22

1.9K 149 1
                                    

KALLON KITSE PRT (22)

Aikuwa watsi tayi da almajiran baki dayansu, ta nufoshi, mal. Kasimu tsaye yayi kikam, ta shake shi, duk yadda taso ta hana shi karatun, amma ta kasa, can ta fara kaiwa kasa da kanta. Gwiwarta a kasa tana fadi , tana fadin, nadaina wallahi zan fita, ka sassauta min."
mal. Kasimu kuwa sai karatu yake tayi, suma almajiran sunyi tsaye sun zagayeta, sai zare ido datake ta famanyi. Tayi kwance kasa tanata fizge-fizge, tana fadin, nadaina zan fita, ku daina, nace zan fita." mal. Kasimu yace, "toh fitaman, aiga hanya nan, kuma bari kaji da duk ka kara zuwa ko kusa da wannan wurin, toh wallahi saina tabata ka kone kurmus."
"bazan zoba, ka daina karatun nan, kaga ka konamin kafata da bayana, ka bari haka nan, na tuba, nayi alkawari bazan dawo nanba".
Basu dainaba, yace saika fadamin wanda ya aiko ka."
"shanshani ne yace, kada in yadda in fada, dan na riga dana dau alkawari bazan fada ba, wayyo hannuna shima ya fara konewa, ku daina haka nan, zan fita, nayi alkawari ku daina."
sannan suka sassauta. A bingire inna ta fadi kasa, tummm! Ka keji.
Mal. Kasimu ya duba idonta, sun koma yadda suke, sannan yace su tai, su kawo rubutun cikin galan da suka zo dashi, ya diba a hannunsa ya shafa mata a fuskarta.
Inna ta mike zaune, hawaye ta somayi, can mal. Kasimu ya dubeta, "Alhamdulillah! Ya fita, tashi ki zauna da kyau."
godiya ta somayi, dan ta gano abinda ke damunta, "ba inda yake mik ciwo?." ta girgiza kai, "babu, saidai inaso in kwanta, inyi barci."
"toh ba damuwa ki kwanta." ta haugado ta kwanta.
Uwani kam har lokacin bata daina kuka ba, su majina duk ta bata mata fuska, tana rungume da salaha, itama hawayen ne shar a fuskarta.
Mal. Kasimu ya fito shatab, yayi zufa kamar wanda aka watsawa ruwa ajikinsa, suna ganin ya fito kawu ya masta gunsa, yana yi masa sannu.
Ya amsa tare da cewa a taimaka masa da ruwan sanyi. Da sauri zainab ta dauko, su duka suka sha, suna hamdala, mal. Kasimu ya gyara zama sosai, sannan ya dubi baba yunusa, toh Allah ya taimaka abun yazo da sauki, tunda ya fita Alhamdulillahi, sai muyiwa Allah godiya, aljani ne aka turo mata, kafiri ne yanada kaifi sosai, duk wani farin ciki da baiwar Allah nan zata samu, saiya hana hakan, sannan yayi sanadin mantar da ita dan nata, yana yi mata illa can cikin jikinta, in aka fara yimata zancen dan nata, dan shiyasa bata so ayi mata maganarsa, sun sa mata bata iya fadin abunda ke damunta, ko in anyi mata maganarsa tana nuna damuwarta, shi dan a ina yake ne?
"yana kaduna".
"a'ah babban magana dan nashi aikin zaifi wahala, saidai za'a taimaka ayita addu'a, saboda maiyin wannan aikin tana iya kisa akan duk wanda ya nemi ya rabata dashi, saidai a yawaita addu'a, har sai dan kansa yazo gida.
Akwai taimako da zanyi saidai ba wai abu na gaggawa bane, zai dau lokaci, inaso ne ya dawo gida da kansa, in muka ce ya dawo da gaggawa, aikin bazaiyi ba sosai, don haka don Allah inaso ku kula, kuyi amfani da abunda zan fada muku, kuyi ta addu'a ba dare ba rana, nima zamu tayi a can, insha Allahu zaku ga sakamako. Amma kuma saikun tashi tsaye, ni zan wuce." kawu hashimu yace, "malam me zai hana ka bari har gobe?
"a'a gaskiya akwai abunda zanje inyi, saboda aikin da nayi yau ba karami bane, zai iya yiwuwa a kara nemanta da daddare, dole inje inyi wani aikin."
"toh Allah bada sa'a, amma ita yaya shikenan ba wani abu da za ayi mata?
"eh ga rubuntun da zata sha data tashi daga barcin data keyi, shikenan insha Allahu ta rabu dashi har abada." baba yunusa yamike sukayi waje da mal. Kasimu, su zainab akayi zaune kamar ana zaman makoki. Sun wuni cur, bamai bawa wani hakuri, hardai uwani duk tabi ta lalace, ko zata iya tuna rabonta da abinci?
Inna bata farka ba sai karfe tara na dare, koda ta bude idonta uwani ta gani zaune kusa da ita rike da hannunta, da sauri uwani ta kwallawa zainab kira, "momi, mami ta tashi." da sauri ta iso ta bata rubutun malam tasha, sannan ta mike, yadda taga duk sun rame yasa ta saki murmushi, "ina so inyi wanka duk jikina yayi tsami."
"inna ki bari kici abinci tukunna."
"a'a uwani bari dai inyi wanka tukunna, sai inci."
"ba inda ke maki ciwo inna?" ta rike hannun uwani sosai tace "babu". Sai a lokacin ta saki fuskarta.
Bayan tayi wanka ta fito, uwani gabanta ta zauna tana kallonta, inna tace, saikace ke kikayi ciwon, duk kinbi kin rame uwani, dama gaki yadda kike ba wata kiba ba."
tayi murmushi ta shige jikin inna tana dariya, "inna wallahi na zata zan rasa kine."
"insha Allahu sainaga jikokina uwani, karki damu, lokaci bayyi ba tukunna."
tun daga lokacin kowa ya tashi da addu'a badai kamar inna.
Uwani suna ta shirin jarabawa ta shiga aji biyar (s.s 2), tana zaune tana karatu, inna ta dubeta, uwani tashi ki dauko abinci muci.
"inna saidai in debo miki, amma ni na koshi."
"kai tawan, a rika cin abinci, dubar ki 'yar siririya kamar zaki karye."
"inna kenan, ni kuwa gani nake nafi kowa ci."
"a da ba, da kina karama, yanzu kam kin daina."
"dama girma nasa rashin cin abinci? Inna gashi nikam na koshi dazun nan naci abinci."

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now