2

4.6K 266 4
                                    

KALLON KITSE PRT 2

Yace, ai ko dan kirkin shatu dole arike mata ita, saboda nikam inna yanda shatu ta daukeni tamkar dan data haifa, tunda ta raineni na fahimci haka, ki duba lokacin dakina zuwa aiki, hka zatai ta fama dani, har saikin dawo, sannan zata sami sassauci. Inna tace gaka da rigima kuwa, kai jafar kayi rigima wallahi. Dariya yayi tareda tafa hannu, gaskiyane inna, amma yanzu na bari ko? Ta harare shi, sai dai abunda ya karu.
indoce ta shigo tare da sallama, suka amsa mata baki daya, ta ajewa jafar abincin sa agabansa, yace sannu indo, tadanyi fara'a tace, "ina wuni kato! Yadan sha mur, inna kinganta ko? Har yanzu bata daina cemin kato ba, ni wlh bana son sunan nan. Indo tana dariya tace zan bari amma saika haifo mana wani katon, sannan sai in daina. Ta zauna akan kafet, tace inna kinga yarinyar nan uwani taki hakura abincin ma taki ci, sai ajiyar zuciya takeyi. Inna tamike ta isa bakin kofar falon. Uwani na nan inda take, tana kuka a hankali. Inna ta dauki abincin dake gabanta tare da rike hannun tace taso mu shiga daga ciki, in kinaso in maidake wurin shatu.
Mikewar da zatayi saita ga fitsari, "haba uwani fitsari kuma kikai anan? Indo dan Allah taso ki taimaka mata ts cire kayan nan. Indo dakinta ta kaita ta tubeta, ta bude 'yar leda data zo dashi bakomai aciki sai ragadadu, ta rasana wanda zata saka mata, har gara ma wnda ta cire matan, tafi sauki. Indo kam dan kwalin wata atamfar ta ta daura mata, don dai ba kayan da zata sa mata, duk ragane, sun dawo falon ta zaunar da ita, ta dauki abinci ta ajiye a gaban ta. Amma uwani ko kallon abincin batayi ba, ta soma wani sabon kuka, inna sai aikin lallashi takeyi, amma fafur taki. Jafar na zaune, yana sauraren su, saida ya gama sannan yazo har inda uwani take. Ya daka mata tsawa, yace ke zki daina kukan nan kosai na mareki? Nan da nan jikinta ya hau rawa, tayi tsit! Yace sa hannu kici ko in bata miki rai, kinaji ko? Inna tace, haba jafar lallashi fa akeyi da iyayen ta fa aka rabata? Yana duban uwani yace inna kyaleni da ita, haka kawai zatasa mu agaba tanayi mana kuka. Uwani kam sai sa loma take, cike da tsoro dan ita a rayuwarta dama bataso ayi mata tsawa, saida yaga tayi nisa da cin abincin, sannan yabar wurin, yayi wa inna saida safe, ta amsa masa, tana gamawa ko ruwa bata shaba. Ta soma yin bacci indo ta dauketa suka shiga daki, can gefen dakin inna,

*********************
Haj. Fatima, mace ce mai zuciyar maza, irin mazan nan masu halin dattako, ita 'yar asalin sokoto ce, anan mahaifanta suke tana da yayye da kanne, dan ba mahaiyarta kadaice agun mahaifisuba, mahaifinta dan boko ne sosai, dan hkane baya aurar da yaransa mata har sai sun gama universty dinsu. Haj. Fatima taci sunan inna tun tana gidan mahaifinta saboda sunan mahaifiyarsa taci, marigayi Hon. Alkali bello shine mijinta na farko kuma shine na karshe,
shima tsohon dan boko ne dan lawyer ne anan jihar sokoto. Allah ya albarkesu da 'ya'ya bakwai amma uku kadai suka rayu. Shima mijin nata baifi shekara bakwai da rasuwa ba kenan. Sunan yaran nata zainab itace babba, tana aure a gusau, tana auren wani attajiri, da yake aikin mai tanada 'ya'ya shidda maza uku mata uku duk sun girma, saboda 'yarta ta fari ma tanada aure anan gusau, harda yara biyu.
Sunanta mariya, saita biyu mansura ita tana nan a universty dake cikin zaria wato (A.B.U) ba wani shekaru mariya ta bawa mansura ba, amma saboda ita tana gama secondary school tayi aure, saina uku shine moh'd shima yana S.S.2, sai mukhtar yana J.S 3, sai faruk yana J.S 2, sai muhibbat tana primary 5. Karamar ce sai yanzu za'a sata makaranta.
Saliha itace ta biyu gun Haj. Fatima, duk da ba ita kebima zainab ba, itama tayi aure suna abuja da mijinta, 'ya'yanta uku , saidai kanana ne, faisal shine babba, yana aji biyu, hafsat itace ta biyu, ita nusery, akwai dan karami hafiz shibai riga ya shiga makaranta ba.
Jafar shi take kira auta, saboda shine na karshe yana karatunsa a dan-fodiyo universty, yana karatun doctor, yanzu haka ya samu shekara na biyar kenan. Rayuwar Haj. Fatima a saukake bata sama kanta kwadayin duniya ba, saboda tunda mijinta ya rasu ta samu gadon wasu gidaje biyar tasa haya, dasu take rayuwar ta, tana karba kowane shekara, inda tayi sa'a duk yawanci ma'aikata suka dauka haya, dan haka tana samu ba laifi,bata tsaya anan ba, tunda mijint ya rasu da yake da tana aiki, sai tayi rising tana zuwa dubai da china ta siyo kaya, tana sayarwa, takan turawa yaranta in sun saida suturo mata kudi ta banki ta koma kuma.
Jafar kuwa yaro ne dan gata gun inna saboda shiya zamto dan autan ta. Ikon Allah shine ta haifa na karshe, dan bata kara samun ciki ba, dan haka shagwaba ba wanda bayayi, musamman ta samo masa 'yar raino wato shatu, tun yanada watanni take tare da shi, har ya shekara bakwai, sannan tayi aure, takoma can jega dayake ita 'yar can ce, dan dan uwan mahaifinta take aure. Saboda shakuwar da sukayi wataran haka zai shirya yaje jega ya dawo.....

Mi hofni on bandirabe, barkamon be jumbare, sai jango bo toh Allah wadi

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now