13

2.1K 149 0
                                    

KALLON KITSE PRT (13)

Bata kalle shiba tace "a'ah nagode, Allah ba komai, ya jere da ita suna tafiya, "kin gane ko bai kamata ace kina irin wannan wurin ba, so kizo muje inyi dropping dinki.
Ibrahim yace kibi shi, kada Ammi taji shiru. Ta danyi jim tace toh shikenan.
Da saurinsa yaje ya bude mata kofar gaba ta shiga, shima ya zagaya ya bude na tuki ya shiga, yace "a ina unguwar ku take? Ta fada masa cikin nutsuwa a hankali suke tafiya, kamshin turaren motar ya kasheta sai dadi takeji, ya tsunka mata tunani, "ya sunan 'yan matan?. Tayi kamar bataji ba, saida ya kara da cewa dan Allah ki fadamin. Ta nisa tace "marly.
"what a sweet name? Nan kuwa kamar na taba ganinki wani wuri your face luck familia? Bata kalle shiba tace "uhm".
Haka yaci gaba da tambayarta hanyar dazasu bi, har suka kai gidan magajiya, tace nan ne gidan.
Yayi parking "nagode. Ta fada tare da bude kofar,
ya zan iya zuwa gobe? Inaso in gabatar da kaina sosai zuwa gareki marliya.
Tayi shiru gashi mu ba'a bari muyi hira a gidan mu.
No dont tell me, at your age ace ana hanaki hira, kina fadamin bakida wanda ki keso kenan? Toh shikenan inaso inkara haduwa dake, ya za ayi kenan?
Ta langwabe kanta, saidai inbaka number ta.
"yes...yes bani. Ta fada masa yana sawa a wayarsa, yayi dialing tata ta soma ringing tace, saida safe.
Ta fice a guje, saida ya samu minti biyar a zaune inda yake, shi ya rasa meya haukansa, duk yaji yainyar ta shiga ransa ba kadanba, kamar ta fito ya sake kallonta, ashe haka mutum yake ji inya soma son mutum? Ya tambayi kansa. Jikinsa yayi sanyi lakwas a haka ya kama hanya ya tafi.
Tana labe a kofar gida tana lekensa saida ya tafi, sannan ta kira ibrahim yazo ya dauketa, tun a cikin mota suke dariyar keta, har saida suka isa.
Aranar celebraty akayi na musamman, bata taba tsammani abun zai zo da sauki haka ba, "gaskiya kin iya pretending marly baby, danaga kina acting din kamar 'yar shekara sha tara.
Suka kwashe da dariya.
Ranar ta kasa barci saboda murna.
Washe gari tunda safe taje gun ammi, bayan sun gaisa, ammi tace "kinsan zan wuce london jibi, amma ke kinki ma ki shirya taki tafiyar bamunyi zamu hadu a dubai ba? Tasa idonta kasa tace, Ammi inada magana.
Hajiya magajiya lunke kaya takeyi, saita tsaya tareda kallon marliya, sai yanzu ta lura da yadda marliya ta rame, duk ta fita hayyacinta, meya sameta? Kar dai wani ciwo ya sameta?.
Ta tanbayi kanta, inko hakane na shiga uku 'yar nan itace mai taimaka mini.
Haka ta sake fada a zuciyarta, tsam ta cire hanunta akan aikin data keyi, ta nemi wuri kusa da marliya ta zauna tace maganar me zaki fada min ina saurarenki.
Marliya ta gyara zama ta dubi mahaifiyarta cikin idon ta, "Ammi aure zanyi!!!.
"what? Wane irin magana ki keyine marliya?
"you hard me right Ammi maganar kenan aure zanyi, kuma ba wanda ya isa ya hanani.
Ammi tayi ajiyar zuciya ta kara duban 'yarta cike da zagwadin jin amsar tambayar da zata je fawa 'yarta, "wazaki auran? Itama ajiyar zuciya tayi, tace, wani bacholor ne, dan jihar kebbi 2 let jafar yazo yin wani course ne anan, amma asali a N.D.A yake, shi likita ne kuma soja ne.
"oh my God, kar dai dan yaro kike so marliya?
"eh toh bazai wuce thirty three ba.
Kinsan abunda kike fada marliya? He is five years younger than you?
"toh ai ammi ba haram bane, aiba akaina farau ba, kuma ba akaina za a daina ba, common Ammi nifa tunda inasonsa to koda shekara ashirin ne.
Ta juyar dakai gefe tace, "ina fatan yanada abunda zai dauke nauyi na dan kinsan fa dama kece mai bani, dan yanzu bazan iya.....".
Ammi wannan ba abun damuwa bane zai iya kula da irinki goma ma, so abunda nakeso, inaso kisa hannu mu hadu, mu kamashi a hannu tukunna,"
"hey! Magajiya tasan 'yarta tanada taurin kai, intasa abu a gabanta, to saita ga bayansa, kuma sau dayawa tana cin nasarar kudirinta, dan haka tasan ko yanzu za aci nasara shiyasa ma gabanta bai fadi sosai ba, tace dont worry my girl, zaki aure shi insha Allahu, ki saki ranki zan baki 100% hadin kai. "yauwa Ammi nagode, yau zai fara zuwa gidan mezamu shirya masa?
O.k, kice yau zan kasance da in-low dina, its going to be special, da kaina zanje kasuwa yanzu in sawo kayan girki.
"nagode Ammi, kamar kinsan jiya ban samu barciba, dan haka Ammi ni zanje in kwanta, yace zaozo da karfe biyar na yamma....yauwa na manta in fada miki Ammi, dole kiyi pretending as irin iyaye masu daukar addini da muhimman ci, ina nufin ki kasnce maisa hijjabi, sannan ki nuna masa mu masu tarbiyane.
"nida ko hijab bana dashi marliya.
"karki damu na dauko na hafsat, zan baki saiki sa.
Ahaka sukai ta shirin zuwan jafar alkali Bello,shima din matsuwa yayi lokaci yayi yaje ga wannan baby-face din da ya gani jiya, tunda ya fita sallar la'asar bai koma office ba, saiya wuce shopping mall yayi tsaraba, baisan ma nawa ya kasheba, da kayane ya cika boot din motarsa. Ya isa gida yayi wanka, ya shirya, kwarjininsa ya bayyana sosai, ya feshe jikinsa da turare.
Karfe biyar saura minti goma sha biyar yana harabar gidansu marliya, ita kuwa tana daki dadi ya cikata,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now