8

2.4K 152 0
                                    

>>>KALLON KITSE PRT (8)

shine nace zaba maka akayi?
"wallahi ni kasan yare nake so, amma ya zanyi tunda mama tasa baki, sai kuma dan yarinyar tayi minne.
"shege ina fata kayi bankwana da shashanci, dan aure ba abun wasa bane.
"i will try and stop, amma kasan is not that easy"
"dama nasani, gashi dama ka koma lagos, kayi barna da hujja,
"a'a zan daina insha Allahu, suka kwashe da dariya, safwan yace, "da yake fadane abaki, akwai sauki. Amma dai baikai zuci ba.
Adai-dai wannan lokaci wayarsa ta soma ringing, yayi saurin dauka, "ya lawal kana lafiya? Daga can lawal ke fada masa jarabawarsa ta fito sunansa ya fito a list, jafar baisan lokacin da ya yar da wayan ba yana "yes-yes, Allah na gode maka, na samu school din abokai. Yasake daukar wayar, ina! Ta tsinke ya nemi lawal din, toh captain yaushe zan zo kenan? Saika taso next weak, saboda nan da nan za a fara training, the time is going.
"hakane, toh sai mun hadu. Ya dubi abokansa,
abokan zan wuce, dole inje in fara shiri, dama so nake na wuce jibi in Allah ya yarda.
Toh Allah kiyaye hanya sai munyi waya kenan?
"good luck, thanks. Yafada. Ya fita daga dakin. Bai jira komaiba ya wuce birni kebbi, ya fadawa inna, sunyi murna kwarai da gaske, ranar alhamis din kuwa ya wuce.
**** **** *****
a yau an wayi gari uwani tana aji uku na primary a lokacin jafar har ya zama second leauternal ya zama dai cikekken soja, abun gwanin sha'awa gashi cikekken likita ga shikuma soja dan haka jafar yake ji da kansa, yanzu haka a wari yake aiki da yake akwai sabbin sojoji a can, yana daga cikin layin wadanda akeji dasu, ya sami watanni a can, tun inna na damuwa harta barwa Allah, kudi kuwa tuni jafar ya samu, don yanzu haka gida aka bashi a can, akwai dan course din da zaiyi acan din kafin abashi captain yana tare da abokinsa lawal acan yasami wata yarinya 'yar maiduguri wai ita zai aura, shikam lawal ba ruwansa dama shi rayuwarsa ta turawa ce, bai cika shiga harkar da ba tashi ba, akwai wani hutu na sati da ya samu ya tafi kebbi.
Ya samu uwani tana primary 4 headmastern makarantarsu ya bada shawaran abarta ta rubuta jarabawa na zuwa J.S 1.
inna sai murna take jafar dai baice komaiba, yana dai saurare, sai bayan isha'i, suna zaune yana cin abinci, inna tace, wai auta ina maganar da mukayi da kai ne?
"inna nifa yarinyar bata yimin ba.
Shin wai meke da munka dan nan, anya lafiya kalau? Kana neman shekaea talatin da biyar, amma ko tunanin aure bakayi?
"kai inna kidaina karamin shekaru iyaka fa talatin da uku...." ta katse shi, dan Allah gara can, kullum akayi magana saikace kai yaro ne, toh kada Allah yasa kayi auren, nikam bazan sake yi maka magana ba, kaje kayi abinda kaga dama, duk abokanka sunyi aure, yanzu kaida bakinka kacemin 'ya'yan bashir biyu, safwan kuwa daya, wai me kake so ka maida kanka ne, kullum aka hada da yarinya sai kace batayi maka ba?
Ni wallahi na gaji da irin abunda ka keyi....."
ya rike hanunta dole ta daina fadan ta dube shi, "inna zanyi aure kwanan nan, na sami matar da zan aura."  ta harare shi haka kace wancan zuwan ma da kayi, amma har yanzu shiru.
"inna abun da ya kawoni kenan, inaso aje a nema min auren yarinyar, inna ta washe baki yauwa ko kaifa auta, a ina take haka?
"uhm...uhm...'yar can warri ce, saidai su 'yan asalin maiduguri ne, shuwa arab ce...."
eye? auta nikam banason irin auren nan na nesa....," ya katseta inna aidai nanda maidu guri ba wani nisa...." itama ta tsinke shi, kai nifa nace ma bazan yarda da irin wannan auren ba, gaskiya haka kawai nan kebbi zuwa katsina ka rasa yarinyar da zaka aura sai 'yar maiduguri, duk yanda aka bada labarin tsafinsu?
"ai inna ba duka a taru aka zama daya ba, don Allah inna kidaina fadin haka.
"eh gaskiya ne, indaina fadin gaskiya dan kana son tayar mana da hankali.
"a'a inna ba haka bane, nidai inna ban yarda da asiri ba, kinsan sai inka yarda da abu zai zama gaskiya, agareka. Allah kuwa inna ba wani matsafa bama a can iyayenta sukeba, anan warri suke baki dayansu.
Inna kam taki ta saurara masa tace sam bata yarda ba, haka kawai taji auren bai kwanta mata ba, haka suka rabu ya kasa shawo kanta.
Dakinsa ya wuce, ya rasa abunda keyi masa dadi a duniya. Shikam inba marliya ba, toh bazaiyi aure ba kenan. Adaren ko abinci yaki dauka, har saida indo ta tura uwani takai masa. Tayi sallama bataji ya amsa mata ba, saita ci gaba da kwada sallamar ya shaka ya bude labule da karfi, saida ta firgita yace cikeda masifa, ke wai meke damunki, kinyi sallama ba a amsa ba basai ki koma ba, ko baki san hakan ba? Tayi saurin juyawa zata koma, ya daka mata tsawa saida hanjin cikinta yayi rawa, saikace hantar cikinta zata fita, ta tsaya cak! Yace zonan. Ta ware idanun nan nata farare tas, ta soma tagiya a hankali, ta iso kusa da kofar, sai kuma ta tsaya, ya harare ta zaki kawo min abincin ko kuwa, da wasu idanuwa kamar na mujiya" ita dai idonta tasa akasa, ta isa ta shiga ta ajiye akan center table din dakin. Zata fice taji yakai mata ran kwashi akai, saida hantar cikinta ta kada..

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now