58

3.7K 172 4
                                    

Kallon kitse

Batun inna kuma tunda ta farka bata ga uwani ba, tasan cewa tabi mijinta, dariya ma abin yaba inna, can kasan ranta kuma taji dadin hakan.
Watanshi biyu da sallama ya samu lafiya sosai baya kula matan waje tunda ya gane KALLON KITSE yake wa rogo. Batun barasa bai cika shaba, sai lokaci-lokaci.
Waya yayi ma inna yau kam ta dauka kuma sun gaisa faram-faram, yasa ya shirya musu tafiya.
Uwani tace itakam bata zuwa dan tana jin kunyar inna, yace kada ta damu bakomai. Haka suka nufi birnin kebbi dauke da dan cikinta wata daya, da sati biyu, inna ta tare su da murna, musamman ganin yanda uwaninta ta cika tayi dam! Tana sheki. Haka 'yan uwa suka ta zuwa gaida shi, saboda inna taki sanar da kowa ciwon nashi. Sai wanda ya ce "ina uwani, sannan zata fada mishi, su hafsat, fa'iza da lawisa duk sun zo sun gaida uncle dinsu, kowa da dan yaronta.
Satinsu daya suka koma, inna kam tace zahra 'yarta ce.
Jafar ya jawo uwani jikinshi, sannan ya rada mata a kunne cewa, "dama gidanta akai cikin zahra dan haka mu bar mata."
ta dubeshi tana dariya, tace, "kai uncle kazo su tafi."
saida inna ta bashi wani magani na gargajiya, bata ce ko maganin menene ba, har uwani tana cewa, "nima insha inna?
Tace "a'a kada kisha, na kula dake ba ke kadai bace."
yace, "hakane inna, taci wake ne."
ta rufe fuska tana mamaki, meyasa jafar baya jin nauyin inna?
Sun koma gida da yamma, suna shiga da gudu jafar ya shiga toilet amai yaketa shekawa, tamkar zai amayar da hanjin cikinsa, amma daya gama yace babu inda ke mishi ciwo, giya ce dai daga wannan aman baya son koda warinta ne.
Sai ya ji zuciyarshi tana tashi kamar zai kara irin aman. Haka rayuwa taci gaba da wakana, soyayya kuma sai wanda suka manta, balle uwani akwai gyaran jiki, tunda tasan ga yanda mijinta yake. Ya samu karin girma sun koma abuja, kullum inna tana farin ciki, tare da yi musu fatan alkhairi.

Tamat bihamdulillah.

Halima Abdullahi k/mashi

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now