LAIFINA NE 41

79 13 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 4️⃣1️⃣*

Ummiey ne kwance Akan gado, Itama ta suma, Nan da nan dr Ya fadawa Mama kasancewar ita taji sauqi dan Haka daga jinyar kanta ta dawo Jinyar Ummiey Dan Dr Muhd yamata alkwarin Duk inda fauxeey take inshaa Allah seya nemota ko a raya ko a mace,

    Farfado wa ummiey tayi daga doguwar sumar datai, tana ina takeee, ina takeee, Maman sune na rike mata hannu tace ganinan, shuru tai Tana nazari itafa kamar taga Fuskar fauxeeya a hospital dinnan, Amma tana tinanin mafarki tayi dan haka tai shuru dan tafi dangarta abun da mafarki

   ***
     Bangaren Aisha Igala kuwa yau sun shirya da Hashimu akan Zasu kaiwa Haidar Ziyara dan Haka ta dakko abun da bokanta ya bata yace mata ta tabbata se zasu hadu zatai amfani dashi,

Shiryawa sukai Tsab suka nema nepep suka hau Har kofar gidansu Haidar Sauka sukai Me Gadi yaje ya kira musu Shi
   Har Ya fito Seya tina da Mafarkin da Yai na Fauxeeya akan ya tsare Azkar ya kasance kuma duk inda zaije yayi addu'a
Addua yayi sannan ya tinkaro kofar gate din

    Ita kuma Aisha Igala tasan yana shirin fitowa, kuma se kai 30mins wani be wuce ta layinsu ba saboda GRA ne she's sure shi zata fara gani, dan haka tai maza ta ciro abun da bokanta ya bata ta goga A fuskarta da jikinta

  Ya fito kenan bata kai ga kallonshi ba, Wani Sautin Kida sukaji, ya dauke masu hankali Dukansu suka maida hankalinsu wajen
Wani Mutun harda Haidar din, Shi ba mahaukaci ba shi ba mutun me lafiya ba ko sanyine ya bugashi Ni kaina bansani ba, jikinshi yaji kayan sanyi yai fururu ga k'ura duk yasa kaya yai datti ga wan canvass kafarshi Tafkeke, Hannunshi rike yake da wani radio yana Shan kida kamar na yan bori,

    Nan take suka hada ido da Aisha igala, Murmushi ya sakar mata, Kwalla ihu tai tace" Na shiga huku Hashimu, bashine nakeso ba, Haidar nakeso

   Haidar tsayawa yai yana kallonta
Kamar wasan kwaiwayo wani irin ni takeso

    Shikuma mutumin nan Ya zo Kusa da igala yace Nice Wanda Bokan ki yaiwa aiki ba kan Haidar ba ya wani kwashe da dariya, Nine dama zaki fara gani, Haidar Kallon Hashimu yai yace meke faruwa ne wai?

Dasauri  Haidar Yacewa Megadi yaje ya kira su Hajiya da Alhaji, Aiko jikinshi na rawa Ya nufa, 2mins Saiga su sun fito

Nan Aisha igala ta rikice fada suka fara da Hashimu, Anan suka tunawa kansu asirin Har Aikin da Akasa Aka kora Haidar har Shiga malamai Da Aisha igala takeyi na akan a rufe bakin Hajiya da Shi kanshi Haidar din Amai asiri dan ya aura Aisha

Hajiya lubabatu and Co tsayawa sukai suna kallonsu kamar  a film,

"Aisha Igala ta chakomo Hashimu Tace seya biyata kudin datake bashi, Yace Bazan biyaba, kin tina lokacin Da Hajiya tazo Company kikace a hada karya da gaskiya a fada mata, Se yanzu kinga Bokanki be miki aiki da kyau ba zakice in biyaki

Haidar Alhamdulillah yace Allah na godema da ka wankeni a idon mahaifiyata, Allah nagode maka da Kasa bani bane farkon wanda tai tozali dashi, yanzu dama asiri sukai Suka nufo Ni? Lalle Allah yayi gaskiya da yace ku lazimci azkar domin Kariyace gareku Alhamdulillah

Haidar ce musu yai Maza kubar nan Ko In kira muku sodoji kuje chan  ku karata

Ba yanda suka iya, Hashimu nan take yace Haidar ka yafemun dan Allah, Becemai uffan ba, kallon Aisha igala yayi yace seda na fada miki Gaskiya kikaqi,

Harararshi tai tana kuka, Shi kuma dayan bokan na nan makale da ita yace Kizo mutafi

Zaka hannu akai tai tana kuka kaichonta yau,

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now