LAIFINA NE 50

88 9 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*This page goes to all my fans na fili dana boye i so much love youuu*

*PAGE 5️⃣0️⃣*

Agurguje...Haka dai rayuwarsu ta kasance Kullun cikin nunawa junansu sosayya sukeyi, idan ko weekend ne Haidar na makale da Fauxeeya Ko ina ta sa kafa yana binta Kamar zai cinyeta

   Bangaren Su Muhseen kuwa Matarshi Cikin 7months Tahaihu, akasama diya mace, akasa ma yarinyar Fauxeeya, Koda fauxeey taji labari tayi murna sosai, Muhseen yace da yanzu ke kika haifan mu baby ko? Tace uhmm Allah ya kaddaro haka Sai mugodemai, Yace hakane

   Kiran Zainab tai itama tamata barka sukaji dadi sosai

Tunda Haidar yaji labarin matar Muhseen ta haihu ya shiga damuwa, Yau kusan 6month ko bari fauxeeya bata taba, ba hankalinshi yai matukar tashi, dan haka ya zaunar da ita Yace Baby please ya kamata ace kina da ciki fa, dukda nasan Allah ke kawowa

   Gabantane ya fadi kardai Asirinta ya tonu,

Yace ya naji kinyi shuru? In akwai wani abune please let me know Dan nasan halinki, kinga ba boye boye, Dan nasan mun tabayin maganar tun kafin mui aure kikace Bazaki yarda da ga shiga ki haihuwa ba,

Rufe fuska tai ta fada kirjinshi tana bashi hakuri, Tace Baby am sorry Wlhi drugs nakesha na hana daukan ciki amma dagayau bazan kara ba kaji tana magana tana narkewa a jikinshi

  Hmm yace I doubt much, Amma baby meyasa haka? Bakyason kiga Danmu? Idan muka mutu fa wazai dinga mana addu'a

Kara narkewa tai a jikinshi tace I'm so sorry my love ka yafemun dan Allah, Yace Ok Ba komai Amma dan Allah karki kara, ina magungunan da kike sha?

Zamewa tai a jikinshi ta Bude side drawer dake gefen gado ta dakko ta bashi,

Budewa yai yagansu yan kananu yace baby please kidena sha basu da kyau fa

Tace inshaa Allah bazan karaba, Lakatan hancinta yai yace shine kikasa inata aiki akanki ko? Ashe ba wani baby da zai fito da ban wahalar dake ba nima da ban wahala ba tunda bakyason baby ai da bama making love semuita baccinmu ko?

Yanda yake naganar akwai alamun damuwa a tattare dashi amma sai ya boye mata

Saboda sonshi da tausayinshi daya shigeta batasan sanda tace Baby inason making love dakai ba, dan ka iya service sosai, inajin dadin hakan kuma I'm so sorryyy

Yace Lalala baby who spoiled you?

Tace na youuuuu spoiled me, yace baruwa baby

Tashi yayi yace ina zuwa, Shiga toilet yayi ya zubar da maganin yai flushing dinshi a toilet sannan ya dawo, Suka shiga nuna wa juna soyayya

***
  Watansu 6 a kasar Waje akaima Haidar transfer zai dawo kaduna, yan uwa da abokan Arziki kowa murna yakeyi sosai

Haidar kiran dad dinshi yai ya sanar dashi zai dawo zai rike wani babban company su, Alhamdulillah Babanshi yace Hajiya lubabatu ma murna taji sosai Dan yanzu tanason Fauxeeya matuka, kannanshi ma Dadi sukaji sosai dan they're missing Ya Haidar

***
Ana gobe Su haidar Zasu dawo Ahmad yaje gidansu haidar yace Suzo suga wani abu? Dad din Haidar yace menene? Nan Ahmad ya sanar dasu Ai Haidar yai gida babba me kyau kuwa

Dad Din Haidar shuru yai yace Allah yamai albarka, Tuntuni nake tinanin wani gida zasu zauna, tunda dai yarinyar nan yar manyane ba ko wani gida za'a aikata ba, ko namai magana sai yace kar in damu ashe yasan plan din da yakeyi, Kallon Ahmad yai yace sannu da kokari da rike Amana, kaima fa ya kamata ka fito da mata kai aure

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now