11

2.2K 143 0
                                    

KALLON KITSE PRT (11)

Adai-dai wannan lokaci kuwa ya fito, marliya ta juyota tace gashi nan ya fito jamila, dubeshi bai hadu ba? Ki kalle shi da kyau.
Jamila ta girgiza kanta, "hakane marliya "he is too much", kamar daga sama sai suka hada ido dashi, batasan sanda ta saki bakiba, ta kwantar da kanta kujerar da take zaune akai.
Shikam ya shige motar shi ya wuce inda zashi, cewa jamila tayi mu bishi muga inda zai shiga.
Jamila tayi reverse tabi bayansa saida suka shiga cikin gari, basu san sanda ya bace musu ba, da kyar suka gano shi, suka ci gaba da binsa, haka suka gane yana zaune ne inda sojoji ke zama, jamila ta daga kan mota sukayi gida.
Tun daga lokacin da marliya tasa ido kan jafar, bata kara samun kwanciyar hankali ba koda yaushe zaka ganta cikin tunani, tasa aje abincika mata shi, amma yau kwana hudu kenan babu bayani.
Jamila tayi kokarin ta kwatar mata da hankali, amma ina taki, harda 'yar rama tayi, duk wadanda taba appointment duk taki zuwa, saidai jamila ta wakilceta, ita kam dama jamila abunda takeso kenan, dan bata kai marliya karbuwa ba a wannan sha'anin, duk da haka yawancinsu basu yadda da hakan ba,
ibrahim shine dan masanin marliya ko kai waye awannan garin, inta turashi ya ganoka, to sai yayi bincike koda number mota ne, shikuma aikinsa kenan, indai ta nemi ibrahim tace tana son ya bincika mata waye mutum dan hakane data dawo gida, shita nema, ta bashi number motar jafar, shikuwa ya shiga gari nemansa, an sami kwana shidda ana neman jafar, ranan saiga ibrahim yazo mata da hotunan jafar kuwa, aranar kudin data bashi bata san ma nawa bane dan murna.
Tayi tsalle, tayi rawa, batasan inda zatasa ranta ba, dan murna. Tas aka bata labarinsa. Ibrahim ya fada mata cewar, sunama da wani taro da za ayi na sojoji in zataje, dan shima zaije, ba inda taji jafar ya burgeta yadda taji cewar shi likita ne kuma soja, gaskiya ya hadu da yawa.
Haka kullum take fadi.
Jamila tace, toh ya zamuje taron kenan?
"haba dan Allah jamila dadina dake sauri da garaje, bazan tunkare shiba harsai naje naga mal. Hussaini da shanshani, ya za ayi kinsan fa wannan gayen sonake in aure shi, don haka dole insan yadda zanyi.
"hakane. inji ibrahim, marli baby magananki kinada kashin gaskiya, don haka yaushe zamuje gunsu?
"yau dinnan zamuje gun mal. Hussaini, da yake shi a bauchi yake, sannan in wuce gun shanshani a maiduguri.
Amma da sharadi banaso Ammi (mahaifiyarta), taji wannan labarin, kunsan bason shawarar zatayi ba kun ganeko?
"toh ai muna tare, ba yanda za ayi taji,
"a'ah jamila ke zaki zauna dan nace da Alh. Sani gold yazo yau, kinga saiki wakilceni. Jamila bataso hakan ba dan itama tanaso taje taga malamin marliya, duk lokacin da zataje sam bata yadda tabita tarasa dalili.
A ranar kuwa suka kama hanyar bauchi, da yake shararren malami ne, yada inda yake sauke baki, bata damuwa da neman masauki, cikin kankanin lokaci aka hadata dashi. Bayan sun gaisa, ta gyara zama tace, mallam kasan yanda nake baji ba gani idan inason aiki dan haka nake son aikin gaggawa, akan wani gaye. Ina sonsa mallam, inaso shima ya soni, kota halin kaka, inaso ya soni tamkar uwar data haifeshi.
Mal. Hussaini ya juya wuyarsa dama, tana magana yana 'yan rubuce-rubuce yace, bake yafi sonki akan yadda yake son uwar tasa? Tayi murmushi mai gamsarwa tace, inaso mana mallam, inaso kada yaga kowa daga shi saini marliya.
Mallam ya buga kasa sau uku, ya kara bugawa yadanyi tsaki, "mts...marliya kina son gayen nan da aure kikace?
"eh mallam inaso in aure shi, in mallake shi kuma.
"toh naga zako aure shi, zai kuma biki, amma fa akwai duhu mai wahalar ganewa.
"mallam ka gani ko menene. Yaci gaba da bincike, yauwa na gano matsalar, saidai fa da wahala in zaki iya yi.
"wace irin wahala ce banyiba abaya mallam, ka manta dani wacece ka manta dani mai naci ce, akan abinda nasa gaba.
Hakane marliya amma gaskiya wannan daban ne, saboda aiki ne sosai.
"gaya mini wane irin aiki ne? "na farko inji mallam hussaini, "ni zanje wani kauye daba asanni ba, in zama mahaukaci cikin kwana tara, ina binne-binnena, sannan inna kwana sha uku in binne kare mace da namiji agu daya, saidai  kuma ke awannan lokaci zaki kasance baki yiwa kowa magana ba sai bayan na fada maki na gama.
Wannan yaro dakike so yanada karfi sosai, jininsa akwai karfi, sannan iyayensa ba wai mahaifansa ba, a'a kakaninsa sunyi musu kafi mai karfin gaske, asiri baya tabasu, dan haka duk abunda nace dake dole kiyi.
Ta girgiza kanta da sauri, "eh zan iya mallam.
"toh sai abu na biyu zan shiga daji in kwana uku, bayan sati biyun nan, ke wasuma basai na fada maki suba, ayanzu amma fa akwai aiki ja a gabanmu, sai a hankali zan gano saura.
"toh Allah ya taimakemu, ya ams da amin"
yaushe zaki wuce? ya tambayeta
sai jibi, domin gobe zan wuce maiduguri.
"dakin kai saiki kirani dan in fara aikin.
"toh ga wannan mallam.
"marliya kenan dubu hamsin me zasuyi? "a'a ai bawai kudin aiki na bada ba, ina zaton saika gama zan baka cikon kudin.

KALLON KITSEOn viuen les histories. Descobreix ara