LAIFINA NE 25

77 7 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 2️⃣5️⃣*

    Bobo kafeta da ido yai, yace inajinki, tace" Ok ta fara gyara murya, murmushi yai, Tashi yai da kanshi ya miko mata ruwa Swan yace tasha yanda zataji dadin bashi labari

     Bismillah tai ta kurba ruwan, Still idonshi na kanta ko kiftawa bayayi,

Labban tane suka fara motsi alamar zatai magana, Kallonta yai yace" namanta na fada miki wani abu, idan kikaimun karya kinga bindiga ko? saina kasheki, Kuma ba wanda zaisan nayi,

Taji tsoro sosai dan komai ma zai iya amma tasan Wasa yakeyi, tace Bazan maka karyaba tana magana kamar zatai kuka muryarta na rawa

Da zata fara magana tai nazarin dole ta chanza muryanta, dan idan tai magana me tsaho tabbas zaigane, So sai tafara tana in'ina gashi she's good in English dan zata iya subutar baki tai turanci dan bazata iya magana mai tsaho batare da ta hada da turanci ba
Tace kamar yanda kaji anacemun Fauxeey, sunan yasamu asaline

Gyara zama yai yace Ko ina jinki

  "Tace sunana Zainab Na dade a birni inda nai Saurayi Fauwaz, to dan bokone sosai nikuma kaga daga kauye nake, shine ya hada farkon sunanshi da nawa, nashi Fau nikuma Xeey, anan aka sama Fauxeey,

Bobo tun lokacin da tace Saurayi yaji yanata jin haushi,

yace ina shi fauwax din? Kuma dan gidab waye

"Tace" yayi aure, Kasan masu kudin nan bazasu taba yarda su aura yar talaka ba bare ni yar kauye,

Yace" Ok
    Yace ku asalin yan inane? Tace" a wani kauye muke Karfi, yace Ok
   
Tunda ta fara magana yaji maganarta is different da wanda yaji dazu, so sai wata zuciyar ta cemai ba ita bace gaskiya, Dan wanchan sunanta Fauxeeya, amma kuma abunda yake dauremai kai hatta a fuska sundanyi kama sedai wannan tafi wanchan wanda suka hado a school a Dubai kyau, kuma wannan sam bata wayeba amma wanchan ta school din tasu a awaya take
Tana magana yana kallonta,

"Tace ni marainiya ce

se tabashi tausayi,

"tace banda kowa Se mahafiyata da kanwata guda daya ummiey Munsha wahalar rayuwa ko ince muna sha ma, dan na abincima gagararmu yakeyi

Bobo yaji dadin maganar yace" Ina suke mamanki da kanwartaki? Tace suna kauye

Yace to yanzu a ina kike zaune? Kuma kedawaye, gabantane yai muguwar fadi, Tace Wasu bayin Allah ne

Yace" Ok

    Murmushi yai ya kalla agogo yace ki tafi gida, Tace to bakaban labarin wacce kke nema ba

Yace" gobe idan kingama aiki zan baki labarinta tace" Tace To Ya Allah ka kara tsareni da sharrinshi,

Shi kuma bayan ta fita, Ya buga kafita yace" Yess zan cimma burina, Yarinya sai kinyi nadamar zuwa gidan nan, Ba wanda ke shugowa ya fita ba tare dana fiddamai budurci a tare dashi ba,

A sannu zan janyo ki a jiki yanda zaki summiting gaba daya, Kuma dole ki dawo aikin kwana gidan nan, Nan yaji yana feeling dinta, dan she's beautiful, gashi duk lokacin da yaji muryanta sai yaji wani iri

     Fauxeey kuwa da zata fita gidan tai adduan fita gida, haka takeyi ba inda zatashiga ba tare da addua ba, Tana tafe ahankali tino karyar datai mai ne, na wai ta taba saurayi fauwas
Anan aka sama Fauxeey, bushewa da dariya tai, tace wawa kawai saboda karamar kwakwalwarshi har ya yarda,

Tino bindigar daya nuna mata yai, Da yanzu yagane itace Fauxah da yanzu haka yakasheta, Itafa tsoro takeji, gaskiya bazatai aikin nan ita kadaiba dole ta sanarwa aminiyarta Farida, in case wani abu ya faru tasan zata iya komai ita faridan dan tonamai Asiri

   Tana tafe tana tinani barkatai a zuciyarta..

Shi kuma bobo hawa upstairs yayi (gidan sama) Ya tsaya yana kallonta, Yanda take tafiya ahankali, yaji yarinyar ta kara burgeshi

Wasu mazane suka tsayar da ita suna tambayarta ko tasan Alhaji Bala, Tace aa bata saniba, ita bakuwa ce suma binta da kallo sukai

Bobo Kuwa nan da nan yaji yana kishinta ko meyasa oho, Shi bayason idan yana tare da wata a dinga mata magana

        Kishi yaji yaga bazai iya tsayawa ba dan da alamu tsaf mazan nan zasu iya binta dan haka sakkowa kasa yai abunshi ya shiga dakinshi

     Kamar Ancewa Fauxeey Bobo be kallonta, Bude jakarta tai ta dakko wayarta

Haha Nace Allah ya rufa maki asiri dama yana zarginki, daya kamaki da waya ba ruwana Lol

Kiran Kawarta tai farida take sanar da ita ga halin da take ciki, Nan tai mata kwatancen Usman Bobo saboda School daya sukai da Faridan itama,

Farida kwalla ihu tai  driving takeyi amma seda ta sama waje ta parka, tace are you serious? Tace" I'm serious,

Farida tace kodai kamane? ni ban yardaba dan Wallahi nima da zanganshi yanzu seyayi nadama,

Fauxeey tace zan tura hotanshi a wayana zan turo maki kigani da idonki

Farida tace" Wow What a Sweet story wato Bobo nanan, yananan da halinshi kenan, Zai gane kuranshi

    Fauxeey tace" Ki tayani addua dan Aikin nan da nasa kaina hatsarine, he can kill me a duk lokacin da yagane gaskiya,

   Farida tace" Calm down, inshaa Allah ba abun da zai faru yanzu ki turamun  Address dinshi, Fauxeey tace" Ok Yauwa akwai ma wani pic dana daukeshi yan mata su biyu sunfito a gidan,

Farida tace Very good, Ki turamun shima, Da duk wani abu idan kinsamu game dashi make sure kinyi snapping kin turamun, zaigane kuranshi
    Fauxeey tace Alright Kawata Sai anjuma
Sukai Sallama

Ranar Farida jinta tai kamar An maya albishir, koda yake albishir dinne

Shiga WhatsApp Fauxeey tai ya turaa farida komai da komai
   
Farida was surprised ganin abun take kamar a mafarki

Dukda hoton Bobo daga nesane amma tabbasa shine, Sake baki tai tana karewa hoton kallo

Lalle bobo, Tasha wahalar bobo sosai, Saboda Shi Hakanan ta hakura da school a dubai ta koma Sudan da karatu,

Fauxeey ta kirata tace kingani ko? Kinyadda yanzu?  Farida tace yes na yarda Wallahi, ikon Allah

Fauxeey tace ina hanyane idan nakoma gida zamui magana

Farida tace Ok

Taren Mashin tai ya karasa da ita gida

      Muje ZUWA

Urs
    Ummiey Xeey

Follow
Vote
Comment

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now