LAIFINA NE 15

89 10 1
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 1️⃣5️⃣*

Washe gari
    Tun asuba Haidar ya tashi yai wanka kamar zaije office, Kasancewar ana dan sanyi agarin kuma ba inda zaije ya dakko track suite dinshi ya saka sky blue yamai kyan gaske kamar dan kasar waje, ga gashin gemunshi dan daidai ga Sumar kansa ya kwanta luf, dakko turare silver yayi ya fesa a jikinshi dan shi mutun ne meson kamshi, direct Dakin mum dinshi ya nufa cikin natsuwa da yanayin ban tausayi, Gurfana gaban Mahaifiyar shi yayi yace" ina kwana hajiya kintashi lafiya? Bata amsa ba, Ya sake gaisheta for the second time shima still shuru tayi, yace" dan Allah hajiya kiyi hakuri ki gafarceni wallahi abunda suka fada ba daidai bane, ni tunda nake ko hannun mace ban taba rikewa ba, Rufemun baki tace" ba wuyanka ya isa yanka ba, nidai nafada maka, bakai ba Fauxeey sedai idan na mutu kwanan nan zan maka mata like i said yesterday tunda ashe ka isa aure bansaniba, Besan sanda yace" Mum wallahi inason Fauxeeya kuma wannan hukuncin da kke yankemun yamun tsauri Ni bawanda nakeso sai fauxeeya, "dago kanta da sauri tayi, taji matukar mamakin maganar da ya fada, Eh lalle kuwa wato hudubar datai maka har yanzu begama sakinkaba kenan, se Yanzu nakara tabbatarwa da wuyanka ya isa yanka tunda zaka kalla tsabar idona kacemun Ga wanda kakeso
   Sunkuyar da kanshi yayi, yace Kiyi gakuri karkimun auren dole wallahi banason kowa sai ita, Still binshi da kallo tayi, wai yau HAIDAR ne ke fadan haka, Ta kara cewa lalle baka da kunya, yana tsugunne a gabanta, be kara cewa komai ba, Yasmin da safiyya kuwa suma suna labe sunajin abunda ke faruwa indai hakane mum bataiwa Ya Haidar Adalciba ai yanzu an wuce Zamanin da za tursasa miji ya aure mace dole, Ba ai ma  mace dole bare namiji, kallon juna sukai Sannan suka koma falo suka zauna, Kowacce da nazarin maganar takeyi, Dan tabbas sun shiga yanayin tausayawa ya Aliyu Haidar dan Sunsan kadan daga cikin aikin mahaifiyar suce intai magana bata chanzawa....Fans yaku ke ganin haka??

****
   Bangaren Fauxeey kuwa itama tunsafe ta tashi tai kudirin yau dinnan inshaa Allah setasan yanda tai ta shiga gidan da akaiwa zeenatu Fyade dan kawai  takoya wa yaron hankali, Dan haka tashi tai ta shirya ta tafi gidan su zeenatu,
  Tana ganinta ta fara oyoyo Auntie fauxeey, Fauxeey kuwa murmushi tai cikin Murna da kulawa ta rungumeta tace" ya jikinki na abarku? Zeenatu tace" lafiya lau aunty,
Adaidai lokaci mahaifiyar Zeenatu ta fito, Maraba da Fauxeeya, Fauxeey tsugunnawa tai cikin ladabi da biyayya ta gaisheta tace yasu mamanku tace" lafiya lau,

Wajen ne yadau shuru na yan mintina sannan fauxeeuy tace mama wajenki nazo, Mushiga ciki, Tace" yo yar nan

Sunshiga dakin, Fauxeey ta soma magana tace da Allah mama wani temako nake nema kuma dole ta hannunki zan samu, Maman zeenatu tace taimako kuma? Nida bani da komai amma koma mecece ki fada Allah yasa zan iya. Murmushi Fauxeey tai tana wasa da yantsunta tace mama zama ki iya, Taimakon shine..Dan Allah inason kikaini gidan da zesnatu tai aikine Nima zanfara aiakatau a gidan

Maman zeenatu binta da kallo tai, bata manta abunda yafaru da yarta ba, Badan Allah ma ya kawo Fauxeeyan ba da setai Yanda Allah yayi kawai, Maman Zeenatu tace" Ehh Inda halin temaka miki amma gaskiya ina tsoro, Bancin hakama kalli kifa? me kika nema kika rasa?

Fauxeey murmushi tai tace zeenatu da sauran Yaran zan kwato ma yancinsu, inshaa Allah, yanzu abun wahalar shine kawai nasamu na shiga gidan
   Maman Zeenatu taji dadi sosai, tace to mungode da kokarin nan amma dai bani na kaita gidan ba, akwai nan makwabciyar mu ita tai mana hanya, Saboda safaran kai yara aikatai takeyi shine aikinta

Fauxeey Ok To kozan iya ganinta? Maman Zeenatu tace mezai hana, bari na aika yaro yaje Ya kirata, Tashi tai ta fita Ta sama aika yaro yaje gidan kiran baba lami

   Fauxeey kuma tace" yes tana murna tana rokon Allah yasa asama matar....

Shuru kusan 15mins Yaro be shugoba, Fauxeey zaune take gefen gadon Maman Zeenatu tana ta Addauan Allah yasa matar nanan dan taji shuru

Yaro ns ya shugo "yace wa Maman Zeenatu Tace gatanan zuwa" toh tace, Fauxeeya kuma wani Dadi taji aranta, Ba'ai minti 15 ba saiga matar nan ta shugo wacce akecewa Lami, Sallama tai sannan maman Zeenatu ta amsa da waalaikis Salam, shugo nan, Daki suka shiga
   Ganin Fauxeeya tai tace" au bakuwa kikai? Ta amsa da eh, Sannan ta sama waje ta zauna. Maman Zeenatu tace ga wacce ke nemanki Nan, kare mata kallo tai tace" toh daga Ina? Murmushi fauxeeya tayi tace" daga simbisa, baba Lami tace karkisa na gudu, sukai dariya dukansu

Fauxeey gyara zama tai tace Batakai ga magana ba Wayanta yai ringing...........

Muje ZUWA

yours Fresh Ummiey Xeey

Dont forget to Follow, comment and Vote Thanks

More Comment More Typing............

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now