasu basa duba wani hali yaransu suke ciki, sudai asamo masu kudi, tana cikin tinanin Zuci ne, Taji uwar yarinyar ta kwarma ihu, tana tashiga Uku, Wani yace Yarinya ta Uku kenan fa da akaiwa fyade a gidan, da zaran uban yaji labari saiya turashi kasar waje koda ance yarinya ta nuna wanda yai mata sai suga babu, dole zasu hakura

   Fauxeey tana gefe tana karema yarinyar kallo da bata wuce 10years ba, daga gani girman jikine, Aran fauxeey tace muma da muke yanmata taka tsantsa muke da maza barega Wannan yarinyar matasani,

Anadaita surutai daga masu Allah ya kyauta sai masu Allah Ya tsare nagaba, Yarinyar na zaune a kasa jini sai zubo Mata yakeyi, gasu talaka daga ganin kudin da za'akaita asibiti ma aikine
   Jitai tausayinsu ya kamata, Aranta tace kodan uban Waye sainayi maganinshi, Niko nace zaki Iya kuwa? Tambayar wani tai  inane gidan da akaima yarinyar fyade, Aka ce gashi shan Upstair din Chan, Ta jinjina kai tace" OK tana mai nazarin Wani Abu

Kowa ya watse, Yayan yarinyar ya dauketa sukai hanyar gida ba wanda ya taimaka musu, bayan an watse ne fauxeey ta dakko wayarta tai snapping gidan, Sannan ta kalle sunan Layin ta rik'eshi akanta

Fauxeey kuwa bin Bayin Allah nan tayi suna tafe tana binsu a baya da sun waigo saita juya kamar basu take biba, wata sa'in kuma ta Fara danna wayarta, tana dai ta binsu har suka isa gidan, suna shiga itama ta shiga

Maman yarinyar ce ta Fara kuka tana yanxu wazai temaka mana, muda hatta abinci ba samu muke ba, a daidai lokacin Fauxeey ta shugo, Tace Allah ne ya kawoni Dan na temaka maku!

Sake baki sukai suna kallon abun kamar a film dan basu taba tinanin haka

Nan fauxeey ta jajanta musu, tace Wani Asibitine kusa aka dauketa aka kaita, Dinki akai mata sannan aka ba yarinyar magunguna, fauxeey ta Biya kudin komai, ta Kara da cewa meye sunan yarinyar?

"Sukace sunanta Zinatu, Tace OK,

Nan yayyin Zinatu suketa ma fauxeey godiya, sukace badan itaba basusan yanda zasui ba, Murmushi tayi tace ko banzo ba, Allah zai kawo wani, Domin Allah na duba bayinsa na gari, Maman tace tabbas hakane, fauxeey tace to Zan tafi, Nan ta Ciro kudi kusan 20K ta basu tace dan Allah KO kunu da kosaine su Fara, Allah ya Kara Rufa mana Asiri, godiya sukai Mata sosai, Sukace Ameen, nan ma Tasha addu'a a bakin mahaifiyar zinatu, Tace inshaa Allah nan ma zata dinga zuwa tana duba su Sukace sungode kwarai

Sannan ta kalle Zinatu tace Allah ya Kara sauqi, Zinatu cikin kuka tace Amin Aunty nagode, Harta mik'e zata tafi mahaifiyar Zeenatu tace Dan Allah wacece ke? fauxeey tai murmushi tace" bakowa bace ni, Nima kamar Ku nake, Amma lokaci kadan, Zaku San ni sosai, Maman Zinatu tace to Bakomai mungode

    Fitowa gidan tai tasama waje Chan gaba ta zauna ta kira Su ummanta da kanwarta Ummie, suka gaisa tace Hope kuna Lafiya? Sukace Lafiya lau tace to Alhamdulillah Anjuma zaku jini komun dare Zan dawo, Maman tace kinga wajen kuwa? Tace Eh amma yayi nisa, sedai nadawo zamui magana umma tace to Allah ya tsare Allah yayi Albarka, Fauxeey tai murmushi Tace Ameen, Mik'ewa tayi tace My Mum's prayer's Always keeps me moving, To Dan Allah yan uwa mukasance masu yiwa yaranmu Addua a koda yaushe...

Tafiya tai tayi batasan ko inaba hartazo kan titi Tsallaka titin tai ta ga wani shago shi kadai a jikin wani gida, kuma da alamun Sabon gini ne ba'a Shiga ba, Tambayarshi tai dan Waye me gidan, yace kinasone? Tace in ba'a kamaba ba, "yace Kai da kyar in ankama, ya nuna Mata wasu tanfatsa  tanfatsan gidaje Chan gaba dasu, Yace duk na shine in kinaso ga number shi nan a jikin gidan, ki Kira shi

Tace Ooh To nagode, Daukar Number tai sukai magana yace to badamuwa, Akai sa'a yana kusa, zuwa yayi sukai chiniki, yace a shekara 150K , Falo ne se dakuna 2, da toilet da kitchen se tsakar gida dan madaidaici, tace Ok munason na shekara biyune nan take tamai transfer na  2years 300K kenan, ya bata receipt, Tace zuwa gobe inshaa Allah zasu dawo yace to bakomai

   Magrib ya kusa samun adaidata sahu tai ya kaita hotel din datai keeping her Mum & sister

Shiga tai da Sallama, mammansu ta amsa lokacin Ummie na sallah

Sannu da hutawa tace, mamansu ta amsa da yawwa, ya hanya? Tace Alhamdulillah

Ummie Na idar da Sallah bayan tai azkar ta gaisheta, har tana mata tsiya kinsha kwanan tsami wai yau kece wuni Harda kwana baki chanza kaya ba?

Fauxeey tace to nadawo kenan zamu Fara, Ummie tace ya ya haidar nasan kinata missing dinshi, mamansu dai najinsu batace uffan ba

Fauxeey hararta tai tace agaban Umma KO? Aranta kuwa ita sam tama Manta da wani Haidar dan taga bayin Allah su 2 suna cikin Wani yanayi, Sai alokacin ta tino yanzu Ko wani hali yake Oho tasan dai confirm gobe no going to Work Dan an dakatar dashi, Oh Allah tace a fili

Da sauri mamansu tace" Lafiya?

Tace Lafiya lau umma nagajine

Nikuma nace zakiyi bayanine, Hakki ba karya bane tunanin zuciya saiya fito fili ne ma Lol....

Haidar Kuwa tunda yaje wajen abokinshi yai shuru, kanshi inbanda saramao da yakeyi ba abunda yakeyi, Tinanin Fauxeey ne yabi ya dameshi meyasa ta aikwata wannan aikin

Yanzu ina ta nufa? Tausayinta ne ya kamashi, Nace Allah Sarkii, Lalle kanason Fauxeey duk abunda tai maka baka ganiba? SO KENAN me hana ganin laifi....Muje zuwa

Urs Ummiey Xeey

VOTE
FOLLOW
COMMENT

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now