LAIFINA NE 43

75 11 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 4️⃣3️⃣*

Tunda suka kama hanyar Kamu Hankalin Muhseen sam baya jikinshi, Lukman ne ya lura da haka yace Please ka bar komai a wajen Allah, Fauxeeya ba robonka bane kuma kasan ba wanda ke aurar Mijin wani, Shuru yai amma Shi Wallahi yanason Fauxeeya, Aranshi yace Bazaka gane bane

    Sun isa wajen Kamu lafiya, nan aka umurce Amarya da ango sui rawa, Haka Muhseen Ya fito jikinshi sam Ba kwari kamar ba Ango ba, Text yaji ya shugomai yana dubawa yaga Fauxeeya ce, Karantawa ya farayi, _Ango kasha kamshi ina maka fatan alheri, nayi murna matuka, naso ace nice matarka, amma karka damu haka Allah ya kaddaro, Kokarin dakai akaina Allah yasaka maka da alheri Nabarka lafiya_ tana text tana hawaye

Karantawa yayi nan take annurin fuskarshi ya chanza, "Wayyo Fauxeeya yace"

Text yai mata da I'll call you later, Tana Gani Taji Wani kishi sosai, Yanzufa saboda yana kusa da Wata macen yasa yai mata haka, Yar karamar tsaki taja dan Fauxeeya mace ne me matukar Kishi....

Jitai gidan yamata Zafi dab haka ta roka mamansu tace Ummiey Ta karata gidan Su baba Mairo da Su Zeenatu

Koda taje gidan su baba mairo tunda su basusan makasudin zuwanta ba kawai Ce musu tai tagama Aikinta gobe zata koma gida, Amma duk randa ta shugo zata zo dubasu inshaa Allah, Sukace Allah Sarki amma zamui kewarki sosai...nan ta basu sha tara ta arziki sukace Sungode tace in akwai wani abun ga phone number nan su kirata

A gurguje, Taje Gidan su Zeenatu nan ta labartawa maman Zeenatu duk abun da yafaru har artabun da sukai da bobo, Sukace Lalle a jinjina maki Fauxeeya, nan ma ta hada musu sha tara ta arziki kuma tace duk abunda suke nema karsuji kunya ga number nan su kirata, sukace Sungode, Sannan suka dawo gida
   

Bangaren Su Muhseen kuwa Anyi kamu lafiya sun koma gida, Tun daren fauxeeya suka harhada kayansu, Ta kashe wayarta, Muhseen yai neman duniyar nan be samuba, sai yaji sam Bayajin dadi Gashi dare yayi balle yaje gidansu A ranar dai a daddafe yai Bacci

    ***
  WASHA GARI
da Asuban Fari Fauxeeya taso subar garin dan Tsabar kishinta, mamansu tace Saurin me kkeyi, Ko karfe 11 ai se jirgi ya iso

   Fauxeey tace Hun'um tanajin radadi a zuciyarta, Wani irin so takewa Muhseen haka, Kodan Ya cetota daga Azzalumin nan ne?

   Bangaren Muhseen Kuwa, Da sassafe ranar daurin aurenshi ya sata hanya yazo gidansu Fauxeeya suna shirin Fita sai gashi yazo,
Hada ido sukai Da Fauxeey saiga Hawaye fal a idonta, Ko kallonshi batai ba, Mama na lura da ita tace bazaku gaisa bane?

   Shi kuma Muhseen Jikinshi duk yayi sanyi,

Gaisheshi tai ba tare da ta kalleshi ba dan komai zai iya faruwa da ita, Umimiey kuwa se satar kallonsu take dan Tana tausayawa yar uwarta,

Bata bari magana ya hadasu sosai ba, kuma duk maganar da sukeyi Muhseen ya kafeta da ido yaso su hada ido Ko zata ga how much he loves her amma Taqi yarda Sam dan Duk lokacin data kalle Idanunshi sukai arba da nata wani kasala takeji dan rasa mezatai takeyi Dan Son Gaskiya ba karya bane.....

Hakanan yaketa janta da hira amma tana kaucewa, Suna chikin hakane Saiga Dr Muhd saurayin ummiey
Nan suka gaisa da mama and everyone a wajen, Kallon Muhseen yai yace Har kazo? Yace eh Wallahi

Dr Muhd yace Jirginku ya sauka ya kamata by now kuna airport dan nan da 30mins zai tashi Sukace Ok

Nan Mama Tai musu godiya sosai, Dr Muhd kuwa yakaisu Airport,

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now