31

1.9K 168 0
                                    


Amma gashi kyamarsa ma takeyi, ita ta tsinka masa tunani,
"bari akawo maka naka, wannan nida uwani ne."
ya saki baki eh lallai ya yarda inna bata sonsa, dole kuwa ya nemi son nan, ya dawo dashi kamar yadda suke da.
In banda sha'anin uwani ba ruwanta dana kowa, su duka 'yan matan suka shigo falon, ko wacce ta gaidashi, ya amsa cike da kulawa. Uwani ta zauna zata fara cin abinci.
Ya dubeta ke tashi ki debomin abinci."
inna ta dubeshi tare da bata fuska, "kai dai kazo ka damemu, keyi zamanki har ki gama."
ya lura uwani taji dadin hakan, shiru yayi yana kallon uwani batada dan kwali akanta, sannan batayi kitso ba, tayi parking din gashinta, gashinta irin wannan mai taushin ne, duk da batasa relazer ba, yayi kwance lub akanta
dan tsantsine dashi.
Gashin yayi masa kyau, da sauri ya kauda idonsa, shi wai meyake damunsa ne, ya ya za ayi yarinya 'yar kama tana nema ta maidashi wani wawa? Duk inda yake inbanda tunaninta ba abunda yakeyi.
Hafsat ta tsinka masa tunaninsa da ajiye masa abinci a gabansa, "ga abincin nan uncle rabu da inna." harara uwani ta sakar mata
"toh 'yar iyayi a rabu da ita din meye ruwanki?
"eh da ruwana, 'yar shiga sharo ba shanu." magana uwani zatayi sai suka hada ido da jafar, dauke kansa kenan an dauke wuta, tayi shiru ta maida hankalinta kan abincinta. Lokacin hafsat ta samu damar zakalkaleta. Inna tace, "rabu da ita ke dai ba a magana idan anacin abinci."
haka suka kare cin abincin, jafar dai a hankali yanata nazarin uwani.
Sai karfe tara da rabi zainab ta iso, gida ya cika da murna, gaskiya mumy (haka suke kiran zainab) kinyi sammako?
"eh toh gara mu shigo kar muyi latti. An shigo da kwanoni dauke da kayan fulawa, irin su, bonus, donut, cake, dabulan, da kuma gurasa da miyarta, sukaita jin dadi, dan suna son gurasa, tunba uwani ba, da yake akwai wata 'yar kano anan gusau tanayi, fashi kuma ta iya sosai.
Salaha ma ta iso da tata gudumawar, nasu sweet da cewing-gam duk dai komai anshirya, harda na kyauta, 'yar jakace aka hada hotunansu su duka sai akasa Alqur'ani mai girma dasu hadisai, gaskiya abun yayi sha'awa.
Ancika sosai, a wurin walimar jafar abaya ya soyo musu, shine gudumawarsa, yata jini-ni dasu, salaha wai anki a fadamasa balle yayi wani abun, inna tace, ni nace kada a fada maka, saboda dai an riga da angama shirya komai, yaushe ka shigo? Yau kwananka shida agari, donme za ayi maka maganar walima? Muka san da irin shirinka jafaru?
Kansa a kasa, idonsa jajur, lallai yayiwa inna laifi, tausayinta ya kamashi, ya kirkiro murmushin dole, "o.k hakane inna, amma da andan fadamin koda bazanyi komaiba am part of the family." inna tai ajiyar zuciya kawai batace komaiba.
Haka akayi taro yayi kyau ko wacce tayi karatu, kuma anyaka raguna har uku, can sai akaga anata shigowa da nama, abun ya basu mamaki, inna ta kira mal. Mamman ta tambaye shi inda aka samo nama yace, "ai inna tun safe jafaru ya aikeni na siyo, ashe bai fada muku ba? Allah yayi albarka,
Allah ya kara budi." inji mal. mamman, "ai haka ake so." ga baki daya aka amsa amin.
Anyi walima yayi armashi sosai, saida mangariba aka watse, shikam jafar daya bar gidan, wurin baba yunusa ya wuce, saida
suka zauna sosai sannan yace, "baba nazo da wata bukata ne, don Allah a taimaka min."
inajinka jafaru Allah yasa zan iya."
"baba inaso ne ka nema min auren uwani gun inna! Baba yunusa ya wangale baki dan murna, "dama nayi maka sha'awar haka jafaru, da yake ban san ra'ayinka ba, shiyasa banyi maka magana ba, tunda abun ya zama haka ba damuwa, zanyi duk abunda zanyi dan inga haka ya kasance.
"nagode baba Allah kara girma." hira suka shiga sosai, saboda abun ba karamin dadi yayiwa Alh. Yunusa ba, ya kara nuna masa muhimmanci da kwarin gwiwa.
Tunda safe asabar Alh, yunusa ya shiga gidan, aka tarbeshi da abincin kari, bayan ya gama yace yanaso yayi magana da inna, harda zainab dan saboda a falo suka zauna. Adai-dai lokacin jafaru ya shigo, gabansa sai faduwa yakeyi, ya sami wuri ya zauna, shima baba yunusa, ya fara, "Haj. Fatima gunki nazo, dan jafaru ya sameni da wani sako mai muhimmanci, nasan yayi tunani kwarai da gaske da yayi hakan.
Fatima nazo nemawa jafaru auren uwani, dan kece uwarta, kece ubanta, kinga sai ayi tuwona-maina, Allah ya kawo abunda sauki, ni banyi tsammanin zai sakko hakaba, kinsan shi Al'amari dama na Allah ne, dan hakane nace bara nazo da kaina, ba sakoba in fada maku wannan abun farin cikin."
ga mamakinsu saiji sukayi inna tace, "gaskiya niban yardaba." Alh. Yunusa ya dubeta cike da mamaki, baki yarda bafa kikace? Me yayi zafi haka? Bashi ba harda jafar yayi matukar mamakin hakan, lallai inna ta tsaneshi, abun ya daure masa kai, inna ta katse masa tunani, "gaskiya ni ban yarda ba baban yusrah."
ta kara maimaita maganarta, kuma fuska babu alamun wasa acikinta.
Ta gyara zama, bazan iya ba jafar auren uwaniba, saboda ban yarda dashi ba, bazan iya baiwa uwani mijin da hankalina bai kwanta akan shiba, dan dai yarinyar nan amanace guna."

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now